Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Horarwa - Ba da horo a kan wani ilimi na sana'a ko aiki domin kara gogewa da sabunta fahimta.
Horn -
A turance tana nufin ƙaho.
Misali; Shanu suna da ƙaho a kansu.
HAU; Ƙaho (Tana nufin wani abu mai ƙarfi da ke fitowa a kan dabba kamar shanu, awaki ko tumaki)
Horse - A turance tana nufin doki.
Misali; Almustafa ya hau doki.
HAU; Doki (Tana nufin dabba mai ƙafa huɗu wadda ma'abotra sarauta ke hawa a ƙasar Hausa)
Kishiyarta; Goɗiya
Horse-riding for pleasure - A turance tana nufin kilisa.
Misali; An shirya kilisa a bikin angwancin Abdullahi.
HAU; Kilisa (Tana nufin hawa dokuna don nishaɗi)
Hospitality & Tourism Management Association of Nigeria (HATMAN) - Ƙungiyar Gudanarwa da Tarbar Ƴan yawon Buɗe-Ido To Najeriya
Hot Embers - A turance tana nufin garwashi.
Misali; Ta yi amfani da garwashi wajen gasa cibiyar jaririn.
HAU; Garwashi (Tana nufin diddigar wuta)
Hotel & Personal Services Employers’ Association of Nigeria (HOPESEA) - Ƙungiyar masana'antun Otal da Hidimar Jama'a Ta Najeriya
Hoto - Tana nufin taswira.
Misali; Idan an gama taron za mu ɗauki hoto saboda tarihi.
ENG; Photograph (A turance tana nufin hoto)
House - A turance tana nufin gida.
Misali; Ya gina ƙaton gida a sabuwar unguwa.
HAU: Gida (Tana nufin mazauni ko gini da ake yi don ba wa kai kariya daga abin cutarwa)
Huce - Tana nufin yin sanyi.
Misali; Abincin da na kawo har ya huce kuna hira.
ENG; Cool Off (A turance tana nufin huce)