Tag: yadda ake

  • Sallar Asham Da Raka’o’inta

    Sallar Asham Da Raka’o’inta

    Sallar Asham ita ce nafilfili da ake yi a bayan sallar Isha’i a cikin watan Ramadan, wato da zarar labarin ganin wata ya bayyana, domin wannan dare na Ramadan ne. Sannan yin ta cikin jam’i, sunna ce.

    Hadisi ya tabbata daga Nana A’isha (Radiyallahu Anha) cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya fita a wata rana da tsakar dare, sai ya yi sallah a Masallaci, sai wasu cikin sahabbai suka bi shi. Da gari ya waye sai mutane suka ba wa junansu labari, da dare ya yi sai yawan mutane ya ƙaru, sai ya yi sallah su ma suka bi Shi.

    Da gari ya waye sai mutane suka ƙara bai wa junansu labari, sai Masallaci ya cika a dare na uku, sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya fito ya yi sallah. A dare na huɗu mutane suka taru har Masallaci ya gaza ɗaukarsu; sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ƙi fitowa har zuwa sallar Asubahi.

    Yayin da ya idar da sallar Asubahin, sai ya juyo ya fuskanci mutane, Ya ce; “Lalle halinku bai ɓuya gare Ni ba; sai dai Ni na ji tsoron kada a wajabta muku ita ku zo ku gaza”. (Bukhari 3/220, Muslim 761).

    Bayan wafatin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) shari’a ta gama cika, tsoron da ake ji ya kau; sai Sayyadina Umar Bin Khaɗɗab (Radiyallahu Anhu) ya raya wannan Sunnah; kamar yadda Abdulrahman Bn Al-ƙariy ya faɗa cewa; “Na fita tare da Umar Bn Khaɗɗab a wani dare cikin Ramadan zuwa masallaci, sai ga mutane a warwatse, wani yana sallah shi kaɗai; wani yana sallah da yan mutane kaɗan.

    Sai Umar ya ce: “Ni ina ganin da a ce na haɗe mutane bayan karatu ɗaya da ya fi kamata”.

    Sai ya yi ƙoƙarin haɗe su a bayan Ubayyu Ibn Ka’ab (Radiyallahu Anhu). Sannan muka fita tare da shi a wani daren, mutane suna sallah a bayan limaminsu, sai Umar ya ce; “Madalla da wannan sabon abu…”

    Game da adadin raka’o’inta kuwa, ya zo cikin hadisin Nana A’isha (Radiyallahu Anha) cewa; “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam ba ya wuce raka’a goma sha ɗaya a Ramadan ko waninsa”. (Bukhari: 1147). Sannan ta bayyana yadda kyawun wannan sallah take; da kuma yadda yake jimawa a tsaye, wanda har ƙafafuwanSa ke kumbura saboda tsayuwa.

    Hadisi daga Jabir Bn Abdullahi (Radiyallahu Anhu) cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) yayin da ya raya daren Ramadan da mutane; ya yi sallah raka’a takwas sannan ya yi wutiri. (Ibn Hibban 920).

    Domin karanta cikakken bayani akan Ma’anar Azumi A Musulunci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Kaffarar Azumin Ramadan danna nan.

    Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Zakkar Fid-Da-Kai

    Zakkar Fid-Da-Kai

    Zakkar fid-da-kai sunnah ce daga cikin sunnonin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), domin ya fitar kuma sahabban Sa masu albarka ma sun fitar. Shari’a ta shar’anta wannan zakka domin tsarkake masu azumi daga yasasshen zance da batsa; kuma ciyarwa ga miskinai inda za ta wadatar da su a ranar sallah ta farin ciki.

    Hadisi daga Abdullahi Bn Umar (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam)ya farlanta zakkar fid-da-kai ta bayan Ramadan kan mutane” (Bukhari 3/291, Muslim 984). Haka zalika hadisin Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu), wanda Abu Dawud da Nasa’i suka fitar ya nuna hakan.

    Hadisi ya tabbata daga Abu Sa’id Alkhudri (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Mun kasance muna bayar da ita a zamanin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) sa’i ɗaya daga abinci; ko sa’i ɗaya daga dabino, ko sa’i ɗaya daga alkama, ko sa’i ɗaya daga zabibi (busasshen inibi). A wata ruwayar “Sa’i ɗaya daga cikwi”. (Bukhari 1508, Muslim 985).

