Kwaleji - Tana nufin makarantar gaba da firamare ko gaba da sakandire.
Misali; Duk wanda zai shiga kwaleji sai ya yi jarrabawa.
ENG; College (A turance tana nufin kwaleji)
Kwaleji - Tana nufin makaranta musamman ta gaba da sakandire.
Misali; Idan matasa suka shiga kwaleji suna jin kansu.
ENG; College (A turance tana nufin kwaleji)
Kwalekwale - Tana nufin ƙaramin jirgin ruwa.
Misali; Ba a zuwa ƙauyen sai an hau kwalekwale.
ENG; Canoe (A turance tana nufin kwalekwale)
Kwalli - Tana nufin nau'in abin ado da ake sa wa ido don ƙara masa kyau da ƙwari.
Misali: Kwaliiya ta ba ta cika sai na sa kwalli a idona.
ENG: Antimony (A turance tana nufin kwalli)
Kwaɓa - Tana nufin haɗa abu da ruwa a jujjuya.
Misali; Farida ta kwaɓa miki fanken mana, za ki samu sauƙin aikin.
ENG; Mix Something (A turance tana nufin kwaɓa)
Kwaɗayi - Tana nufin tsananin son cin abu ko yin abu.
Misali; Tun da ta fara kwaɗayi na san tana da juna biyu.
ENG; Craving/ Yearning (A turance tana nufin kwaɗayi)
Kwaɗo - Tana nufin wata dabba da ke rayuwa a ruwa kuma da doron ƙasa.
Misali; Tahir ya ga kwaɗo a bakin kwatar da ke ƙofar gidansu.
ENG; Frog (A turance tana nufin kwaɗo)
Lack - A turance tana nufin fatara.
Misali; Gidan suna fatarar abinci.
HAU; Fatara (Tana nufin rashin kuɗi ko abin duniya)
Lack of Energy - A turance tana nufin kasala.
Misali; Jin kasala na ɗaya daga cikin alamomin juna biyu.
HAU; Kasala (Tana nufin mutuwar jiki ko rashin jin ƙarfin jiki)
Lahadi - Rana ce ta ƙarshe a mako.
Misali; A kan ɗaura aure a ranar Lahadi.
ENG; Sunday (A turance tana nufin Lahadi, rana ta ƙarshe a mako)