Tag: yadda ake

  • Ƙa’idoji Da Laduban Neman Halal

    Ƙa’idoji Da Laduban Neman Halal

    Abu ne sananne ga kowa cewa addinin Musulunci bai bar komai ba, sai da ya yi tanadin yadda yake so a fahimce shi, ko a aikata shi. Neman halal ko kasuwanci da sana’a ginshiƙi ne a rayuwar mutum, saboda haka ba a bar mutum ya yi yadda ya ga dama ba, a kasuwanci ko harkokin sana’arsa.

    Da farko an gina tunani da aƙidar ɗan kasuwa musulmi a kan waɗannan dirkoki:

    1) Dukiya Ta Allah ce:- Wato mutum ya sani ya kuma yarda cewa, duk dukiyar da take cikin duniyar nan, da ita kanta duniyar, mallakin Allah ce shi kaɗai. Amma ya bai wa ɗan Adam damar amfani da ita a bisa dokokin da ya tsara masa na shari’a. Wato duk abin da kake da shi kamar aro ko ajiya aka ba ka, amma an yarda ka ɗan taɓa daidai da tsarin da aka yi maka (Shari’a)

    2) Neman Falalar Allah: Duk sana’ar da kake ka dinga yin ta da fatan samun falala daga Allah a cikin ta, wato ka yarda Allah shi kaɗai ne mai bayarwa, kuma shi ne mai hanawa.

    3) Dogaro Ga Allah: Kada ka dogara da wayonka, iyawarka ko jarinka ko iyayen gidanka, kawai ka dogara ga Allah shi kaɗai shi ne mai azurtawa, kuma shi ne mai karɓe arziki yadda yake so, wanda ya so, a lokacin da ya so, kai dai ka yi ƙoƙari da dogara gare shi, sai ya taimake ka, ya yi maka fiye da yadda kake zato.

    4) Imani da Hisabi:- Musulmi ya yi imani da cewa ranar lahira za a yi masa hisabi kan duk abin da yadda ya yi amfani da shi, ta hanyar halal ne, ko ta hanyar haram? wannan imani zai hana musulmi hauma-hauma da ya-ki-halal da kuma ya-ki-haram a kasuwanci, zai kuma hana shi almubazzaranci da zalunci da saɓa wa Allah ta’ala da dukiyarsa.

    5) Neman Kuɗi ba ya hana bin Allah:- A kowane hali musulmi yake komai girman hada-hadarsa, kada ya mance da dokakin Allah da ambatonsa da kula da ibada, musamman sallah. A Musulunci, babu wani aiki ko sana’a da za a ce ba ruwan Allah da shi, ko kuma a ce ai in ba ai ƙarya, ba za a samu komai ba a kan waɗannan harkoki, ya wajaba dukkan musulmi ya gina harkar neman abincinsa. Allah ya sa mu dace. Amin.

    Bayan haka, ga wasu ƙa’idojin neman halal a Musulunci a taƙaice:

    1) A kauce wa Riba a kowanne Hali:-Allah ta’ala ya haramta riba da duk wata mu’amala da take da alaƙa da riba. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Allah ya la’anci mai cin riba, da mai ciyar da ita, da mai rubuta ta, da masu shaida a kanta; ya ce duk matsayin su ɗaya” Muslim ne ya ruwaito shi.

    2) An haramta Algus da Ha’inci da yaudara: Duk wani nau’i na ha’inci da yaudara, zamba da cin amana haramun ne a kasuwanci. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Wanda ya yi mana algus ba ya daga cikinmu”. (Muslim ne ya ruwaito shi).

    Hanyoyin ha’inci da algus suna da yawa kaɗan daga cikin su sune:

    1) Sayar da kaya marasa inganci da waɗanda lokacin amfaninsu ya ƙare (expiring date).

    2) Tauye mudu da ma’auni da rage nagartar abin sanyarwa (quality).

    3) Sanya tsofaffin kaya a cikin sabbin kwalaye da ledoji da gyara su,su zama kamar sababbi, a yi musu kuɗin sababbi.

    4) Sayar da duk wani abu da yake cutarwa ga lafiya da rayuwar ɗan Adam da dabbobi da tsirrai.