    Ana fitar wa yaro, babba, mace, namiji da kuma bawa da ‘yantacce; saboda hadisin Abdullahi Bn Umar (Radiyallahu Anhu) da ya ce; “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi umarni a fitar wa yaro, babba, bawa da ‘yantaccen daga waɗanda kuke ɗaukar nauyinsu”.

    (Darukuɗniy 2/141, Baihaƙiy 4/161).

    Sannan ana bayar da ita ce kafin tafiya sallar idi, ba ya halarta a jinkirta ta har zuwa lokacin sallah; koda kwana ɗaya ko biyu kafin ranar sallah; ya halatta a fitar saboda abin da ya zo daga aikin Abdullahi Bn Umar (Radiyallahu Anhu).

    Ya zo cikin hadisin Abdullahi Bn Abbas (Radiyallahu Anhu) cewa; “….. wanda duk ya bayar da ita kafin sallah, to ya yi ta karɓaɓɓiya; wanda kuma ya bayar bayan an yi sallah, to sadaka ce daga cikin sadakoki”.

    Domin karanta cikakken bayani akan Azumin Kwanaki Shida A Watan Shawwal (Sitta Shawwal) danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Azumin Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijja danna nan.

    Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Ma’anar Azumi A Musulunci

    Ma’anar Azumi A Musulunci

    Azumi a Shari’a shi ne: kamewa daga barin ci da sha da jima’i da abin da zai ɗauki hukuncinsu; tun daga fitowar Alfijir; har zuwa faɗuwar rana ga keɓantattun mutane da niyyar bauta wa Allah.

    Domin karanta cikakken bayani akan Dalilan Wajabcin Azumin Ramadana danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Sallar Ƙiyamul Laili (TAHAJJUD) danna nan

    Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Watan Ramadan (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Cikakken Bayani A Kan Sahur

    Cikakken Bayani A Kan Sahur

    Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya kwaɗaitar da yin sahur; har Ya ambata cikin falalar sahur a hadisin Anas Ibn Malik Radiyallahu Anhu cewa, “Ku yi sahur, domin haƙiƙa akwai albarka a cikin yin sahur” (Sahihul Bukhari 1923).

    An karɓo hadisi daga Salman (Radiyallahu Anhu) cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Albarka na cikin abu uku: jama’a, abincin rashi da kuma abincin sahur”. (Ɗabrani cikin Mu’ujamul Kabir 6127).

    Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ambaci sahur da kumullo mai albarka; kamar yadda yake cikin hadisin Al’irbadh Bn Sariyata, da Abud-Darda’a (Radiyallahu Anhu) cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Ku taho mu yi kumullo mai albarka, yana nufin sahur”.

    Haka nan hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa; “Sahur abinci ne mai albarka. Don haka kada ku bar shi, ko da ruwa ne ɗayanku ya kurɓa. Haƙiƙa Allah da mala’ikunsa na yin salati ga masu yin sahur”. (Sahih Targhib wal Tarhib 1066).

    Sannan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bambanta azuminmu da na ma’abota littafi (Yahudu da Nasara); da sahur, kamar yadda ya ce, “Bambancin da ke tsakanin azuminmu da na ma’abota littafi; shi ne yin sahur”. (Sahih Muslim 1096).

    Game da lokacin da ake yin sahur ko bari kuwa, akwai hadisai da suka zo a kai. An karɓo hadisi daga Anas Ibn Malik (Radiyallahu Anhu), daga Zaid Ibn Thabit (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Mun yi sahur tare da Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) sannan sai ya tashi zuwa sallah. Sai na cewa Anas, “Yaya tsawon da ke tsakanin kiran sallah da yin sahur ɗin yake? Sai ya ce; “Gwargwadon karanta ayoyi hamsin”. (Bukhari 1921, Muslim 1097).

    Wani hadisi daga Sahl Ibn Sa’ad ya ce; “Na kasance ina yin sahur cikin iyalina; bayan wannan sai na yi gaggawa domin samun sujada (sallah) tare da Manzon Allah(Sallallahu Alaihi Wasalam)”. (Bukhari 1920).
    Wannan hadisi ya nuna ana yin sahur ne dab da ketowar alfijir.

