Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

International Maritime Organization (IMO) - Hukumar Sufurin Teku Ta Duniya
Internationl Air Transport Association (IATA) - Ƙungiyar Jigilar Jirgin Sama Ta Duniya
Intrusiveness - A turance tana nufin katsalandan. Misali; Makwabcinsa yana yawan yi masa katsaladan a al'amuran shi. HAU; Katsalandan (Tana nufin shiga abin da bai shafi mutum ba ko shisshigi)
Invent -

A turance tana nufin ƙaga.

Misali; Masanin ya bayyana sabuwar na'urar da ya ƙaga.

HAU; Ƙaga (Tana nufin ƙirƙirar wani sabon abu wanda ba a taɓa yin irinsa ba)

Invent / Create - A turance tana nufin ƙirƙira. Misali: Manhajar da Isa ya ƙirƙira ta ƙunshi sabon tsarin gudanar da makaranta ta yanar gizo. HAU: Ƙirƙira (Tana nufin samar da wani sabon abu ko tunani ta hanyar amfani da fasaha, ilimi ko basira)
Investigation - A turance yana nufin bincike. Misali; 'Yan sanda na bincike don gano masu aikata laifi. HAU; Bincike (Tana nufin ƙoƙarin gano wani abu)
Invite - A turance tana nufin gayyata. Misali; Malaman sun samu saƙon gayyata ne daga hukumar ilimi ta ƙasa. HAU; Gayyata (Tana nufin kira zuwa wani sha'ani, wato sanar da mutum cewa ana buƙatar ya zo)
Inzali - Tana nufin gamsuwar jima'i. Misali;Lalurar sanyi na sanya saurin inzali ga ma'aurata. ENG; Orgasm (A turance tana nufin inzali)
Iri - Tana nufi abin da ake shukawa. Misali;Iri ya yi tsada yanzu shi yasa manoma ke kokawa. ENG; Seed (A turance tana nufin iri)
Ishara - Tana nufin nuni ko alama. Misali; Duk wanda ya yi mugunta sai ya ga ishara kafin ya mutu. ENG; Sign/Indication (A turance tana nufin ishara)
1 169 170 171 172 173 337