Terms Dictionary

World Trade Organization (WTO) - Hukumar Kasuwanci Ta Duniya
World Youth Organization (WYO) - Kadaurar Matasa Ta Duniya
Worn-out palm-leaf mat - A turance tana nufin keso. Misali; An ɗora buhun geron a kan keso. HAU; Keso (Tana nufin tsohuwar tabarmar kaba)
Worship - A turance tana nufin bauta. Misali; Musulmai sun yarda da Allah shi ne kaɗai abin bauta. HAU; Bauta (Tana nufin sadaukarwa da biyayya ga abinda mutum ya yarda da shi)
Worth, Value - A turance tana nufin daraja. Misali; Zinare na da daraja a halin yanzu. HAU; Daraja (Tana nufin muhimmanci ko tsada)
Wrestling - A turance tana nufin kokawa. Misali; Su Lado sun tafi kallon kokawa a dandali. HAU; Kokawa (Tana nufin ɗaya daga cikin wasannin gargajiya, inda maza biyu ke doke-doke a tsakaninsu har a kayar da ɗaya)
Yam - A turance tana nufin doya. Misali; Doya za mu dafa yau da rana. HAU; Doya (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abinci wanda ke sa ƙarfin jiki)
Yandagaji - Waɗanda ba kwararrun 'yanwasa ba a harkar wasanni.
Yawning - A turance tana nufin hamma. Misali; Tun ɗazu nake hamma saboda yunwa nake ji matuƙa. HAU; Hamma (Tana nufin fitar da iska ta hanyar buɗe baki wanda jin yunwa ko bacci ke sa wa)
Yelling - A turance tana nufin ihu. Misali; Matasan na ihu ne don sun ci ƙwalo. HAU: Ihu (Tana nufin ƙara ko fitar da sauti da ƙarfi)
1 293 294 295 296 297 300