Tag: yadda ake

  • Manhajar Tsangayar Gwaji

    Manhajar Tsangayar Gwaji

    Ya kamata manhajar wannan tsangaya ta gwamnati ta fuskanci cimma manufofin ingantaccen imani, da samun rayuwa ta dogaro da kai, da wayewar zamani.

    Wannan manhaja za ta yi ƙoƙarin cimma koyarwar Shehu Usmanu Ɗan Fodiya, wadda ke komawa kan ilmi da noma da kiwo. Sauran tsare-tsare za su iya shiga sannu a hankali.

    Wajibi ne manhajar ta cimma:

    1. Samar da ingantacciyar haddar Alƙar’ani ko tilawa mai ƙarfi.
    2. Koyar da almajirai wani abu na ilmin Fiƙhu da Hadisi.
    3. Cusa son Larabci da magana da shi da ilmin lissafi da Hausar boko, don gogayyar rayuwar yau da gobe.
    4. Ƙarfafa tukuri da musaffa da sauransu.

    Albashin Malamai
    1. Hafizi – GL 09
    2. Dattijon Alaramma – GL 12
    3. Gwani – GL 13
    4. Gangaran – GL 15

    Domin karanta cikakken bayani a kan Gudunmawar Mawadata Da Ɗaiɗaikun Jama’a Ga Tsangayu danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Gudunmawar Tsangayun Alƙur’ani Wajen Cigaban Al’umma danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihinsu Da Zamantakewarsu Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Samar Da Tsangayun Gwaji Na Gwamnati

    Samar Da Tsangayun Gwaji Na Gwamnati

    Ya zama wajibi ga dukkan jihar dake son bunƙasa tsangayun Alƙur’ani da inganta rayuwar almajirai, bayan ta ba da dukkan kulawar da ta gabata, ta samar da tsangayar Gwamnati ta Musamman (Model Tsangaya).

    Wadda za ta zama misali ga sauran alarammomi, kuma ta cike giɓin da ke tsakanin tsangayu da sauran takwarorinsu ‘yan zamani ma’ana ‘yan boko.

    Ya kamata yanayin wannan tsagaya ta gwaji, kada ta fita daga irin yanayin Tsagayunmu na gargajiya, musamman tsarin karatu da hura wuta da amfani da alluna da sauran fuskokin karatun tsangaya.

    Abubuwan da gwamnati za ta samar sun haɗa da:

    1. Muhalli mai yalwa da ɗakunan kwanan almajirai, da wurin darasu da Masallaci da kuma banɗakuna.
    2. Gina gidan alaramma da na mataimakansa.
    3. Gina wurin koyan sana’o’i dabam-dabam.
    4. Samar da katafariyar gona kusa da tsangaya da shanun huɗa da amalanke da kaltibeta da kuma ɓangaren kiwon kaji ko dabbobi.
    5. Samar da ɗakin shan magani.
    6. Samar da ofishin babban jami’in gwamnati. (Officer in Charge/Director) daga Ma’aikatar Kula da Al’amuran Makarantun Alƙur’ani.

    Wannan ofishi, shi zai riƙa tattara bayanai da adana su, da kuma bibiyar halin da tsangaya ke ciki. Kuma shi ne mai alhakin bayar da shaidar karatu ga almajirin da ya kammala a hukumance.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Manhajar Tsangayar Gwaji danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Neman Laƙani Da Asiri Ya Shiga Tsangayu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya, Tarihinsu Da Zamantakewarsu Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan

  • Yadda Ake Wankan Tsarki Bayan An Gama Al’ada (2)

    Yadda Ake Wankan Tsarki Bayan An Gama Al’ada (2)

    Shi yin wankan tsarki alama ce da take nuna cewa an gama al’ada, za ki fara sallah; wadda ya wajabta a kan ko wacce mace, idan ta gama ta yi shi.

    Ruwa me tsafta, mara kala, farin ruwa a buta.