    Amma yayin da mutum ke yin sahur, sai alfijir ya keto, to zai ƙarasa cin abincinsa ne; dogaro da hadisin Abu Huraira (Radiyallahu Anhu)cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Idan ɗayanku ya ji kiran sallah alhali ƙwarya tana hannunsa, kada ya ajiye ta, har sai ya biya buƙatarsa”. (Abu Dawud 2060).

    Amma a nan mutum ya yi hattara kada ya mayar da wannan ita ce ɗabi’arsa; wato jinkirtawar da zai fita daga lokaci.

    Wani abin lura game da alfijir, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya nuna iri biyu ne cikin hadisin da aka karɓo daga Ibn Abbas, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Alfijir iri biyu ne, na farko ba ya haramta abinci; kuma ba ya halatta sallah, na biyu kuwa yana haramta abinci, yana halatta sallah”.

    A wannan gaɓar, wajibi a ja hankalin ladanai waɗanda ke kiran sallah, wato lokacin da ake daina yin sahuur; domin ba sa kula da fitowar alfijir. Misali, a kalandar Jihar Yobe; alfijir zai hudo a farkon azumi da misalin ƙarfe 4:37 a bana; yayin da a ƙarshen azumi zai kai ƙarfe 4:40. To amma za ka ga ladanai ba sa kiran sallar daina sahur (assalatu), sai misalin ƙarfe 4:55; wasu ma sai ƙarfe 5:00, alhali da yawa daga cikin mutane sun dogara ne da kiran assalatu wajen daina cin abinci.

    Haƙiƙa ladanai su sani, yin hakan kuskure ne da kuma ɗaukan haƙƙin al’umma; don haka su ji tsoron Allah, da sannu za su tsaya a gabansa, kuma za a tambaye su kan dukkan abin da suka aikata.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Buɗa-baki danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ɗabi’ar Lokaci, Saurin Wucewa danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Cikakken Bayani A Kan Buɗa-baki

    Cikakken Bayani A Kan Buɗa-baki

    Buɗa Baki – Ana buɗa-baki da zarar rana ta faɗi, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalaml) ya yi umarni wajen gaggauta yin buɗa-baki; kamar yadda ya zo cikin hadisin Sahal Bn Sa’ad (Radiyallahu Anhu) cewa; Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam Ya ce; “Mutane ba za su gushe cikin alheri ba, matuƙar suna gaggauta buɗa-baki”. (Bukhari 4/173).

    An karɓo hadisi daga Abu Huraira Radiyallahu Anhu cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Addini ba zai gushe ba yana mai galaba, matuƙar mutane na gaggauta buɗa-baki; domin Yahudawa da Nasara suna jinkirtawa”. (Abu Dawud 2355).
    Har ila yau, wani hadisi daga Abu Darda’i (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Abubuwa uku suna cikin ɗabi’un annabawa: gaggauta buɗa-baki; jinkirta sahur da ɗora hannun dama a kan na hagu lokacin sallah”. (Sahihul Jami’u 3034).

    Game da abin da mutum zai fara buɗa-baki da shi kuwa, an karɓo Hadisi daga Anas (Radiyallahu Anhu) cewa; “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance yana buɗa-baki da ɗanyen dabino kafin ya yi sallah; idan kuma bai samu ba sai ya yi da busasshe, idan kuma bai samu ba, sai ya kurɓi makwarkwatai na ruwa”. (Abu Dawud 2/306, Tirmizi 3/70).

    Hadisi ya tabbata daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Addu’o’i uku karɓaɓɓu ne: addu’ar mai azumi, da wanda aka zalunta, da matafiyi”. (Sahihul Jami’u 3027).

    A wani hadisi daban ruwayar Tirmizi; Ibn Majah da Ibnu Hibban cikin hadisin Abu Huraira (Radiyallahu Anhu), Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa ya yi; “Mutum uku ba a dawo da addu’arsu: mai azumi yayin da yake buɗa-baki, da shugaba adali, da addu’ar wanda aka zalunta”.

    An karɓo hadisi daga Abdullahi Ibn Amru Ibn Aas (Radiyallahu Anhu) cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Waasalam) ya ce; “Haƙiƙa mai azumi yayin buɗa-bakinsa yana da addu’ar da ba a ƙin karɓa”. (Ibnu Majah 1/557, Hakim 1/239).

