Terms Dictionary

Last year - A turance tana nufin bara. Misali; Bara ya cika shekara biyar da rasuwa. HAU; Bara (Shekarar da ta gabata)
Last year’s kolanuts - A turance tana nufin daushe. Misali; Gwaggo ta fi son goro daushe. HAU; Daushe (Tana nufin tsohon goro)
Later - A turance tana nufin bisani. Misali; An ɗauke min kuɗina amma daga bisani an dawo min da su. HAU; Bisani (Tana nufin daga baya ko kuma bayan)
Laugh - A turance tana nufin dariya. Misali; Jama'a na ta dariya sakamakon ganin ɗan wasan barkwancin da suka yi. HAU; Dariya (Tana nufin canja yanayin fuska tare da bayyana haƙora sakamakon wani abin farin ciki ko nishaɗi)  
Leader/Guide - A turance tana nufin ja-gaba. Misali; Annabi SAW shi ne ja-gaban dukkan halitta. HAU; Ja-gaba (Tana nufin shugaba ko jagora)
League - Hukuma, Ƙungiya
League Management Company (LMC) - Kamfanin Harkokin Wasanni
Leaves of Guinea-corn - A turance tana nufin karmami. Misali; Da ya bi shi da gudu, cikin karmami ya shige. HAU; Karmami (Tana nufin ganyen dawa)
Leaves or stalk of beans, groundnut etc - A turance tana nufin harawa. Misali; Dabbobin na cinye buhun harawa biyu a mako guda. HAU; Harawa (Tana nufin busasshen ganyen wake ko na gyaɗa da sauransu wanda ake ba wa dabbobi)
Left - A turance tana nufin hagu. Misali; Da hannun hagu yake rubutu. HAU; Hagu (Tana nufin ɓarin hagu a jikin ɗan Adam, idan aka kalli mutum daga sama zuwa ƙasa, ɓari ɗaya shi ne hagu ɗayan kuma dama) Kishiyarta; Dama
1 199 200 201 202 203 300