West African Linguistic Society (WALS) - Ƙungiyar Masana Kimiyyar Harshe Ta Yammacin Afirka
West African Monetary Institute (WAMI) - Cibiyar Ƙuɗin Bai-Ɗaya Ta Yammacin Afirka
West African Monetary Union (WAMU) - Hukumar Kuɗin Baiɗaya Ta Yammacin Afirka
West African Research Association (WARA) - Ƙungiyar Manazarta Ta Yammacin Afirka
West African Women Association (WAMA) - Ƙungiyar Matan Afirka Ta Yamma
Where - A turance tana nufin inda.
Misali; Mukullin yana inda nake ajiye kayana.
HAU; Inda (Tana nufin gurin da abu yake)
Whip - A turance tana nufin bulala.
Misali; Malam ya zane ɗaliban da suka makara da bulala.
HAU; Bulala (Tana nufin busasshiya kuma nannaɗaɗɗiyar fata da ake amfani da ita wajen duka)
Whip, Flog - A turance tana nufin fyaɗa.
Misali; Ai alamajirin nan ya sha fyaɗa a gurin malaminsu.
HAU; Fyaɗa (Tana nufin duka musamman da tsumagiya)
Whirlwind - A turance tana nufin guguwa.
Misali; Bishiyar ta faɗo ne yayin da ake guguwa.
HAU; Guguwa (Tana nufin iska mai ƙarfi)
Whistling - A turance tana nufin fito.
Misali; Waye yake fito a waje?
HAU; Fito (Tana nufin fitar da iska da baki har ya ba da wata siririyar ƙara)