    Mafificiyar addu’a yayin shan ruwa ita ce, addu’ar da aka rawaito daga bakin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) mafi tsarki.

    Wannan addu’a ita ce:

    “Zhahabaz Zama’u Wabtallatil Uruk Wathabatal Ajru Insha Allah”.

    Ma’ana: “Ƙishirwa ta tafi, jijiyoyi sun jiƙu; kuma lada ya tabbata insha Allah”. Sannan babu laifi mutum ya yi wata addu’a ta shi ta neman wasu buƙatunsa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Halayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Nafilolin Azumi danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Falalar Yin Umara A Watan Ramadan

    Falalar Yin Umara A Watan Ramadan

    An karɓo daga Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu anhu) ya ce; “Yin umara a watan Ramadan dai-dai da ladan aikin hajji ne; ko kuma dai-dai da ladan aikin hajji tare da ni yake”. (Bukhari 1764, Muslim !69).

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Shan Ruwan ZamZam danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Sallar Roƙon Ruwa danna nan.

    Wannan bayani anciro shine daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Kaffarar Azumin Ramadan

    Kaffarar Azumin Ramadan

    Game da kaffara kuwa; ya gabata cikin hadisin Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu); inda wani mutum ya sadu da iyalinsa da tsakar rana a watan azumin Ramadan; kuma aka ce akwai ramuwar kaffara a kan sa, wato ‘yanta wuyaye, idan bai samu dama ba; to azumin watanni biyu a jere; idan kuma ba zai iya ba; to ya ciyar da miskinai sittin.

    An ce, kaffarar jima’i a kan zaɓi ake yi ba a tartibi (jere) ba; sai dai waɗanda suka rawaito tartibin sun fi yawa. Saboda haka ruwayarsu ta fi rinjaye saboda sun fi yawa, kuma suna da ƙarin masaniya (ilimi) sama da ragowar; inda suka yi ittifaƙi kan cewa azumin wanda ya yi jima’i ya warware; wanda hakan ba ta samu ba cikin ragowar ruwayar, kuma wanda ya sani hujja ne a kan wanda bai sani ba; kuma daga cikin abin da ke rinjayar da tartwikiibin cewa ya fi taka tsantsan kuma riƙo da shi ya isar; idan mun ce zaɓi ne ko ba zaƙi ba, saɓanin idan muka riƙi ragowar hadisan.

    Haka kuma wanda kaffara ta hau kansa, kuma ya kasa ‘yanta wuyaye ko yin azumi ko ciyarwa; to za ta sauƙa daga kansa, saboda ba a kallafa abu sai har idan za a iya. Allah Maɗaukakin Sarki ya ce:

    “Allah ba ya kallafawa rai abu face wanda za ta iya”. (Baqara: 286).

    Kuma ga dalilin aikin Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasalam); wato inda Ya ɗauke kaffara kan mutumin nan yayin da ya gaya masa wahalar da yake ciki, har ma ya ba shi dabino akan ya je ya ciyar da iyalansa.

    Sannan kaffara ba ta hawa kan macen da mijinta ya neme ta; saboda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) an ba shi labarin abin da ya faru tsakanin wannan mutumi da matarsa, amma bai wajabta mata kaffara ba, sai guda ɗaya (wato ramuwar azumin). Allahu a’alam.

    Domin karanta cikakken bayani akan Ramuwar Azumin Ramadan danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Raya Daren Lailatul ƙadari danna nan.

    Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Don karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yadda Al’ada (Jinin Haila) Yake

    Yadda Al’ada (Jinin Haila) Yake

    A wannan shafin za mu tattauna akan abubuwan da suka shafi al’adar ‘ya mace. Yadda zaki san in al’adarki daidai take ko kuma kina da matsala. Abubuwan da za kiyi amfani dasu idan kina al’ada kamar: Auduga (Pad) da tsumma da sauransu. Yadda zaki tsaftace jikinki da suturar ki idan kina al’ada.

    Mecece Al’ada?

    Ita al’ada jini ne ko kuma gudan jinni wanda yake fitowa daga mahaifa a jikin mace. Al’ada na zuwar wa mace duk wata. Aduk sanda kika ga irin wannan jinin to shi ake nufi da al’ada.

