Terms Dictionary

Liver - A turance tana nufin hanta. Misali; Farfesun hanta zan dafa a matsayin karin kumallo. HAU; Hanta (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan ciki wadda ke tace jini da fitar da datti daga cikin jini)
Local Authority Administrator - A turance tana nufin kantoma. Misali; An naɗa baban su Sharif kantoma a ƙaramar hukumar Dala. HAU; Kantoma (Tana nufin mai riƙon ƙwaryar shugabancin ƙaramar hukuma)
Local Government Council - Majilisar Ƙaramar Hukuma
Lock - A turance tana nufin kulle. Misali; Lokacin da muka je an kulle ƙofar saboda mun makara. HAU; Kulle (Tana nufin rufewa)
Locust bean - A turance tana nufin daddawa. Misali; Miyar kuka ta fi daɗi idan ta ji daddawa. HAU; Daddawa (Tana nufin sinadarin girki mai sa ƙamshi da armashin abinci)
Long metal horn blown in honour of an Emir - A turance tana nufin kakaki. Misali; Da ka ji kakaki to sarki ya fito daga fada. HAU; Kakaki (Tana nufin abin busa na ƙarfe wanda sarki kaɗai ake busawa)
Long sleeve worn as inner garment - A turance tana nufin jamfa. Misali; Ya sa jamfa mai gajeren hannu kalar makuba. HAU; Jamfa (Tana nufin rigar da ake sa wa a ƙasa kafin a ɗora babbar riga)
Looting in a noisy manner - A turance tana nufin ɓuruntu. Misali; Ɓera yana ta ɓuruntu a ɗakin Kaka. HAU; Ɓuruntu (Tana nufin ɓare-ɓare da hayaniya)
Lose Interest - A turance tana nufin gundura. Misali; Kallon wasan ƙwallon ƙafa ya gundure ni. HAU; Gundura (Tana nufin jin abu ya fita daga rai)
Losing Baby Teeth - A turance tana nufin famfara. Misali; Muntari yana famfara. HAU; Famfara (Tana nufin cirewar da haƙoran yara ke yi kafin na girma ya fito)
1 202 203 204 205 206 300