Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Leucoma - A turance tana nufin hakiya.
Misali; Hakiya ce ta fito masa a ido.
HAU; Hakiya (Tana nufin ciwon da ke fitowa a cikin ido)
Library Registration Council of Nigeria (LRCN) - Hukumar Ɗakunan Karatu Ta Najeriya
Licensed Electrical Contractors Association of Nigeria (LECAN) - Kungiyar Sahalallun 'Ƴankwangilar Lantarki Ta Najeriya
Lie - A turance tana nufin ƙarya.
Misali; Ya faɗi ƙarya domin ya gujewa hukunci.
HAU; Ƙarya (Tana nufin faɗin magana wadda ba gaskiya ba).
Lie curled up - A turance tana nufin ƙudundune.
Misali: Yaron ya ƙudundune a kan tabarma saboda yana jin sanyi.
HAU: Ƙudundune (Tana nufin kwanciya a nannaɗe ko a dunƙule saboda jin sanyi, ko ciwo)
Lie down -
A turance tana nufin kwanta.
Misali; Bayan ya wuni yana aiki, ya kwanta a gado don ya huta.
HAU; Lie down (Tana nufin shimfiɗa jiki a ƙasa ko kan gado don hutawa ko yin bacci)
Lift and carry something heavy - A turance tana nufin cicciɓa.
Misali; Buhun simintin za mu cicciɓa mu kai saman benen.
HAU: Cicciɓa (Tana nufin ɗaukar abu mai nauyi)
Light - A turance tana nufin haske.
Misali; Haske ya mamaye ɗakin sakamakon kunna fitilar da Laure ta yi.
HAU; Haske (Tana nufin abin da ke fitowa idan rana ta fito kuma yake gushewa idan ranar ta faɗi)
Kishiyarta; Duhu
Limping - A turance tana nufin ɗingishi.
Msali; Ɗingishi take yi saboda marurun da ya fito a ƙafarta.
HAU; Ɗingishi (Tana nufin yin tafiya ba daidai ba, ana yi ana dakatawa saboda dalilin ciwo a ƙafa ko wani abu daban)
Linguistics Association of Nigeria (LAN) - Ƙungiyar Masan Kimiyyar Harshe Ta Najeriya