Tag: yadda ake

  • Narkewar Tsibbu Cikin Bokanci

    Narkewar Tsibbu Cikin Bokanci

    Wannan shi ake kira “gamin gambiza”, ma’anar wannan ita ce wata dabara ta yin gamin gambizar magungunan gargajiya na Bahaushe da ba Musulunci ne ya zo da su ba, da kuma nassoshi ko ayoyin Alƙur’ani. Misali a nan shi ne:

    – Haɗa hayaƙin biya-rana da ƙasar ƙafar yarinya ko wata mace da ake so, Wanda da ma can Maguzawa ke yi kafin Musulunci, sannan a haɗa da waccan aya ta Alƙur’ani don mallakar zuciyarta.

    A daidai wannan lokaci kuma, sai aka samu wasu baƙin littattafai suka fara shigowa daga Maroko da Masar da Tunis da Libya waɗanda ke karanbanin leƙe-leƙen abin da Ubangiji Maɗaukaki da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ba su ce a leƙa ba (gaibu). Waɗannan ilmai sun haɗa da:

    – Ilmin Aufaƙu da siddabaru da Hisabi da
    – Tanjimi da falaƙi da mutantani da Rafani

    A waɗansu lokuta za ka ga ƙwararru a wannan fage na tsibbu, ba masana ne na Alƙur’ani ba. Kodayake su kansu ma makarantan suna alfahari a ce sun shahara a cikinsa.

    Ƙarni na ashirin wani ƙarni ne mai ƙunshe da sauye-sauye masu yawa da suka shafi rayuwa da cigaba. Wannan ya ƙara buɗe ƙofofin cin kasuwar tsibbu.

    Daga cikin asiran da suka shahara a wannan lokaci akwai:

    – Siddabaru
    – Hisabi
    – Ramli
    – Ilmin taurari da falaƙi

    Siddabaru ko rufa ido dai ya ƙunshi wasu ‘yan dabaru, waɗanda na bayan fage bai san da su ba sai an bayyana masa. Amma da an bayyana su, ya gan su, ya san dabaru ne kawai. Watau daga kalmar dabara ko dabaru. Daga cikin abubuwan da ke wakana a wannan ɓangaren na siddabaru akwai:

    1. Saka ƙwai cikin kwalba
    2. Saka allura a hanci
    3. Dabon kuɗi
    4. Haɗiye tsaba a baki ta fito ta ido
    5. Yanka wuƙa a jiki
    6. Dafa nama a saman itaciya
    7. Harbin kasko a ga jini

    Domin ƙarin bayani kan waɗannan sai a duba (Bunza, 1970 da 1995).

    A ɓangaren sihiri kuwa, abubuwa biyu ke gudana. Da farko akwai kimiyya, na biyu kuwa shi ne ƙarfin iskoki ta fuskar tsafi tantagaryar sa. Hanyoyin aiwatar da sihiri cikin tsibbu gamin gambiza ne, ko mu ce hatsin bara ne. Ma’ana akan haɗa da ayyukan Musulunci ko Alƙur’ani, a hautsina da na Maguzawa. ldan kimiyya ce, da yawa daga ciki asiran tsirrai ne da itace.

    Shi kuwa ɓangaren hisabi ko (ramli) da tanjim (ilmin Taurari) bincike ne na abubuwan da suka faku wadanda suka gabata da waɗanda ake ciki da waɗanda za a fuskanta. Don samun haske game da alaƙar aljannu ko shaiɗanu da fagen tsibbu da kashe-kashensa da siffofin matsafa, sai ka ci gaba da karatu har ƙarshen wannan Babi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Neman Laƙani Da Asiri Ya Shiga Tsangayu danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Zirga-Zirga Tsakanin Bokaye Da Masu Duba Don Neman Duniya danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikaken Littafin danna nan.