    Ɗaukan niyya, za ki fara da cewa (Bismillahi rahmanirrahim, na yi niyyar yin wanka, haila domin tsarkake kaina)

    Sai ki wanke hannunki sau uku

    Za ki wanke abin da ya yi daga cibiya zuwa gwuiwar ƙafa, saboda duk wata ƙazanta a tsakankanin nan take; bayan kin kammala, sai ki sake wanke hannun ki sau uku.

    Za ki yi Bisimillah, sai ki yi yadda ake alwala, amma ba za ki wanke ƙafa ba.

    Bayan kin kammala alwala, sai ki ɗebo ruwa, ki wanke saman kanki zuwa wuya; (wanki ba me sabulu ba, kuma ba shafawa za ki yi ba, wankewa mai kyau sau uku).

    A wannan gaɓar, za ki raba jikinki gida biyu, wato dama da hagu.

    Sai ki fara da wanke ɓarin dama, daga kafaɗa gaba da baya, harda hannaye zuwa ƙafafu.

    Sai kizo ki wanke ɓarin hagu, daga kafaɗa gaba da baya, harda hannaye zuwa ƙafafu.

    Bayan kin kammala, sai ki zo ki wanke ƙafa (Ma’ana kin cika da alwala kenan).

    Ƙarin Haske:

    Alwalar da kika yi da farko, ba ki wanke ƙafa ba, to bayan da kin gama wanka kika zo kika wanke ƙafa daga ƙarshe, za ki iya sallah da alwalar da kika yi, tunda tsaftatacciya ce, amma ba ta cikin ƙa’ida, cewa sai daga baya za a dunga wanke ƙafa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Fara Jinin Haila Da Bayanin Siffofinsa danna nan.

  • Yadda Ake Yin Wankan Tsarki Bayan An Gama Al’ada

    Yadda Ake Yin Wankan Tsarki Bayan An Gama Al’ada

    1. Za ta jiƙa tafikan hannayenta da ruwa, sai ta ɗan bubbuga tafikan hannayenta a kanta; sannan ta wanke daga cibiya zuwa gwuiwar ƙafafunta; sannan sai ta ɗebo ruwa cikin tafikan hannayenta biyu, ta wanke kanta, za ta maimaita hakan ne sau uku.

    Sai ta wanke gaɓoɓin alwala, kowanne sau ɗaya; sannan sai ta wanke saman jikinta, daga kafaɗarta zuwa cibiyarta ɓangaren dama. Sai ta maimaita hakan a ɓangaren hagu; sannan ta wanke ƙasan jikinta, daga gwuiwa zuwa idan sawu ɓangaren dama; sai ta maimaita hakan a ɓangaren hagu; sannan ta wanke ƙafafun ta dama da hagu sannan ta kwara ragowar ruwan a gaba ɗaya jikinta.

    Wannan shi ake kira (Sifatul Kamal) wato kalar wanka mai tsari.

    2. Za ta jiƙa tafikan hannayenta da ruwa, sai ta bubbuga tafikan hannayen nata a kanta, saboda kiyaye lafiyar jikinta; sannan ta buɗe shawa ko ta shiga cikin baho ko daro; ko kuma ta juye ruwan bokitin a jinkita, yadda za ta game ko’ina da ina na jikin nata da ruwa.

    Wannan shi ake kira (Sifatul Ijiza’i) wato kalar wankan da shi ma ya wadartar.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hukunce-hukuncen Jinin Haila Da Na Biƙi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Wankan Tsarki Bayan An Gama Al’ada (2) danna nan.

  • Yadda Za Ka Kare Facebook Ɗinka Daga Hackers

    Yadda Za Ka Kare Facebook Ɗinka Daga Hackers

    Assalam alaikum, barka da wannan lokaci. Duba da irin matsalolin da ake samu a shafukan sada zumunta; musamman shafin Facebook da Instagram, ta yadda wasu ɓata-gari ke amfani da basira wajen ƙwace asusun ɗin mutane domin su damfari bayin Allah.

    Mutane da yawa na kukan an ƙwace musu Facebook account, an chanja musu suna, an cire bayannansu, an ɗora na wasu; kuma ba su san dalilin yin hakan ba.

