Yesterday - A turance tana nufin jiya.
Misali; Jiya ban je makaranta ba saboda babanmu ya aike ni.
HAU; Jiya (Tana nufin ranar da ta gabata kafin yau)
Youghurt - A turance tana nufin kindirmo.
Misali; Ina son shan kindirmo da safe.
HAU; Kindirmo (Tana nufin Nonon da ya kwana ya yi kauri)
Young cow who has not yet given birth - A turance tana nufin karsana.
Misali; Naman karsana yana da taushi da sauƙin dahuwa.
HAU; Karsana (Tana nufin matashiyar saniya wadda ba ta taɓa haihuwa ba)
Yuli - Wata ne na bakwai a shekara.
Misali; A watan Yuli zai cika shekara biyar da gama makaranta.
ENG; July (A turance yana nufin wata na bakwai a shekara)
Yuni - Wata na shida a shekara.
Misali; Damina na kankama a watan Yuni.
ENG; June (A turance wata ne na shida a shekara)
Zayyana - Aikin zana tsari da yadda zubin mahalli, kamar gida zai kasance a gine.
Ɓaci - Tana nufin lalacewa.
Misali; Rigar ta ɓaci da amai sai an sake wata.
ENG; Spoiled (A turance tana nufin ɓaci)
Ɓagas - Tana nufin samun abu cikin sauƙi ba tare da an sha wahala ba.
Misali; A ɓagas y samu kayan da ya siyo.
ENG; Cheaply (A turance tana nufin ɓagas)
Ɓararraka - Tana nufin dahuwa ba ƙaƙƙautawa.
Misali; Waken yana ta ɓararraka tun ɗazu.
ENG;Boil Continuously (A turance tana nufin ɓararraka)
Ɓarawo - Tana nufin mutumin da yake sata.
Misali;An kama ɓarawo a gidan Alhaji Iro jiya da daddare.
ENG; Thief (A turance tana nufin ɓarawo)