Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Large Edible Toad - A turance tana nufin ƙozo. Misali: Masunta sun kama ƙozo a bakin ruwa da yamma yayin da suke kamun kifi. HAU: Ƙozo (Tana nufin babban kwaɗo)
Large hen - A turance tana nufin daƙwalwa. Misali; Kazar daƙwalwa ce don ta ƙosar da mu. HAU; Daƙwalwa (Tana nufin babbar kaza ma'abociyar tsoka)
Large hoe with wide blade - A turance tana nufin garma. Misali; Gatari ba zai yi aikin nan ba sai dai a sa garma. HAU; Garma (Tana nufin ƙaton gatari mai faffaɗan kai)
Large Mass - A turance tana nufin dafifi. Misali; Mutane sun yi dafifi a wajen kallon wasan kalankuwa. HAU; Dafifi (Tana nufin taruwar jama'a da yawa)
Large millipede -

A turance tana nufin ƙadandoniya.

Misali; Yara sun ga ƙadandoniya a bayan gida.

HAU; Ƙadandoniya (Tana nufin wani ƙwaro mai ƙafafu da yawa)

Large needle - A turance tana nufin basilla. Misali; Na yi amfani da basilla na ɗinke buhun kayana. HAU; Basilla (Tana nufin allura babba da ake amfani da ita wajen ɗinke buhu ko ƙwarya da sauransu)
Large noise -

A turance tana nufin kwaramniya.

Misali; An ji kwaramniya a kasuwa lokacin da mutane suka taru.

HAU; Kwaramniya (Tana nufin hayaniya mai ƙarfi ko girgiza kunne)

Large Stallion - A turance tana nufin ingarma. Misali; Dokin yarima ingarma ne. HAU; Ingarma (Tana nufin babban doki ko gabjejen mutum)
Large wide-mouthed earthenware pot - A turance tana nufin kwatarniya. Misali: Kaka ta cika kwatarniya da ruwa domin amfanin gida. HAU; Kwatarniya (Tana nufin babbar tukunyar ƙasa mai faɗin baki wadda ake ajiyar ruwa ko hatsi a ciki)
Last Long - A turance tana nufin daɗe. Misali; Yau ɗaliban sun daɗe ba a tashe su ba. HAU; Daɗe (Tana nufin ɗaukan lokaci mai tsaho)
1 215 216 217 218 219 337