  • Yadda Neman Laƙani Da Asiri Ya Shiga Tsangayu

    Yadda Neman Laƙani Da Asiri Ya Shiga Tsangayu

    Kamar yadda ya gabata, makarantu a tsarin tsangaya sun shahara da neman laƙani ko wani sirri na Alƙur’ani don samun biyan buƙatun rayuwa.

    Da yawa akan samu makarancin da ke ɗalibta wajen wani Alaramma, ba don ya koyi wani abu ba; sai don kawai wannan alaramman ya sanar da shi wani laƙani. Irin wannan shuhura a fagen sanin laƙanoni shi ne a mafi yawan lokaci yake fito da malami ko kuma ya samu wani kwarjini na musamman a wurin al’umma. Da zarar malami ya zama gwani a wannan ɓangare na laƙani; to fa jama’a za su yi ta taruwa zuwa gare shi.

    To wannan yanayi cikin rayuwar makaranta, shi ya ƙara buɗe ƙofar kasuwar tsibbu a tsarin tsangaya. Don haka ma ake samun makarantar da ke sare sanda a fagen laƙani; har ake kiran su Malam Gobe-da-nisa ko Malam mai gani har hanji da sauransu. Asalin laƙani a wurin makaranta an fi yin sa ne don fahamin karatu da kuma maganin wasu cututtuka kamar yadda ya gabata.

    Alƙur’ani dai magani ne na dukkan cuta, sawa’un cutar zuciya ko cutar jiki; Kuma amfani da ayoyin Alƙur’ani don magani sanannen al’amari ne tun zamanin Sahabbai (Radiyallahu Anhuma).

    Mas’alar rubuta Alƙur’ani a sha kuwa sananniya ce a wurin malamai; kuma abu ne mai asali matuƙar ba a jirkita Alƙur’anin ba. Amfani da Alƙur’ani a matsayin maganin cututtukan jiki da samun biyan buƙata a Arewacin Najeriya yana da faɗi. Mutane kan nufi makaranta a tsangaya don neman dafa’i ko jalabi, neman kasuwa, maganin ciwon jiki; fahamin karatu, haihuwa, da raba aure, sammu farin jini, jifan wani da sauransu.

    Irin waɗannan laƙanoni sun haɗa da Baru uwa-uba da Burdin Yasin da Ummi Musa da Darni; da kurat mai fika-fikai da Gursan da Tabbat Yada mai ƙwai, da kinzan waji da gwamalan da Zailun da sauran su.

    A ɓangare guda kuwa, makaranta a tsarin tsangaya; musamman a Maiduguri sun shahara da ɗaukar mummunan mataki; ko ramuwar gayya kan duk wanda suka samu taƙaddama ko rashin fahimtar juna da shi. Masu irin waɗannan asirai kan sabbaba tawaya ko cutuwa ko ma mutuwar abokin hamayyarsu. Makaranta kan jefi junansu wadda zai iya kawo zubewar tilawar ɗan uwansu ko samun tasgaro a rayuwarsa. A arewacin Najeriya a kan ce an yi wa wane Yasin ma’ana an yi masa asiri. Anya kuwa surar ta Yasin ake karantawa babu wani kauce hanya?

    Tsokaci

    Yana da kyau mu ba wa mai karatu haske game da yadda laƙani yake, kuma yaya ake yin sa? Mene ne bambanci tsakanin amfani da Alƙur’ani ta fuska halattacciya da kuma wadda ta haramta?.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Haramtaccen Laƙani Ko Asiri danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Matsayin Tsibbu Da ‘Yan Tsibbu A Wurin Shehu Usman Bn Fodiyo

    Matsayin Tsibbu Da ‘Yan Tsibbu A Wurin Shehu Usman Bn Fodiyo

    Jagoran jaddada Musulunci a ƙasar Hausa, Shehu Usman Ɗanfodiyo a cikin rubuce-rubucensa da yawa, ya yi gargaɗi; ya tsoratar, ya kuma yanke hukunci ga ayyukan tsibbu na duba da hisabi da sihiri da siddabaru da layu.