    Wannan yasa naga ya dace, na yi wa ƴan’uwa bayanin yadda za su kare kansu, don gudun faɗawa komar kifi, ta yadda babu wanda ya isa ya yi maka hacking account ɗinka na Facebook ko Instagram, ba tare da izininka ba, ko da ya san password ɗinka.

    2FA (Two Factor Authentication)

    Akwai abin ake kira Two Factor Authentication; wani Security ne wanda ake kunnawa, akwai shi a cikin mafi yawan shafukan sada zumunta, wanda idan ka kunna shi; ɓarawon account ba zai samu damar yi maka hacking ba, ko da ya san password ɗinka. Abin da 2FA yake nufi shi ne, mukulli na biyu wanda zai tabbatar da kai ne mai wannan shafin, a duk lokacin da ake je yin Login (shiga).

    Duk lokacin da wani ya yi ƙoƙarin shigar da bayanan Account ɗinka, domin ya buɗe; idan ka kunna #2FA za a tura maka saƙo da lambobin sirri a cikin wayarka ko email ɗinka; ya danganta da wanda ka zaɓa, dole sai an shigar da su sannan wannan Account zai buɗe.

    Yadda Ake Kunna 2FA A Facebook

    Da farko za ka shiga cikin #Settings a cikin facebook, sai ka shiga ‘Security and Login’; a ciki za ka ga inda aka rubuta “Two Factor Authentication”; sai ka shiga ciki, za ka ga “Your Security Method” sai ka shiga, zai nuna maka inda za ka shigar da lambar wayarka, wacce za a dinga tura maka saƙo akan ta; sai ka saka Password na Facebook ɗinka, za su nuna maka “Two Factor Authentication is active” shi kenan, komai ya yi daidai.

    Note!!!

    Ya kamata ka shigar da number da ka san kai ne ka yi registration na layin; saboda ba za ka iya Login Facebook ba, sai wannan layin yana cikin wayarka, saboda halin faɗuwar waya, Allah ya kare. Kar ku manta da yi wa ‘yan’uwa sharing saboda kowa ya ƙaru.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Amfani Da Kafar Sadarwa Ta Whatsapp danna nan.

  • Lokaci Da Yanayin Sadarwa A Waƙar Baka

    Lokaci Da Yanayin Sadarwa A Waƙar Baka

    Bisa yawancin lokuta na sadar da waƙoƙin baka na Hausa, kamar yadda aka yi bayani a baya; akan sadar da waƙar baka ne a lokaci na safiya ko na hantsi ko na rana ko na yammaci ko na daddare da dai sauran lokuta.

    Haka kuma Hausawa sukan sadar da waƙoƙin baka a kowane yanayi na damina ko na kaka; ko na rani ko na bazara ko na hunturu ko na ɗari. Alal misali waƙoƙin noma an fi yin su a yanayi na damina, wato lokacin da ruwan sama yake sauka.

    Haka kuma waƙoƙin ɓullowar kaka akan yi su ne da zarar damina ta shige ko tana gab da wucewa; wato an cimma amfanin gona ka’in da na’in, da dai sauransu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Wuraren Sadawar Waƙar Baka danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yabon Gusau A Waƙoƙin Baka danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Aiwatarwa Da Sadarwa A Waƙoƙin Baka Na Hausa. wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Ɗabi’un Makaranta da Halayensu Cikin Zamantakewar Tsangaya

    Ɗabi’un Makaranta da Halayensu Cikin Zamantakewar Tsangaya

    Ɗabi’un makaranta Alƙur’ani da irin halayyarsu ko kuma yanayin tunaninsu game da rayuwa (world-veiw) wani fage ne mai faɗi da muhimmanci wajen sanin haƙiƙanin tsarin zamantakewar tsangaya da irin wayewa ko gogewa da almajirai ke samu don faɗawa gwagwarmayar rayuwa.

    Bugu da ƙari kuma, abu ne mai ƙayatar da mai karatu, tare da ƙara masa son nazari kan tsarin tsangaya. Tunanin makaranta ya ginu ne bisa tushen ganin girman masu ɗauke da Alƙur’ani. Don haka, duk wanda ba shi da karatu, ba sa sha’awarsa. Al’adar Barebari ta nuna isa da rashin nuna gazawa, ta yi tasiri mai yawa ga tunani ko halayyar gardawa.

