Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Shouting - A turance tana nufin kururuwa.
Misali; Sadiƙ yana da rowa idan aka ɗauki abinsa kururuwa yake.
HAU; Kururuwa (Tana nufin ihu da ƙarfi)
Showing eagerness - A turance tana nufin hanƙoro.
Misali; Tun safe yake hanƙoro, saboda za su buga ƙwallon ƙafa da abokansa.
HAU; Hanƙoro (Tana nufin nuna zaƙuwa)
Showing Energy - A turance tana nufin kuzari.
Misali; Jaririn yana da cikakken kuzari masha Allah.
HAU; Kuzari (Tana nufin ƙarfi da lafiya)
Shrilling done by women to express joy - A turance tana nufin guɗa.
Misali; Matan sun kaure da guɗa a lokacin da aka shigo da amaryar.
HAU; Guɗa (Tana nufin wani salo na sarrafa ihu da mata ke yi musamman a lokutan farin ciki)
Side - A turance tana nufin gefe.
Misali; Na ajiye kayan a gefen rijiya.
HAU; Gefe (Tana nufin wani sashe)
Sign/Indication - A turance tana nufin ishara.
Misali; Duk wanda ya yi mugunta sai ya ga ishara kafin ya mutu.
HAU; Ishara (Tana nufin nuni ko alama)
Similarity - A turance tana nufin kama.
Misali; Yaran gidan suna kama da juna duka.
HAU; Kama (Tana nufin shige)
Siren - A turance tana nufin jiniya.
Misali; Na jiyo jiniya, da alama 'yan kwana-kwana sun zo gurin gobarar.
HAU: Jiniya (Tana nufin ƙarar da motar asibiti ko ta 'yan kwana-kwana ko 'yan siyasa ke ɗauke da ita. Ƙarar na nuni da cewa abu ne na gaggawa ya faru, ko gobara, ko an ɗauko mara lafiya da sauransu)
Skilled - A turance tana nufin gogagge.
Misali; Ai malamin gogagge ne a fannin kimiyya da fasaha.
HAU; Gogagge (Tana nufin ƙwarewa a wani abu ko wani fanni)
Skin - A turance tana nufin fata.
Misali; Ana amfani da fata don yin jakunkuna da takalma.
HAU; Fata (Tana nufin abin da ya lulluɓe jikin mutum ko dabba)