    Don ƙarin haske, za a iya duba littafan Shehu irin su Nurul-albab da Wasiƙatul Ikhwani da Sirajul Ikhwani; da Bayanil Bidi’i da Tabsiratul Mubtadi da kuma Tamyizil Ahlis Sunnu. A inda ya tabbatar da fitar su daga tafarkin tsira, zuwa ga tafarkin ɓata, tare da wajabcin yaƙar su.

    Koda yake a ɓangare guda, akwai gunaguni da wasu ke yi game da rabuce-rubucen da wasu mataimakan Shehu suka yi, wanda ke marawa tsibbu baya.

    Rubuce-rubucen sun haɗa da: Ƙirar Ahibba’i da Muhawwanatil Ikhwani ila Mubashshiratil Miswani da Kitabul Hisabi wal Asrari; da kuma Ma’awanatil Ahibba’i Fil Ilmil Adibb’i waɗanda Muhammad Bello da Muhammad Tukur; da Abdullahi da kuma Muhammad Buhari suka rubuta.

    Amsa a nan ita ce, koda an danganta musu irin waɗannan ra’ayoyi, to lallai za a ga suna nuna irin maganin da ya halatta a yi da tsantsar Alƙur’ani da Hadisan Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ne. Kamar kuma yadda za a iya gani cikin babukan littafan Bukhari da Muslim da sauran Sittu sihah.

    Ma’ana waɗanda ba a jirkita ayoyin Alƙur’ani ba, kuma ba a amsa umarnin aljanu da shaiɗanu ba. Don ƙarin gamsuwa sai a nemi waɗancan littafai don a nazarce su.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ƙalubale Ga Makarantun Tsangaya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Wasu Birane Da Garuruwa Da Makarantu Da KumaTsangayu A Arewacin Najeriya danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Nau’o’in Sihiri

    Nau’o’in Sihiri

    Da yawa akan ruɗi gardawa da jama’a da yi musu magani da Alƙur’ani; kai ko ma a yi wani aikin sharri, a ce da Alƙur’ani ake yi.

    Wannan sam ba haka ba ne, domin kuwa Alƙur’ani tsantsar alheri ne, babu sharri a cikinsa.

    Sihiri yakan ɗauki waɗannan siffofi:

    1- Raba ma’aurata
    2- Haɗa soyayya ko gaba
    3- Sammu
    4- Rufa-ido
    5- Haukata mutum
    6- Sakar wa mutum wani sharri, da sauran su

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tsibbu Ta Hanyar Duba Ko Ilmin Taurari danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Siffofin Da Suka Bambanta Mutum Da Dabba danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Alamomin Gane Malami Mai Sihiri Ko Matsafi

    Alamomin Gane Malami Mai Sihiri Ko Matsafi

    Ana iya gane ɗan tsibbu, matsafi mai sihiri ta hanyoyi kamar haka:

    1- Yakan tambayi sunan mutum ko na iyayensa.

    2- Yakan nemi wani abu da ya shafi mutum, kamar hankici ko hula ko tufafi ko farce ko gashi da sauran su.

    3- Yakan nemi wata dabba mai wata siffa ta musamman.

    4- Yakan sa a rabuta harufa ko alƙaluma marasa ma’ana.

    5- Yakan karanta wasu sunaye masu rikitarwa.

    6- Yakan yi bunne a ƙasa.

    7- Yakan ƙona wani abu da dai sauransu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nau’o’in Sihiri danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Da Ake Yi Ga Mamaci A Cikin Sallar Jana’iza danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Laƙani Ta Hanyar Wuridi

    Laƙani Ta Hanyar Wuridi

    Da yawan ‘yan tsibbu kan yi wani adadi mai yawa na wuridi. Wanda a mafi yawan lokuta sunayen aljannu ake kira.