    Akwai wasu ɗabi’u ko ta’adoji da makaranta a tsangaya suka yi tarayya, cikinsu tun daga kan ƙananan almajirai har zuwa kan gardawa da manyan alarammomi. Irin waɗannan ɗabi’u sun haɗa da zumunci da son juna da biyayya ga na gaba da ƙanƙan-da-kai da barkwanci da sauransu. Wasu ɗabi’un kuwa, an fi danganta su ga gardawa, misali son burgewa da ban dariya da taƙadaranci da son gayu da tsafta da dai makamantansu.

    A wasu lokuta kuwa, za mu ga cewa ɗabi’un wasu makarantan sawa’un gardawa ne ko alarammomi ne sun dogara ne kan irin ɗabi’ar makaranci a karan kansa. ma’ana za a iya samun alaramma dattijo wanda bai bar halayya da ɗabi’un gardanta ba. Ɗabi’u irin su tsafta da son ado kuwa an fi danganta su ga gardawa, koda yake da yawa wasu dattijan cikin manyan alarammomi, za ka same su ba a raba su da tsafta da yawan son ado.

    Mai yiwuwa mai karatu ba zai samu cikakken hoton rayuwa ko yanayin zamantakewar makaranta a tsangaya ba; har sai mun gutsuro wani abu daga hikayoyi da labarai da suka shafi waɗannan bayin Allah. Wasu labaran na nuna jarunta da juriya da zumunci da tattalli; wasu kuma suna nuna hazaƙa da kishin zuci da son burgewa da sauran su, don haka sai mun haɗu a sashe na huɗu cikin wannan ɗan littafi don mu ga waɗansu ‘yan misalai.

    Abu ne mai matuƙar muhimmanci mu san cewa, makaranta musamman gardawa mutane ne masu naci da azama ko himma kan duk abin da suka sa a gaba ta yadda wahala ko wani tsanani na rayuwa ba ya hana su zarcewa, matuƙar dai akwai wannan buƙata tasu, misali da yawa za ka samu gari ana rashin abinci ko rashin wadataccen ruwa, amma sai ka iske ɗaruruwan gardawa maƙil a wannan gari, musamman in sun sami labaran cewa tsangayar na tashen tara makaranta ko akwai wani mashahurin malami, to kuwa su sun samu mashekari.

    Gardawa masu himma, ba su cika son a san su a gari ba, domin hakan zai jawo musu yawaitar abokai, daga bisani kuma, hakan ta riƙa kawowa shagaltuwarsu da karatu cikas, wannan ya sa duk inda gardi ya fara samun irin wannan, to kuwa za ka wayi gari babu shi a wannan tsangaya, wannan ya sa ake yi masu kirari da “Gardi na inna mai ‘yan kaya a kwana da ku, ba a wayi gari da ku ba”.

    Kasancewar galiban gardawa na cikin shekarun samartaka, wannan yasa suke da son a dama da su a duk wani abu da zamani ya kawo, kuma samari ke yayin sa. Misali da yawa za ka samu gardi mai almajirai a ƙarƙashinsa idan zai je kaɗar-raɓa, to sai ya shirya almajiransa, ya tura su zuwa garin da za su sauka, daga baya kuma sai ka gan shi ya bi su cikin wata irin shiga ta ‘yan birni da jaka mai tsada da gogaggen takalmi da gilashi ta yadda wani ba zai raina shi ba.

    Wannan ya sa da yawan su na koyon boko, ba tare da sun je makaranta ba.

    Gardawa sun shahara da neman na kai da iya tsimi da tanadi, don haka ma za ka same su da gwaninta wajen iya ɗinkin hula; yankan farce da makamantan sana’o’in da ba za su hana su karatu ba. Saboda yawan ƙanƙan da kai, kuwa zai yi wuya ka ji an kira makaranci da alaramma face ka ji ya ce, “Almajiri dai”.

