Terms Dictionary

Whole - A turance tana nufin ilahiri. Misali; Ya shafe ilahirin jikinsa da maganin. HAU; Ilahiri (Tana nufin duka ko gaba ɗaya ko bai ɗaya)
wikiHausa - wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.
Wisdom - A turance tana nufin hikima. Misali; Ya yi amfani da hikima wajen daidaita abokan da suka samu saɓani. HAU; Hikima (Tana nufin dabara ko baiwa)
Wish - A turance tana nufin buri. Misali; Zuwa ƙasa mai tsarki shi ne babban buri na. HAU; Buri (Tana nufin abinda mutum yake so ya cimma)
With - A turance tana nufin da. Misali; Ni da yayana farare ne. HAU; Da (Tana nufin tare)
Without - A turance tana nufin babu. Misali; Babu kaya a cikin akwatin. HAU; Babu (Tana nufin wayam ko ba komai)
Woman’s Head-tie - A turance tana nufin kallabi. Misali; Ƙanwata ta iya ɗaura kallabi. HAU; Kallabi (Tana nufin ɗan kwali ko fatala)
Woman’s Large Wrapper - A turance tana nufin gyauto. Misali; Ta ɗaura gyauto mai matuƙar kyau da tsada. HAU; Gyauto (Tana nufin babban zani na mata)
Woman’s Shawl - A turance tana nufin gyale. Misali; Kande ta yafa sabon gyale. HAU; Gyale (Tana nufin mayafi ko abin rufe jiki na mata)
Woman’s Underskirt - A turance tana nufin fatari. Misali; Ta shanya fatari a igiya bayan ta wanke. HAU; Fatari (Tana nufin siket ɗin da mata suke sa wa a ƙasan kaya)
1 291 292 293 294 295 300