Majibanta - Masu taimakawa jama'a
Majority - A turance tana nufin galibi.
Misali; Galibi akan yi ruwa mai yawa a watan Agusta.
HAU; Galibi (Tana nufin mafi yawa)
Makamashi - Sinadarin da ake hada wuta ko makami da shi kamar itace ko uraniyam.
Makaranta - Makaranta wuri na koyon ilimi wanda mutane suke zuwa dan koyon karatu,kamar yara ko manya jinsin maza da mata suke zuwa dan koyon ilimin addini ko na boko.
makaraya - Masu kai ƙara kotun shari'a, waɗanda suke shari da wani/wasu a gaban Alƙali.
Make Slushy - A turance tana nufin caɓa.
Misali; Amaryar ta caɓa ado sosai.
HAU; Caɓa (Tana nufin yin ado da yawa)
Makimanta - Masu kimanta darajar ƙasa ko gida, musamman wajen kimanta darajar muhalli.
Male Hyena - A turance tana nufin kure.
Misali; Auwalu ya kamo kure, da shi yake wasa ranar kasuwa.
HAU; Kure (Tana nufin namijin kura)
Man’s charm worn around the arm - A turance tana nufin kambu.
Misali; Gaba ɗaya mafarautan suna ɗauke da kambu a hannunsu.
HAU; Kambu (Tana nufin wani nau'in surkulle da maza ke ɗaurawa a hannu musamman mafarauta da 'yan dambe)
manufacturers Association of Nigeria (MAN) - Ƙungiyar Kamfanonin Ƙere-Ƙere-Ta Najeriya