    5) Bayannan ƙarya da zugwigwita kayan sayarwa don kawai a jawo hankalin mai saye, musamman magunguna.

    6) Ha’inci a wajen gini, ta hanyar rage sumunti, ko rodi, a yi ginin da nan da nan zai tsatstsage ko ma ya ruguje.
    (2) Kaucewa duk wani aiki na haram ko wani abu da aka haramta amfani da shi a kasuwanci.

    Iri-iren waɗannan harkoki suna da yawa, kaɗan daga cikinsu su ne:

    1) Haramta saye da sayar da giya da dukkanin kayan maye.

    2) Saye da sayar da fina-finan batsa da mujalla da hotuna da duk wani abu da yake yaɗa ɓarna da ta’addanci.

    3) Keɓantar ta sakatariya wannan haramun ne, haka ma duk kasancewar ta sakatariya wannan haramun ne, haka ma duk wani aiki ko sana’ar da sai mace ta bayyana jikin ta sannan za ta yi ta.

    4) Sana’ar raye-raye da kaɗe-kaɗe da wasannin kwaikwayo da duk masu hannu a ciki irin su mai ba da umarni, mai ɗaukar hoto, mai kwalliya, mai ƙir- ƙirar labari, mai bada kuƙi , mai tsara waƙa, mai rerawa da sauran su.

    Na san wasu za su ga wannan hukuncin kamar ya yi zafi, to tambaya a nan gare su ita ce, shin a Musulunci wasan kwaikwayo (film) yana daga cikin uzurin ko dalili da suke halatta bayyana tsiraici yin ƙarya? Shin yana halatta keɓantar mace da wanda ba muharraminta ba? Shin wasan kwaikwayo zai iya halatta ɗimbin ayyukan saɓo, sabo da keta alfarmar shari’a da kyawawan ɗabi’o’i, har ma a ce wai sana’a ce ta faɗakarwa da ilmantarwa?

    Ni dai a iya ɗan karatuna, wanda bai kai ko rabin cikin cokali ba, da kuma gurguwar fahimtata, ban ga inda film zai iya halatta haramun ba. Sai dai an ce fahimta fuska?

    5) Saye da sayarwa da dillancin kayan sata da na ƙwace, duk wannan haramun ne. Haramun ne saye da sayar da duk wani abu da yake cutarwa ga hankali da lafiyar mutane da zaman lafiyarsu.

    Duk wata sana’a ko harka da ta ƙunshi zamba, yaudara, ha’inci, algus da rashin tabbas (garari) kan abin saye ko kuɗin wannan ma haramun ne.

    Waɗannan kaɗan ne daga ƙa’idodin kasuwanci a Musulunci, sai mu kula ko ma samu albarkar nemanmu.

    Su kuwa laduban kasuwanci, wato ɗabi’u da halaye da ya kamata duk wani ɗan kasuwa ko mai sana’a ko ma’aikaci ya siffantu da su, su ne:

    1. Kyakkyawar niyya ya kasance niyyarsa da burinsa a wannan harka da yake yi mai kyau ce.

    2. Fita a kan lokacin zuwa kasuwa ko gurin sana’a ko aiki. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya roƙi Allah ya sa albarka a harkar masu zuwa a kan lokaci, ban da masu makara.

    3. Ambaton Allah lokacin shiga kasuwa sai ka ce: la ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu lahul mulku wa lahul hamdu yuhyi wa yumitum wa huwa ala kulli sha’in ƙadir.

    4. Yiwa mutane sallama da amsa sallamar su a wurin sana’a ko kasuwa.

    5. Sauƙi da rangwame yayin saye da sayarwa da biyan bashi, ko karɓar bashi da yin sassauci ko afuwa ga wanda yake cikin ƙunci.