    Makaranta a yayin darasu kan nutsu su tara hankalinsu, don su nuna gyaran baƙi, kamme ko camme; kara ko kurne ko kuma gyaran wasali a allon ɗan uwansu. Wannan ya sa duk wanda ya sanya allonsa a gaban alaramma; kuma ya ɗauke ba tare da wani ya sa hannu a allon ba, to wannan ya yi babbar bajinta. Makarancin da ya sanya allo gaban alaramma, tun daga Baƙara har Nasi, ba tare da an ci gyaransa, ko da da ɗugon wani harafi ba; to akan ce wane ya sha fari.

    Gardawa cikin makaranta ba sa ganin kowa da wata baiwa matuƙar ba mahaddaci ba ne.

    Wannan ya sa da yawa suna da wata inkiya, alal misali, idan guda ya yi baƙo; to ragowar za su yi ta hidima da girmama wannan baƙo don tsananin kara. Domin su gano matsayin baƙon kuwa, don kada su ba shi matsayin da ba nasa ba; sai guda ya tattara turɓaya a ƙasa a fakaice, kamar yana wasa da ita. Da zarar gardin da ya sauki baƙon ya ga haka, to zai ɗau haske. Don haka sai ya cigaba da tattara wannan ƙasa yana ƙara mata tsini, ma’ana dai hakan take baƙon makaranci ne. Amma idan ba makaranci ba ne, to shi mai masaukin baƙon zai baje wannan ƙasa a fakaice, har sai ya ƙarar da ita; ma’ana dai Malam Baƙo ba kowa ba ne. Daga nan ne suke cewa wane “curinbaje” ne ko “bajencuri” ne.

    Makaranta a tsangaya sun ginu bisa haɗin kai don gudanar da al’amuran tsangaya.

    Wannan yasa kowanen su suke zuwa jeji don saro itacen hurawa a gargari. Irin wannan hidima ita ake kira mako. A waɗansu lokuta kuwa, za ka ga an tara wannan itace tamkar wata dalar gyaɗa. A lokacin da wutar gargari ke ci ganga-ganga, makaranta kan kewaye ta suna karatu suna gwali; ma’ana suna iza ta suna ƙara itace. Da yawa gardawa kan sallamawa wanda ya fisu naci. Irin waɗannan masu naci, za ka same su ko yaushe suna kwami; ko da kuwa an tashi daga karatu, kowa ya fashe an gaji. To su ba sa sarewa, Gardi mai irin wannan naci shi ake kira Buna..

    Wani abu mai ban sha’awa game da makaratan musamman ma gardawa cikin tsangaya; shi ne irin duk fasahar da suke da ita wajen karatu da sana’o’i; da kuma sarrafa duk wani abu da ke kusa da su don ya zama mai amfani gare su. Mu ɗauki yadda suke yin gado mai hawa biyu ko uku da kara da itatuwa, ko kuma mu dubi irin ƙwarewar da suke da ita wajen ɗinkin hula; ko kuma launukan da suke haɗawa don yin zayyana a allunansu. Ko kuma tsayawar hannunsu wajen rubutu ko fitar da bayala bisa takardar Alƙur’ani.

    A wajen gini kuwa, za mu ga yadda suke haɗa kiskalinsu. Har ma na tattauna da wani alaramma a Ƙaramar Hukumar Tudun Wada cikin Jihar Kano; wanda ya gina wani katafaren gini mai benaye da tagogi masu ado da fasalin gine-ginen ƙasashen Larabawa; ko Rumawa, abin dai gwanin ban sha’awa da mamaki.

    Wannan alaramman ya bayyana min cewa ya yi wannan gini ne da hannunsa; kuma duk aune-aunen da ya yi, da zubin ganin ya yi shi ne daga tunaninsa da ƙirƙirarsa; ba tare da ya kwaikwayo daga wani waje ba, ko kuma wani ya gaya masa ba.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Asalin Yawon Bundi Ko Ƙaura Wurin Makaranta danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Asalin Sunan Kakan Manzon Allah(S.A.W) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Azuzuwa Da Kashe-kashen Makaranta A Tsangaya

    Azuzuwa Da Kashe-kashen Makaranta A Tsangaya

    Za a iya karkasa makaranta tsarin tsangaya gwargwadon matsayin karatu ko shekaru tsakanin sa’o’i daga almajirai.

