Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Trading - A turance tana nufin fatauci. Misali; Idi ya tafi fatauci wata biyu da suka wuce. HAU; Fatauci (Tana nufin tafiya daga wani gari zuwa wani gari don siye da siyar da kaya)
Transaction - A turance tana nufin hulɗa. Misali; An ƙulla hulɗar cinikayya tsakanin 'yan kasuwar. HAU; Hulɗa (Tana nufin mu'amala ko cuɗanya)
Translation - A turance tana nufin fassara. Misali; Ya fassara littafin daga harshen larabci zuwa harshen Hausa. HAU; Fassara (Tana nufin daga wani harshe zuwa wani harshe)  
Transmission Company of Nigeria (TCN) - Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki Na Najeriya
Tree - A turance tana nufin bishiya. Misali; Idan an shuka bishiya takan ɗauki lokaci mai tsawo kafin ta girma. HAU; Bishiya (Tana nufin ice ko tsiro da yake fitowa haka kawai ko idan an shuka, yana da ganyayyaki da itatuwa a wasu lokutan)
Tribunal - Kotun Wucin Gida
Tribunal Court - Kotun Wucin Gadi/Kotun Musamman
Truth - A turance tana nufin gaskiya. Misali; Idan mutum na faɗin gaskiya kimarsa na ƙaruwa. HAU; Gaskiya (Tana nufin abinda yake na haƙiƙa ma'ana yanda yake babu ƙari babu ragi) Kishiyarta; Ƙarya
Tsagaita - Tsahirtawa daga yin, ko barin wani abu ta hanyar taƙaitawa ko kaucewa, kamar daina yin abin da yake jawo ko haifar da asarar dukiya ko ta rayuwa.
Tsaron Sirri - Aikin tsaro ne da jami'an tsaro na farin kaya suke yi a boye domin nesa daga magauta.
1 214 215 216 217 218 229