Terms Dictionary

Jaddada - Tana nufin tabbatarwa. Misali; Shugaban makarantarmu ya jaddada mana muhimmancin taron iyayen yara da za a yi gobe. ENG; Reform (A turance tana nufin jaddada)
Jagab - Tana nufin tsananin jiƙewa. Misali; Ruwa ya jiƙa su jagab saboda ba su daɗe da fita ba ya sakko. ENG; Very Wet (A turance tana nufin jagab)
Jahili - Tana nufin wanda ba shi da ilimi. Misali; Rashin zuwa makaranta ne ke mai da mutum jahili. ENG; Illiterate Person (A turance tana nufin jahili)
Jaje - Tana nufin taya alhini da tausayawa wanda wani abu mara daɗi ya same shi. Misali; Shugaban ƙasa ya yi wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa jaje. ENG; Sympathy (A turance tana nufin jaje)
Jajibere - Tana nufin kwana ɗaya kafin ranar biki (sallah ko wani shagali). Misali; Yau jajiberen ƙaramar sallah. ENG; Day before festival day (A turance tana nufin jajibere)
Jaka - Tana nufin abar da ake ratayawa a kafaɗa ko a riƙe a hannu, ana zuba kuɗi da kayayyaki a ciki. Misali; A kasuwa aka sace mata jaka kuma duk kuɗinta suna ciki. ENG; Bag (A turance tana nufin jaka)
Jakada - Tana nufin wakili. Misali; An naɗa babanta jakadan Nageriya a ƙasar Niger. ENG; Ambassador (A turance tana nufin jakada)
Jaki - Tana nufin dabba mai ƙafa huɗu wanda ake amafani da shi don ɗaukar kaya, yana da juriya sosai. Misali; Malam Mudi yana wani tsohon jaki. ENG; Donkey (A turance tana nufin jaki)
Jalla - Tana nufin Allah maɗaukakin sarki. Misali; Allah jalla wa azza ne ya nufa za a yi ruwa mai yawa yau. ENG; God (A turance tana nufin jalla)
Jallo - Tana nufin mazubin ruwa na duma. Misali; Jauro ya shanye ruwan cikin jallo na, sai na ɗebo wani. ENG; Gourd Water Bottle (A turance tana nufin jallo)
1 162 163 164 165 166 300