Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Huge -
A turance tana nufin ƙato.
Misali; Gidan sabon sarki ƙato ne sosai kowa na mamakin girmansa.
HAU; Ƙato (Tana nufin girma sosai)
Huhu - Tana nufin ɓangaren da ke sarrafa iska a jikin ɗan Adam.
Misali; Shan taba yana illata huhu a wasu lokutan ma har a rasa rai.
ENG; Lungs (A turance tana nufin huhu)
Hujja - Tana nufin dalili.
Misali; Sun yi rashin nasara saboda ba su da ƙwaƙƙwarar hujja a shari'ar.
ENG; Reason (A turance tana nufin hujja)
Hukuamar Bunƙasa Binciken Sararin Samaniya Ta Ƙasa - National Space Research Development Agency (NASRDA)
)
0
Hukuma - Tana nufin gwamnati ko waɗanda ke da ƙarfin iko, da shugabancin al'umma a ƙasa da jiha da ƙananan hukumomi.
Misali; Hukuma ce ke da ikon hukunta wanda ya karya dokar ƙasa.
ENG; Government Body/Authority (A turance tana nufin hukuma)
Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Ƙasa - National Hajj commission of Nigeria (NAHCON)
Hukumar Abinci da Aikin Gona - Food & Agriculture Organization (FAD)
Hukumar Adana Jarin Kamfanoni Ta Ƙasa - National Deposit Insurance Corporation (NDIC)
Hukumar Afuwa Ta Duniya /Hukumar Bibiyar Haƙƙi Ta Duniya - Amnesty International (AI)
Hukumar Agajin Gaggawa Ta Ƙasa - National Emergency Management Agency (NEMA)