    Kuma koda an kira sunan Ubangiji Maɗaukaki, to kuwa za a sirka shi da waɗansu kalmomi ko haruffa da ba kasafai ake sanin ma’anarsu ba.

    Za ka iya gane wannan nau’i na wuridi, ya yin da aka ce sai an nemo turare kaza, ko sai an samo garwashin wuta a cikin ɗaki mai duhu. Shi ma wannan yana da tasiri a fagen laƙunƙuna haramtattu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Alamomin Gane Malami Mai Sihiri Ko Matsafi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Nema Wa Yara Samun Karatu Da Raba Su Da Abokanan Banza danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tsibbu Ta Hanyar Duba Ko Ilmin Taurari

    Tsibbu Ta Hanyar Duba Ko Ilmin Taurari

    Shi ma wannnan ba ya buƙatar wani dogon jawabi, domin kuwa duk Musulmin ƙwarai, ya san ba wanda ya san gaibu sai Ubangiji Maɗaukaki.

    Da’awar sanin gaibu kuwa, alama ce ta cuɗe-ni-in-cuɗe-ka da aljannu. Ko leƙen abin da Ubangiji Maɗaukaki ke tsoratarwa a kansa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Matsayin Tsibbu Da ‘Yan Tsibbu A Wurin Shehu Usman Bn Fodiyo danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Dabarun Zaman Lafiya Da Mutane danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Aiki Kamar Yankan Wuƙa

    Aiki Kamar Yankan Wuƙa

    Irin wannan na faruwa ne a lokacin da matakan haɗa asiri; ko laƙani suka nemi a aikata wasu miyagun ayyukan saɓo.

    Kamar a ce sai ya taka Alƙur’ani ya shiga banɗaki da shi, ko ya rubuta ayoyin Alƙur’ani da wata ƙazanta; kamar rubuta shi da jinin haila ko rubuta Suratul Fatiha da baya da baya. Ko a ce ya yi Sallah babu alwala, ko a ce ya yi zina da ‘yarsa ko uwarsa ko mahaukaciya.

    Ko kuma ma, a rubuta wasu haruffa da zantuka da bai san ma’anar su ba; ko kuma ya nemo tufafi ko wani gashi ko farce ko wani abu daga mutumin da ake son yi wa asirin. To kai tsaye za mu gane sihiri ne, ma’ana tsafi ne.

    A irin wannan yanayi ne waɗansu malamai da rigima ta haɗa su a kan limanci; suka riƙa jifan junansu, da haka har suka halaka ‘ya’yansu da matayensu, daga ƙarshe ɗayan ya halaka gudan.

    Tambaya a nan ita ce, me yasa malaman da suke irin waɗannan laƙunƙuna ba sa iya yin tasiri kan manyan kafiran duniya da azzuluman Yahudawa?

    Amsa ita ce, saboda shaiɗan ba ya ruguza aikin sharri, sai dai ya ƙara masa ƙarfi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Laƙani Ta Hanyar Wuridi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Salati Ga Manzon Allah (S.A.W) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Shin Mene Ne Tsafi Ko Sihiri?

    Shin Mene Ne Tsafi Ko Sihiri?

    Sihiri shi ne ƙulla yarjejeniya tsakanin matsafi da aljani, bisa sharaɗin matsafin zai aikata wasu ayyukan saɓo. Sannan aljanin ya taimaka masa ta hanyar yi masa biyayya cikin umarninsa.

    A duk lokacin da aikin saɓo ya fi muni da nesata daga Ubangiji Maɗaukaki, to kuwa aikin da aka sa aljanin ya fi saurin ci. Daga nan ne ake kiran irin waɗannan ‘yan tsibbu Malam Gobe-da-nisa.

    Amma idan matsafi ya taƙaita amsa umarnin shaiɗanin ko aljanin, to ba zai yi masa biyayya ba.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Aiki Kamar Yankan Wuƙa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan SHUGABANCI A WURIN HAUSAWA danna nan.

