Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Hulɗa - Tana nufin mu'amala ko cuɗanya. Misali; An ƙulla hulɗar cinikayya tsakanin 'yan kasuwar. ENG; Transaction (A turance tana nufin hulɗa)
Human Rights Writers Association of Nigeria (HURIWA) - Ƙungiyar Marubuta Hakikin Dan'adam Ta Najeriya
Hunt - A turance tana nufin farauta. Misali; Samarin na shirin fita farauta yau da daddare. HAU; Farauta (Tana nufin shiga daji don kamo namun daji, don a ci ko a siyar da naman)
Hunturu - Tana nufin lokacin sanyi. Misali; Lokacin hunturu akan kunna wuta domin jin ɗumi. ENG; Cold (A turance tana nufin hunturu)
Hura - Tana nufin fito da iska ta baki. Misali; Tun ɗazu nake hura wutar ta ƙi kamawa. ENG; Blow (A turance tana nufin hura)
Hurry - A turance tana nufin gaggauta. Misali; Ku gaggauta gamawa saboda lokacin tashi ya yi. HAU; Gaggauta (Tana nufin a yi abu da sauri ko hanzari)
Husks of Rice - A turance tana nufin ɓuntu. Misali; Shinkafar da muka siyo cike take da ɓuntu, sai an gyara ta ƙwarai. HAU; Ɓuntu (Tana nufin kwanson da shinkafa ke ciki)
Hut - A turance tana nufin bukka. Misali; Fulani na gina bukka a rugagensu domin su zauna. HAU; Bukka (Tana nufin ƙaramin ɗakin da ake ginawa da busasshiyar ciyawar da ake kira da zana)
Hutu - Tana nufin zama guri ɗaya ba tare da aikin komai ba ko rashin zuwa gurin aiki ko makaranta ko gyurin sana'a na wani lokaci don a tsahirta kafin a ɗora. Misali; Yara ba sa zuwa makaranta saboda an ba su hutu. ENG; Rest/Holiday (A turance tana nufin hutu)
Huɗu - Tana nufin lambar da ke bin bayan uku. Misali; Musulunci ya ba wa maza damar auren mata guda huɗu. ENG; Four (A turance tana nufin huɗu)
1 159 160 161 162 163 337