Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kamfani - Tana nufin ma'aikata mai ɗauke da mutanen da suke aiki a ƙarƙashinta.
Misali; Alhaji Mudi ya gina sabon kamfani a karkararsu.
ENG; Company (A turance tana nufin kamfani)
Kamfata - Tana nufin ɗiban abu da yawa.
Misali; Idan ba ka zuba musu abincin ba kamfata za su yi.
ENG; Take much of (A turance tana nufin kamfata)
Kamili - Tana nufin nagartaccen mutum mai kyawawan halaye.
Misali; Malam Musa kamili ne.
ENG; Gentle person (A turance tana nufin kamili)
Kammala - Tana nufin gamawa.
Misali; Idan kun kammala aikin da na ba ku sai ku tafi gida.
ENG; Complete (A turance tana nufin kammala)
Kishiyarta; Fara/Farawa
Kamɓori - Tana nufin ɓawo ko kwanson ƙwai.
Misali; Ana haɗa hoda wacce mata ke shafawa da kamɓori.
ENG; Egg Shell (A turance tana nufin kamɓori)
Kan ƙuda - Tana nufin ɗan ƙanƙani.
Misali; In dai akwai ɗigon da ya kai kan ƙuda na shirka a zuciya, to ta ɓaci.
ENG; Tiniest Amount (A turance tana nufin kan ƙuda)
Kan-gado - Tana nufin hankali ko fahimta.
Misali; Yaron yana da kan-gado ainun.
ENG; Common Sense (A turance tana nufin kan-gado)
Kananzir - Tana nufin makamashin da ake amfani da shi wajen girki da kunna fitila.
Misali; Zamani ya sa an dena amfani da kananzir sosai.
ENG; Kerosene (A turance tana nufin kananzir)
Kanari - Tana nufin wani nau'in tsuntsu ma'abocin rera waƙa.
Misali; Tun asuba nake jin kukan kanari a kan bishiyar gidan nan.
ENG; Canary (A turance tana nufin kanari)
Kandagarki - Tana nufin kariya.
Misali; Ya yi wa kansa kandagarki don ya san zai daku.
ENG; Protection (A turance tana nufin kandagarki)