    Wan nan baya nin anciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya, Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr.Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Hausar Gardawa

    Hausar Gardawa

    Kasancewar tsarin tsangaya wani fage ne mai faɗi, kuma wata wayewa ce ga ma’abotanta mai zaman kanta; tsarin ya haifar da samuwar wasu lafuza ko ƙarin yare wanda ya keɓanci waɗanda ke cikin wannan da’ira ta gardawa.

    Kamar dai yadda sojoji ko wani rukuni na mutane ke da yaren da ya keɓance su, kuma ba mai gane shi, sai su ya su.

    Akwai Hausar gardawa mai alaƙa da Alƙur’ani, wata Hausar tasu na da alaƙa da shi kansa harshen Hausa, wata kuma mai Alaƙa da harshen Turanci ko kuma Larabci.

    Misalin mai Alaƙa da Alƙur’ani:-

    – Tilka: baƙar mace
    – tusuna: mummunar mace
    – Udda: gajeren mutum
    – Ƙala ƙato: malamin littafi
    – Na gaban innaka: maye
    – Wa hananan: an hana

    A wani lokaci kuwa, su kan ƙirƙiri wata sabuwar ma’ana a cikin shi kansa harshen na Hausa; misali:

    – Tashe:- tashi cikin dare don yin karatu maimakon tashe da ake yi da watan Azumi.
    – Sauka:- kammala karatun Alƙur’ani
    – Kasgi:- Jahili
    – Badawai:- ƙauye
    – Yankan baki:- raba kalma
    – Yanka Alamina:- yin ɓarna ko yin zina
    – Rani:- fita Neman karatu lokacin bazara
    – Banda:- kayan tafiya almajiri
    – Warat:- kiran gaggawa don cin abinci
    – Wanke:- baƙin ruwan da ake tawada da shi
    – Kwami:- karatu ko nacin karatu
    – Ɗan bajire:- guntun tuwo
    – Zaman sidi:- jiran abinci a wajen bara
    – Mako:- yin itacen sati
    – Gabza:- abincin maras daɗi
    – Malam Shehu:- talaka
    -Tsoma:- aljani a cikin gardawa
    – Kara:- kuskure ko tsallake
    – Buƙa:- gabatar da buƙata
    – Datsi:- rabo ko gutsiren abinci
    – Kantuga:- wasa ƙwaƙwalwa
    – Alif na gaban wau:- mutum marar ra’ayi
    – Shim mai ruwa Uku:- shashasha ko mara hankali
    – Miya ba gishiri:- makarantar islamiyya
    – Kaukau:- marowaci
    – Bakaddike/Kadikko:- almajirin da ya daɗe a gari
    – Kura:- matar gardi
    – Jargi:- busasshen nama
    – Bugu:- dafa tuwo
    – Gaga:- rashin ji
    – Bajancuri:- ba zato sai ya yi tilawa mai yawa
    – Curinbaje:- ana sa rai kuma sai ya kasa tilawa mai kyau

    Gardawa a tsarin tsangaya, ba su taƙaitu wajen ƙirƙiro sababbin ma’anoni cikin Alƙur’ani da harshen Hausa ba, har sai da suka kutsa cikin harshen Turanci. Misali:

    – Boko:- ilmin boko ko ilmin gangan
    – Ladan boko:- ƙaramar mota
    – Coca-Cola :- ko ka kula giya ce?
    -Chiyaman ko Shugaban cin amanar
    Ƙaramar Hukuma:-

    Tsokaci

    Canza salon kalmomin Alƙur’ani ya zuwa wata ma’ana, abu ne da bai halarta ba. Domin zancen Ubangiji Maɗaukaki ne da ɓace, ko wasa baya zuwa bayansa ko gaba gare shi. Don haka ya zama wajibi ‘yan uwa gardawa su kiyaye, domin hakan zai iya kai mutum ga yin ridda.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Asalin Tsibbu A Tsangayun Alƙur’ani danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Zubin Tsangaya Yake danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.