Terms Dictionary

Iska - Tana nufin abin da ke kaɗawa kuma ababen halitta ke shaƙa don su rayu. Misali; Tun safe iska mai sanyi take kaɗawa yau. ENG; Air (A turance tana nufin iska)
ISlamic Medical Association of Nigeria (IMAN) - Ƙungiyar Likitoci Musulmai Ta Najeriya
Istihara - Tana nufin neman zaɓin Allah. Misali; Ya kamata ki yi istihara a tsakanin masu neman auren ki. ENG; Seeking Devine Counsel (A turance tana nufin istihara)
Itace - Tana nufin bishiya. Misali; Wannan itacen ɗorawa ne. ENG; Tree (A turance tana nufin bishiya)
Iyaka - Tana nufin ƙarshe.  Misali; Komai na Allah yana da iyaka kuma iyakokin Allah su ne abin kiyayewa. ENG; Boundary (A turance tana nufin iyaka)
Iyali - Tana nufin ahali ko kuma uwa da uba da yaransu. Misali; Yana kula da iyali yanda ya kamata. ENG; Family (A turance tana nufin iyali)
Iyawa - Tana nufin ikon yin abu. Misali; Duk abin da aka sa shi yana iyawa don yana da cikakkiyar lafiya. ENG; Ability (A turance tana nufin iyawa)
Iyaye - Tana nufin mahaifi da mahaifiya. Misali; Wajibi ne biyayya ga iyaye idan mutum yana son gamawa lafiya. ENG; Parents (A turance tana nufin iyaye)
Izga - Tana nufin jela musamman ta doki da ake amfani da ita wajen korar ƙuda. Misali; Da izga yake amfani don kore ƙuda daga kan kayan sana'arsa. ENG; Tail used as fly-switch (A turance tana nufin izga)
Izgili - Tana nufin wulaƙanci ko ƙasƙantarwa musamman ga abu mai daraja. Misali; Bayan ya yi wa iyayensa izgili rayuwarsa rugujewa ta yi. ENG; Being Presumptuous (A turance tana nufin izgili)
1 160 161 162 163 164 300