Izifi - Tana nufin ɗaya daga cikin kaso sittin na Ƙur'ani.
Misali; Abdallah ya haddace izifi biyu a watan da ya gabata.
ENG; One of the sixty sections into which the Qur'an is divided (A turance tana nufin izifi)
Izini - Tana nufin dama ko yarda ko amincewa.
Misali; An ba shi izini ya fito neman auren Binta.
ENG; Permission (A turance tana nufin izini)
Izza - Tana nufin jin isa da faɗin rai.
Misali; Sarautar da aka naɗa shi ta sa shi jin izza.
ENG; Haughtiness (A turance tana nufin izza)
Ja - Tana nufin launin ja.
Misali; Akwai launin ja a jikin kayan da ya saka.
ENG; Red (A turance tana nufin ja)
Ja - Tana nufin janyowa.
Misali; Ya ja igiyar da ƙarfi shi yasa ta tsinke.
ENG; Pull/Drag (A turance tana nufin ja)
Ja’iba - Tana nufin masifa ko rashin sa'a ko ibtila'i.
Misali; Ya ga ja'iba, bayan ya rasa ɗansa shagonsa ya kama da wuta.
ENG; Misfortune/Calamity (A turance tana nufin ja'iba)
Ja’iri - Tana nufin mara kunya.
Misali; Babu mai yin rawar Gala sai ja'iri.
ENG; Shameless/Disrespectful Person (A turance tana nufin ja'iri)
Ja-gaba - Tana nufin shugaba ko jagora.
Misali; Annabi SAW shi ne ja-gaban dukkan halitta.
ENG; Leader/Guide (A turance tana nufin ja-gaba)
Jabu - Tana nufin abin da ba shi da inganci.
Misali; Madarar jabu ce, idan aka sha tana sa ciwon ciki.
ENG; Fake (A turance tana nufin jabu)
Jackal - A turance tana nufin dila.
Misali; Akwai dila a cikin dabbobin da na gani a gidan ajiye namun daji.
HAU; Dila (Tana nufin wata dabba mai kama da akuya amma ta fi akuya siranta)