    Me Ake Nufi Da Lokacin Al’ada (Jinin Haila)

    Lokacin Al’ada lokaci ne da yake shiryawa jikin mace ɗaukar ciki duk wata. Lokacin al’ada na amfani da abubuwa guda biyu irin su estrogen da progesterone.

    Bayaninsu ya tafi kamar haka: A jikin mace akwai ƙwayaye guda biyu, kuma kowanne yana riƙe da ƙwayaye ba adadi a cikinsa, kwayayen ƙananu ne, wanda idanu baza su iya ganin sa ba, sai da taimakon na’urar gani. Lokacin al’ada, ƙwayayen suna girma, wanda hakan shi yake nufin cewa maniyi yake jira su haɗu, su haifar da ɗa.

    Bayan mace ta gama al’adar ta, akwai wani mataki da zata shiga, wanda ake kira da “Ovulation”. Da yawan mata basa sanin lokacin da sukeyin ovulating, saboda ba abu bane da mutum zai tayar da hankalin sa. Alamomin ovulation su ne; ciwo a ƙasan mara, wanda zaki ji a ɓari ɗaya ko duka biyun. A turance; bloating, spotting da sauransu.

    Lokutan Da Al’ada Take Farawa Da Kuma Tsayawa

    A wani lokacin girman ‘ya mace, wasu matan suna fara al’ada a shekara sha biyu zuwa sha huɗu. Amma wasu suna ganin nasu da wuri, tunda yanayin jiki ba ɗaya bane; kuma babu tabbacin ga lokacin da zaki ga al’adar. Amma idan baki ga al’adar kiba, har kika kai shekara goma sha shida (16), to ki tuntuɓi likita.

    Yawancin mutane suna daina ganin al’adarsu idan sun kai kimanin shekaru arba’in da biyar (45) ko hamsin da biyar (55), wanda aka fi sani da menopause (lokacin da mace zata daina al’ada). Al’adar mace tana farawa da tsayawa, kamar yadda ragowar mutane suke yi. Amma taƙaitaccen lokacin dainawa shi ne daga shekara arba’in da biyar zuwa hamsin da biyar.

    Abubuwan Da Mace Zata Iya Amfani Dasu Idan Tana Al’ada

    Mace idan tana Al’ada zata iya amfani da su audugar mata da tissue da tsumma da sauransu. Su waɗannan da aka lissafo, suna da inganci a rayuwar mace. Su suke taimakawa wajen tsafta da kuma hana jinin ya ɓata jikin ki.

    1. Audugar mata (Pad): Auduga ce mai fiffike guda biyu, wadda zaki yi amfani da ita wajen hana jinin ya ɓata jikinki. Ita ce mafi ingancin auduga da zaki iya amfani da ita, suna nan kala-kala kamar su: Lady Care da Virony da Always da Molped da 7-layer da sauransu.

    2. Tissue: Zaki iya amfani da wannan idan al’ada ta same ki a waje, ko kuma bakya ɗiga da yawa, amma ba ta ɗaya daga cikin audugar mata da take da kyan amfani. Ita amfanin ta yafi zuwa idan audugar ki ta ƙare, to sai ki yi amfani da shi.

    3. Tsumma: Shi ma amfanin su ɗaya da audugar mata, amma shi wannan zaki wanke shi ne duk sanda kika cire shi.

    Hanyoyin Da Zaki Bi Wajen Tsaftace Jikinki Idan Kina Al’ada

    Idan kina amfani da pad ne, to duk bayan awa shida (6) zuwa takwas (8) ki tabbata kin cire, kin saka wani, idan kuma kina zuba da yawa, to ki dunga cirewa da zarar kin ji ta jiƙe.

    Masu amfani da tsumma kuma, su dunga wankewa, basai sun jira ya jiƙe ba, don da zarar kin jira ya jiƙe, zai iya ɓata ki, kuma abinda ake gudu kenan.

    Tissue kuma bashi da tsayayyen lokaci, tunda shi kamar na agaji ne, zaki iya cire shi duk sanda kika so, ko kike buƙata, amma ki tabbatar bai jiƙe sosai ba.

    Zaki iya amfani da miski ko turare wanda zaki shafa a jikinki, don kashe ƙarni.

    Wanke hannu a duk lokacin da zaki canza, ko bayan kin canza na da matuƙar muhimmanci.