    Kowane aji na da siffofi da ake gane waɗanda ke ƙarƙashinsa, kamar yadda al’amarin yake a tsarin ilmin zamani tun daga kan ɗan firamare, sakandare da ‘yan manyan makarantu. Amma a tsarin tsangaya an fi la’akari da matsayin karatu fiye da shekaru wajen sanya suna.

    Ƙolo:

    Shi ne mafi ƙanƙanta a tsarin tsangaya ta fuskar karatu da yawan shekaru. Ƙolawa su ne a mafi yawan lokatu ke yin bara da ƙoƙo ko kwano don neman abinci. Shekarun ƙolo sukan fara ne daga shekaru bakwai zuwa shekaru goma sha huɗu. Kodayake dai da yawa akan samu iyayen da ke kai ‘ya’yansu tsangayu a ƙasa da shekaru bakwai. Rayuwar ƙolo na kasancewa cikin yanayi mai ban tausayi, musamman ma idan akwai ƙolawa da yawa a wannan tsangaya. ƙarancin shekaru da rashin cikakken wayo na gwagwarmayar rayuwa, kan ƙarawa rayuwar ƙolo tsanani. Rashin wanka da wanki a kan lokaci da kirci da datti, su ne a mafi yawan lokaci siffar almajiai a wannan aji.

    Kirarin Kolo shi ne:

    Ƙolo ɗan matar malam,
    A taɓa ka a taɓa malam,
    A bar ka, ka lalace
    Da da hali, da an kai ka mandanari mandar,
    Garin su gardi Lahirar ƙolawa.

    Titiɓiri:-

    Shekarun tittibiri kan fara daga shekaru sha huɗu, zuwa shekaru ishirin ko ishirin da huɗu. Titiɓiri shi ne almajiri da ya fara mallakar hankalinsa, domin kuwa a wannan lokaci, ya san ya yi wanka da wanki a kan lokaci. Hausawa kan yi wa titiɓiri take:
    Titiɓiri masomin gardi,
    Kai ba gardi ba,
    Amma ka fi gardi ƙeta,
    A saka gaba ka yi ƙeƙere ka ƙi sauri,
    A bar ka a baya, ka tsikari matar Malam,
    Wannan na nuna cewa titiɓiri na matakin balaga, Ma’ana ya zama murahiki.

    Matashiya

    Makaranta a tsarin tsangaya na da hanyoyin ladabtar da almajiransu ta hanyar yin nasiha, bulala, da dai sauransu. Idan kuwa aka samu gagararren yaro, malamai kan yi amfani da mari don ladabtar da shi. Irin waɗannan hanyoyi na da irin nasu matsalolin, tare da cewa suna taimakawa matuƙa wajen gyara tarbiyyar almajirai.

    Gardi:

    Shi ne makarancin da ya wuce ashirin da biyu kuma karatunsa ya yi nisa. A wasu lokuta a kan samu gardawa ɗaruruwa cikin tsangaya guda. Wannan kan sanya rayuwa makaranta samun cikakken yanayin tsangayar karatu, ta fuskar kishin kai da kuma nishaɗin zamantakewa. Tsangaya kan bunƙasa ne da gardawa, fiye da duk wani aji na makaranta da ya gabata. Makaranta kan ce idan tsangaya ta kai ta kawo cike da gardawa za a iya samun tsoma.

    Tsoma aljani ne da ke rikiɗa cikin siffar gardi ya sauka a wata tsangaya ya ɓace cikin gardawa yana gogayya da kowa a matsayin makaranci ba tare da an gane ba. A duk lokacin da aka gane cewa wannan asali ba mutum ba ne, to shi ke na za a neme shi a rasa a wannan tsangaya. Labarai daga ƙasashen duniya na gaskata cewa akwai yiwuwar samun jinsin aljannu cikin masu neman ilmi a jami’o’i da wuraren taruwar ɗaliban ilmi, kwatankwacin tsoma a yanayin tsangayun Alƙur’ani na ƙasar Hausa.