    6. Gaskiya da amana, babu abin da yake bunƙasa kasuwanci da kowacce harka sama da gaskiya da riƙon amana.

    7. Sifantuwa da kyawawan halaye kamar haƙuri, kyauta, kunya, godiya da sauransu.

    8. Cika mudu da ma’auni da bin ƙa’idojin aiki sau da ƙafa da inganta sana’a da kyautata ta.

    9. Yawaita ba da sadaka da fitar da zakka idan dukiya ta kai kuma lokaci ya yi.

    10. Cika alƙawari, ban da ƙarya, ban da yaudara.

    11. Ka guji yawan rantsuwa ko da a kan gaskiya ne ballantana a kan ƙarya.

    12. Kada ka ba da cin hanci, kuma kada ka karɓa.

    13. Ka guji duk wata mu’amala ta cuta da haram.

    14. Ka kula da sallah da sauran dokokin Musulunci.

    15. Ka guji saɓa wa Allah a gurin nema, kamar zina da luwaɗi shaye-shaye da sauransu.

    16. Ka kasance mai tsafta a jikinka da gurin sana’arka da abin sayarwarka ka ƙawata shi.

    17. Ka kasance mai sakin fuska da magana mai daɗi ga duk wanda hulɗa ta haɗa ka da shi.

    18. Ka kai zuciyarka nesa ka danne zuciyarka, ka guji saurin fushi da hasala.

    19. Ka dogara ga Allah shi kaɗai, ka yi ta godiya a gare shi, ka yi ta roƙon sa, ka yi ta ambaton sa.

    20. Ka mayar da hankalinka a kan sana’arka duk abin da bai shafe ka ba, ka rabu da shi.

    Duk ɗan kasuwa ko ma’aikaci ko mai sana’ar da ya kula da waɗannan ƙa’idoji da ladabai, haƙiƙa Allah ta’ala zai sanya masa albarka a cikin nemansa.

    Allah ta’ala ya taimaka mana. Amin.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Illolin Karɓe-Karɓe Da Barace-Barace danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ma’anar Roƙo Take danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Jerin Littafan Hadisai Arba’in (40) Littafi Na Biyu; A kan (Falalar Wadatar Zuci, Neman Halal Godiya Ga Allah Da Illolin Bara Da Roƙo); wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yadda Mutum Zai Kasance Mai Wadatar Zuci

    Yadda Mutum Zai Kasance Mai Wadatar Zuci

    1) Wadatuwa da abin da Allah ya ba ka.

    2) Karanta rayuwar magabata na ƙwarai da gudun duniyar su, da wadatar zucinsu da koyi da su.

    3) Gudanar da rayuwa matsakaiciya, ba ƙwauro babu kuma almubazzaranci.

    4) Yawaita addu’a, Allah ya azurta ka da wadatar zuci kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yake cewa; “Ya Allah ina roƙon ka shiriya, da taƙawa da kamewa da wadatar zuci”

    5) Yin cikakken imani cewa kowa a duniyar nan arzikinsa yake ci, tuni Allah ya gama raba arziki, babu yadda za a yi wani ya ci rabon wani.

    6) Tursasa zuciya a kan yarda rabon ta da arzkin da Allah ya ba wa mutum da nisantar kwaɗayi, da sa ido a kan abin hannun mutane.

    7) ƙarfafa imani da Allah da amincewa da shi

    8) Kullum ka rinƙa duban na ƙasa da kai, ka da ka rinƙa duban na sama da kai.

    9) Yarda da cewa Allah ta’ala ya ƙaddara lallai sai wani ya fi wani wadata. Tilas ka ga wasu sun fi ka, amma kuma ka fi wasu; wasu kuma kun yi daidai, haka Allah yai tsarinsa, to ina dalilin damuwa?

    10) Ka yawaita tunanin mutuwa da ziyartar maƙabarta, sai ka ji duk abin duniya ma ba ya ɗaɗa ka da ƙasa, domin ƙarshe dai ko me aka samu mutum zai tafi ya bar shi.

    11) Yawaita karanta Alƙur’ani da la’akari da ayoyin da suke magana a kan arziki da talauci da kuma haƙiƙanin ita kanta duniyar.

