Terms Dictionary

Left handed person - A turance yana nufin bahago. Misali; Ado bahago ne. HAU; Bahago (Yana nufin wanda yake amfani da hannun hagu ko kuma mutum mai wuyar sha'ani)
Left-over Food - A turance tana nufin dago-dago. Misali; Akwai dago-dago a ɗakin girki, a ba wa almajirai idan sun yi bara. HAU: Dago-dago (Tana nufin ragowar abinci)
Legal Aids Council of Nigeria (LACON) - Hukumar Tanyon Maƙaraya Ta Najeriya
Legion - Ƙungiya
Leken Asiri - Bibiyar al'amuran jama'a ko na wata kasa don gano  wasu abubuwa na tsaro.
Leopard - A turance tana nufin damisa. Misali; Akwai ƙaton hoton damisa a ƙofar fadar sarkin. HAU; Leopard (Tana nufin dabbar daji mai cin nama)
Leper - A turance tana nufin kuturu. Misali; Ya ba wa kuturu sadaka a hanyarsa ta zuwa kasuwa. HAU; Kuturu (Tana nufin mai ɗauke da lalurar kuturta)
Leprosy - A turance tana nufin kuturta. Misali; Gwamnati ta daɗe da yaƙar cutar kuturta a ƙasar nan. HAU; Kuturta (Tana nufin lalurar da ke sa ƙuraje a jiki, ta canja siffar mutum gaba ɗaya kuma yatsu su lanƙawashe)
Lesson - A turance tana nufin darasi. Misali; Malamin na koyar da darasin Lissafi. HAU; Darasi (Tana nufin abin da za a koya)
Leucoma - A turance tana nufin hakiya. Misali; Hakiya ce ta fito masa a ido. HAU; Hakiya (Tana nufin ciwon da ke fitowa a cikin ido)
1 200 201 202 203 204 300