    Alaramma:

    Shi ne mahaddacin da ke da ingantacciyar hadda. Da yawa wasu na ganin matsayin alaramma matsayi ne na wanda ya haddace Alƙur’ani, har ma ya rubuta shi. Ma’ana dai ya laƙanci duk wasu ilmai da luggogin baƙaƙe da wasulan Alƙur’ani. A wasu lokuta ma yana da ilmin “harji”. Harji wasu dunƙulallun kalmomi ne na harufan hisabi da makaranta ke amfani da su don tantance adadin kalmomi ko baƙaƙen Alƙur’ani. Barebari a wani lokaci kan kira mai irin wannan matsayin na Alaramma da Sayna.

    Gwani:

    Gwani shi ne matakin ƙoli cikin azuzuwan makaranta a tsarin tsangaya. Makaranci kan zama gwani bayan ya kai matakin gardi har zuwa matakin alaramma. Bayan alaramma ya yi shekaru da yin fice a fagen Alƙur’ani, makaranta kan ayyana shi a matsayin gwani a cikin su.
    Ayyana makaranci a matsayin Gwani ya sha bamban da ayyana shi a matsayin alaramma. Makaranci kan zama alaramma ne da zarar ya cimma samun cikakkiyar haddar Alƙur’ani ko kuma rubuta shi da ka. Naɗa Gwani ko ayyana shi kuwa ya keɓanci wasu gungun makaranta keɓantattu a Arewacin Najeriya.

    Irin waɗannan gidaje za a same su a Maiduguri. Wannan ya sanya al’amarin ayyana gwani tamkar bayar da silsila ne ko ijazi a wajen malaman Hadisi; musamman ma a ƙasashen Larabawa. Don haka ne ma zai yi wuya ka ga wani makaranci wanda ba ahlin abin ba, ya yi gaban kansa; ko ya bugi ƙirji ya ayyana almajirinsa ko wani makaranci dabam a matsayin gwani. Wannan ya sanya za a iya samum dubunnan waɗanda suka isa a kira su gwanaye, amma ba a kiran su da shi; saboda rashin samun zartarwar irin waɗancan malamai.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Asalin Samuwar Goni danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Asalin Kiɗan Fiyano danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Asalin Yawon Bundi Ko Ƙaura Wurin Makaranta

    Asalin Yawon Bundi Ko Ƙaura Wurin Makaranta

    Yawon bundi al’ada ce sananniya wajen ma’abota tsangaya. Ana kiran almajirai waɗanda ke tashi daga garuruwansu na haihuwa zuwa wasu sassa da sunan ‘yan yawon bundi, ko kuma almajiran kwargo.

    Makaranta na fita da almajiransu don zuwa wajen mashahuran malamai ko tsangayu don Neman karatu. A wani lokaci ma don neman ƙasar noma, musamman idan wurin da suke babu irin yanayin da zai taimakawa karatunsu. Da ma dai kalmar almajiri ta samo asalin ne daga Almuhajir, ma’ana mai ƙaura. Kamar dai yadda Sahabbai (Radiyallahu Anhuma) suka bar Makka ya zuwa Madina, har ake kiran su Almuhajirun.

    A wasu sassa na ƙasar nan, ana kiran su almajirai ne saboda suna yawo da ƙirgi ko buzu. Sannan kuma suna cin abinci a ƙwarya ko kwacciya kamar yadda baƙo ya ke yi. Babban dalili ko asalin yawon bundi wurin makaranta shi ne; rashin gwamnati makamanciyar gwamnatin Sayyadina Umar (Radiyallahu Anhu) wadda za ta ɗauki nauyin rayuwarsu. A ƙasashe Irin su Sudan da Libiya da Mauritaniya; makaranta a tsangaya ba sa ƙaura daga gari zuwa gari, kamar yadda muke gani a nan Nijeriya. Dalili kuwa shi ne galibin su suna samun taimako mai gwaɓi daga gwamnatocinsu da mawadatansu da al’ummarsu.