    Yadda Zaki Tsaftace Jikin ki Bayan Kin Gama Al’ada

    Wanke hannu da sabulu mai ƙamshi ko kuma wanka da su turaren wanka.

    Yin wankan tsarki

    Ki sa miski a auduga sai kisa a pant ɗinki da sauransu.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Yin Wankan Tsarki Bayan Angama Al’ada danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Ciwon Mara Lokacin Al’ada danna nan.

    Don shiga WhatsApp Group ɗinmu na Tsaftar Mata, ku danna nan.

  • Wa ya Kamata In Bayyana Wa Sirrina Idan Na Fara Al’ada

    Wa ya Kamata In Bayyana Wa Sirrina Idan Na Fara Al’ada

    Da yawa mata idan sun fara al’ada, kunya suke ji su bayyana, wasu da dama ba sa iya faɗa wa iyayensu ko kuma wasu manya ko kuma makusanta.

    A wannan shafin namu, zamu bayyana yadda zaki cire kunya, ki faɗa wa iyayen ki; ko wasu manya da zasu baki shawara dangane da yadda zaki fuskanci matsalar.

    Ga kaɗan daga cikin irin tambayoyi da amsoshin su:

    1. Wa zan tunkara dangane da canjin da na fara fuskanta a jiki na?

    Yanayin da kike fuskanta dangane da canjin jikin ki ba abu bane mawuyaci. Idan kina da tambayoyi akan canjin jikin ki, ko yanayin al’adarki; yana da matuƙar muhimmanci ki fito ki bayyana wa mahaifiyyar ki ko yayyan ki ko malamai; kokuma wasu manya da kika sani, don su ɗora ki akan hanyar da ta fi dacewa da ke.

    Duk wacce kika gani ta wuce shekarun ki, to tabbas ta ɗanɗana irin abinda kike fuskanta a yanzu; kuma koda ace basu sani ba, zasu ɗora ki akan tafarkin da zaki fahimta, ko kuma suhaɗa ki da waɗanda suka sani.

    2. Ya zan yi idan na kasa tunkarar iyaye na?

    Jin kunya wajen tattauna maganar da ta danganci al’ada ga iyaye, ba abu bane maiwuya. Yawancin mutane sun fuskanci irin haka, kuma suna son ki; kuma suna son su taimake ki. Su kansu iyaye; zasu ji daɗi idan kika fuskance su da irin wannan maganar. A lokacin zasu ƙara baki kulawar da kike buƙata, su ƙara nusar dake me rayuwar ta ƙunsa.

    Wasu lokutan yana da muhimmanci ki tanadi tambayoyin da zaki yi musu, don ki samu amsoshin su a lokaci ɗaya.

    Gakaɗan daga cikin yadda zaki iya fara tattaunawar:

    • Zaki iya yin alama da ido, ko kuma zirga-zirga a gaban su, don su fuskanci kina da magana; daga nan su da kansu zasu tambaya, su ce, “LAFIYA”; a nan zaki matsa kusa dasu, sai ki fayyace musu abin da ke birnin zuciyarki baki ɗaya.
    • Idan kin san sun riga da sun sani; zaki iya zuwa gurin su, kice kina jin ba daɗi ne, shi ne kike son ki tattauna matsalar dasu ko akwai mafita.
    • Kiyi tunanin tambayoyin da kike son yi, ki rubata su a takarda, ki tabbata babu wasu-wasi a zuciyarki; sai ki basu takardar, su zasu neme ki.
    • Idan kuma baza ki iya yi wa iyaye magana ba, zaki iya samun yayar ki, ko kaka ko malaman islamiyya ko manya a jihar, ko kuma ki ziyarci asibiti.

    3. Ta yaya zan san lokacin da ya kamata na ziyarci asibiti?

    Lokuta da dama, yana da wuya a tattance in kina da lafiya ko akasin haka; ta yaya zaki san ya kamata ki tattauna da likita?

    Muhimmiyar hanya ita ce, ki fara tattaunawa da iyaye ko kuma yayyan ki ko manya da kika yarda dasu. Sun ɗanɗana dayawa daga cikin abubuwan da kike fuskanta yanzu, don haka, zasu baki shawarar da takamata.

    Idan baki da likita, zaki iya zuwa ɗaya daga cikin asibitocin da ke kusa da ke (ƙwararru), kuma karki manta asibiti basa son tambayoyi marasa ma’ana, don aikinsu shine; su taimaka wa al’umma.

