Terms Dictionary

Watermelon - A turance tana nufin kankana. Misali; Kankana ta fi yawa a cikin kayan marmarin da muka siyo. HAU; Kankana (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan maramari mai ɗauke da ruwa sosai a ciki)
Wealth - A turance tana nufin daula. Misali; Lami tana cikin daula saboda mijinta yana da kuɗi. HAU; Daula (Tana nufin dukiya ko kayan alatu da ƙawa na duniya)
Wealthy person - A turance yana nufin mutum mai dukiya. Misali; Maƙocinmu attajiri ne. Kishiyarta; Talaka HAU; Attajiri (Mutum mai tarin dukiya)
Wednesday - A turance tana nufin rana ta uku a mako.   Misali; Ranar Laraba za a fara jarabawar. HAU;Laraba (Rana ce ta uku a cikin ranakun mako)
West Afirican College of Surgeons (WACS) - Kwalejin Likitocin Fiɗa Ta Yammacin Afirka
West African College of Physicians (WACP) - Kwalejin Likitocin Afirka Ta Yamma
West African Examination Council (WAEC) - Hukumar Jarabawar Afirka Ta Yamma
West African Football Union (WAFU) - Hukumar Kwallo Kafa Ta Yammacin Afirka
West African Institute for Financial and Economic Management (WAIFEM) - Cibiyar Nazarin Ciniki da Tattalin Kuɗi Ta Yammacin Afirka
West African Journalists Association (WAJA) - Ƙungiyar 'Ƴanjarida Ta Yammacin Afirka
1 289 290 291 292 293 300