    A taƙaice dai yawon bundi ko ƙaurar malamai da almajirai daga gari zuwa gari, al’ada ce da ta keɓanci makaranta a tsangayun Najeriya; da wani yanki na Jamhuriyoyin Nijar da Chadi, saboda dalilan da suka gabata a wannan babi da kuma babi na huɗu a sashe na ɗaya; mai bayani kan birane da garuruwan da suka shahara da tsangayu a Arewacin Najeriya.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hausar Gardawa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Kayan Karatu A Tsangaya danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Asalin Tsibbu A Tsangayun Alƙur’ani

    Asalin Tsibbu A Tsangayun Alƙur’ani

    Tsibbu ararriyar kalma ce daga harshen Larabci “Ɗibbu” ma’ana magani. Kafin zuwan Musulunci, babu wata hanya ta magani sai bori da bokanci.

    Koda Musulunci ya bayyana, sai ya tsawatar ga barin abubuwan da suka ci karo da tauhidi da imani da Allah Maɗaukaki da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wa Sallam). Tsibbu dai ya samo asali ne daga irin yadda malamai ke horon iyaye da almajirai game da yin sadaka a matakin karatu daban-daban. A riyawar su, rashin yin hakan kan jawo

    wa almajirai haukacewa.

    Kasuwar tsibbu ta buɗe cikin tsangayu a daidai lokacin da aka fara hulɗa tsakanin malamai da ‘yan kasuwa da kuma masu mulki. Ma’ana, a da magungunan tsibbu waɗanda ba su wuce ayoyin Alƙur’ani ba, sun taiƙaitu tsakanin ahalin tsangaya.

    Musamman ma don kafin tilawa, da fahmi da gyaran hadda. Sai kuma ɓangaren mugunta, wadda ta shafi ɓata karatun wani, ɗaure karatun wani, ɓatar da kundi da dai sauran su.

    Farkon fitar tsibbu daga da’irar tsangaya kamar yadda (Jibrin, 1987) ke bayyanawa, ya faro ne daga ba wa mutane taimakon tsaron ƙasa da masu mulki. Sai kuma ba wa ‘yan kasuwa da fatake taimakon samun jama’a da tsari daga ‘yan fashi da ɓarayi. Su kuwa masu sana’o’i aka fara ba su taimakon albarkar hannu da tagomashi da tsaraka.

    A farko farkon bayyanar tsibbu, makaranta kan hausantar da nassin Alƙur’ani (Bunza, 1990) daidai da buƙatar da ake so a cimma, ba tare da an san fassarar ta ba. Misali:

    1. Laƙanin ƙarfin mazakuta: Sai a rubuta “Izazul” saboda kalmar “zul” ta yi kama da ƙarfin mazakuta a Hausance.
    2. Lakanin sauƙin haihuwa ko naƙuda: sai a rubuta “yakhriju min sul” don dai jinjiri ya fito sul.
    3. Laƙanin samun kasuwa: a rubuta “tabbat yada” ya zuwa “sayas” ma’ana za a sayar. Ko a yi wuridin “fala talumuni” musamman wurin Fulani, saboda kalmar “Lumo” na nufin kasuwa da Fulatanci.
    4. Laƙanin ga ‘yan dambe:sai a rubuta “kalla iza dukkatil ardi “dakkan dakka” saboda ya yi kama da sautin duka.
    5. Laƙanin damun fura:sai a rubuta “maadamuu fiha” saboda Kalmar “damu” tayi daidai da damun fura.
    A lokacin da ilmi ya ƙara bayyana sai masu tsibbu suka fara duban ma’anar aya ana haɗa ta da buƙatar da ta dace da ita kamar:
    – Maganin soyayya – “wa’alƙaitu alaika muhabbatan”
    – Maganiin makanta ko ciwon ido – “fabasarukal yauma hadid”
    – Maganin kafe mace – “maakisina fihi abada” Da sauransu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Narkewar Tsibbu Cikin Bokanci danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.