    Babu wanda ya kai likita riƙe sirri, don haka, kar ki ji kunyar faɗa musu abubuwan da ke damunki, don su zasu taimaka miki sosai.

    Bin ƙa’idojina da matuƙar muhimmanci, don su za su taimaka wajen ƙara koyar da ke abubuwan da ya shafi jikinki.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Wankan Tsarki Bayan An Gama Al’ada (2) danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Jinin Haila (Jinin Al’ada) danna nan.

    Don shiga WhatsApp Group ɗinmu na Tsaftar Mata, ku danna nan.

  • Abubuwan Da Suke Hana Karɓar Gaskiya

    Abubuwan Da Suke Hana Karɓar Gaskiya

    Haƙiƙa Allah ta’ala ba ya barin bayinsa cikin ɓata face sai ya kawo wanda zai bayyana musu gaskiya. Masu rabo sai su bi gaskiyar, wasu nan take, wasu kuma sai an turza.

    Amma marar rabo sai su kafe a kan ƙarya duk duhunta, su ƙi karɓar gaskiya komai haskenta.

    Irin waɗannan mutane suna fama da waɗansu cututtuka waɗanda su ne suke hana su karɓar gaskiya, bayan ta bayyana a gare su, waɗannan cututtuka suna da yawa, muhimmai a cikinsu su ne:

    Jahilci Mugun Ciwo

    Shiga cikin ruɗun da ƙarya za ta cakuɗa da gaskiya.

    Maƙaryaci ya ɗauki kansa a matsayin mai gaskiya.

    Sakaci wajen neman gaskiya.

    Tsoron wanin Allah in an bi gaskiya.

    Son girma da ɗaukaka.

    Makauniyar biyayya ga jagorori ko iyaye ko malamai.

    Jiji da kai.

    Girman kai rawanin tsiya.

    Hassada ga wanda gaskiyar ta bayyana a hannunsa.

    Bin ra’ayin ƙungiya ko jam’iyya ko mazhaba.

    Aikata zunubai suna sa tsatsa a zuciya ta hana gaskiya shiga.

    Rashin roƙon Allah shiriya.

    Sakacin malamai wajen bayyana gaskiya, har mutane su saba da ƙarya, su yarda da ita.

    Sabo da tasowa a kan abin da ba na gaskiya ba.

    Yiwa addinin Allah ɗauki ɗaiɗai.

    Rarar magana da ci da sha da kallo da sauran su.

    Ganin yadda masu gaskiya suke shan wahala a duniya.

    Idan aka maƙala ɗan wani abu ƙanƙani na gaskiya a jikin ƙarya sai rabuwa da ƙaryar ya yi wahala.

    Cuɗanya da marasa gaskiya.

    Rashin sauraron ra’ayin waɗanda suka saɓawa mutum da auna nasu da nasa da ma’auni na gaskiya.

    Yawaitar marasa gaskiya da rinjayensu.

    Ɗabi’ar ran ɗan Adam, ta kan ji ɗacin gaskiya.

    Fara yarda da abu, kafin a tabbatar da hujjarsa, kamata ya yi sai ka ga hujja ƙaƙƙarfa bayyananniya sannan ka yi imani da abu.

    Rashin sanin halaye da maganganun marasa gaskiya.

    Rashin fahimtar haƙiƙanin ƙarya.

    Bin gurɓatattun aƙidu, da hanyoyin ɓata.

    Idan malami mai faɗa a ji ya kasance a kan ɓata, zai yi wuya a bi gaskiya, sai fa in shi ne ya yi mara koma baya.

    Goyan bayan manya ga marasa gaskiya.

    Nauyin baki da kasalar masu gaskiya wajen yaɗa gaskiyar.

    Rashin bin hanyoyin hikima wajen faɗar gaskiya.

    Neman gàskiya a wurin marasa gaskiya, kamar wurin wani ɓatacce ɗan bidi’a.

    Rashin Neman shawara ta gaskiya.

    Makirce-makircen marasa gaskiya wajen yaɗa ɓarnarsu da farautar mutane.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ingantattun Hadisai Kan Falalar Ranar Ashura Da Azumin Ranar danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Tasu’a Da Ashura danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana A Kan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.