Lost - A turance tana nufin ɓata.
Misali; Ina tunanin takalmin ya ɓata, don na duba ko ina ban ganshi ba.
HAU; Ɓata (Tana nufin a nemi abu a rasa)
Loud Argument - A turance tana nufin hatsaniya.
Misali; Mata da mijin sun yi hatsaniya har ta kai matar ta yi yaji.
HAU; Hatsaniya (Tana nufin cacar baki ko cece-kuce)
Loud Fuss - A turance tana nufin kwakwazo.
Misali; Tun safe Lami take kwakwazo don an ɗauke mata kuɗi a gidan suna.
HAU; Kwakwazo (Tana nufin hayaniya da hayagaga)
Low mud platform outside compound - A turance tana nufin dakali.
Misali; Baba yana zaune a kan dakali da abokinsa suna hira.
HAU; Dakali (Tana nufin gini mai ɗan tudu da ake yi a ƙofar gida don zama)
Lungs - A turance tana nufin huhu.
Misali; Shan taba yana illata huhu a wasu lokutan ma har a rasa rai.
HAU; Huhu (Tana nufin ɓangaren da ke sarrafa iska a jikin ɗan Adam)
Ma’adinai - Albarkar ko arzikin da ake samu ko hakowa daga karkashin kasa kamar zinare (gwal) ko tama ko azurfa ko mai da makamantansu.
Mabada - masu ba wa mutane musamman dalibai a makarantu shawarwari game da rayuwa da kuma cigaban karatunsu.
Mabambanta - Abubuwa masu bambanci da juna ta wasu fuskoki na musamman.
Madness - A turance tana nufin hauka.
Misali; Ya shekara goma yana fama da ciwon hauka.
HAU; Hauka (Tana nufin rashin ciwon rashin hankali ko gushewar hankali)
Kishiyarta; Hankali
Mahuldanta - Mutane masu kwarewa wajen kai-komo a tsakani ko iya saurarar koken abokan hulda a ma'aikatu da masana'antu.