    12) Ka sani cewa girma da mutunci yana cikin wadatar zuci, shi kuwa kwaɗayi da talaucin zuci, ba ya haifar da komai sai ƙasƙanci da wulaƙanci.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hikimomi Akan Wadatar Zuci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Harsashin Gina Al’umma (Iyaye) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Jerin Littafan Hadisai Arba’in (40) Littafi Na Biyu; Akan (Falalar Wadatar Zuci, Neman Halal Godiya Ga Allah Da Illolin Bara Da Roƙo); wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Dabarun Zaman Lafiya Da Mutane

    Dabarun Zaman Lafiya Da Mutane

    A tasa gudunmawar a wannan fanni, shaihun malamı Abdullahi ibn Fodiyo (R.A) ya bayyana muhimman ƙa’i’doji waɗanda in mutum ya bi su, zai iya samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da kowane irin jinsi na mutane.

    Malamin ya yi wannan bayani ne a cikin littafinsa mai suna:

    “Aadaabu Mu’aasharat, Litaalibinnajaatı Fiddunya Wal Aakhirat”.

    Ga abin da malamin yake cewa:

    1. Ya ɗan uwa kada ka wulaƙanta kowa, domin kai ba ka san matsayin mutum ba a wurin Allah, wataƙila ya fi ka daraja

    2. Kada gafalallu ‘yan duniya masu sharholiya su ɗaɗa ka da ƙasa, har ka girmama su, saboda duniya ba a bakin komai take a ba wurin Allah.

    3. Ka kare mutuncinka, kada ka roƙi kowa sai Allah, sai dai bisa halin lalura. Kuma kada ka damu, ko ka zargi kowa in ka roƙa aka hana ka.

    4. Kada ka wahalar da kanka wajen yin wa’azi ga wanda ba ka ga wata alamar karɓar wa’azi daga gare shi ba. Kuma ka guji ambaton sunayen mutane (ko ƙungiyoyi) cikin wa’azinka.

    5. Idan ka ga mutane suna girmama ka, to ka gode wa Allah, ka roƙe shi ya tsare ka daga dogara ga mutane.

    6. Idan kuwa suka cutar da kai, to ka haɗa su da Allah, ka nemi kariyarsa daga sharrinsa, kada ka damu da ɗaukar fansa, har sai abin ya yı maka yawa, ka rasa da wanda za ka ji, ka ɓata goma ɗaya ba ta gyaru ba. Allah dai shi ne yake sanya a so mutum ko a ƙishi.

    7. Lokacin da kake cikin mutane, ka saurari maganganu na gaskiya, ka toshe kunnuwanka daga ƙaryace-ƙaryacensu. In za ka faɗi, faɗi gaskiya, ka zama bebe wajen faɗin zancen banza.

    8. Ka karanta abota da mutane, saboda yawancin mutane ba sa yin afuwa. ba sa rufa asiri, suna neman haƙƙinsu, amma su ba sa so su bawa mutane haƙƙinsu, sun fi yarda da ƙarya da kuma gulmace-gulmace. Kai zama da waɗansu mutanen ma dai ba shi da wata riba, farat-farat a fuska, amma a zuci ba sa sonka, kuraye ne su da fatun awaki, a kan zato suke yanke hukunci, ga su da yi da mutane, kuma ba sa da wani buri sai su ga bala’i ya same ka.

    9. Kada ka saki jiki da mutumin da ba ka san halinsa ba ta hanyar zama da shi a gida ɗaya, ko a kasuwa ko halin tafiya. Da kuma halayyarsa lokacin da yake cikin wadata da talauci, da murna da fushi. Sannan ka gwada mu’amala da shi ta kuɗi, ko ka bari sai lokacin da ka shiga cikin wani matsi, ka buƙaci taimakonsa ka gani zai taimake ka ko kuwa.

    Duk mutumin da ka gwada shi cikin waɗannan halaye ka ga ya haye to wannan shi ne mutum, in ya girme ka, ka ɗauke shi a matsayin uba, in ka girme shi ka mayar da shi ɗa, in kuma sa’anka ne, ka ɗauke shi a matsayin ɗan uwa.

    10. Ka karɓi aboki da maƙiyi cikin haba-haba amma ban da wulaƙantar da kai.

    11. Ka ja girman ka, amma ka guji girman kai.

    12. Ka ƙasƙantar da kanka, amma ka da ka wulaƙantar da kanka.

    13. Komai za ka yi, ka ɗauke shı (tsaka-tsaki).

    14. Ka guji yawan waiwaye lokacin da kake cikin jama’a.

    15. Kada ka rinƙa wasanni da sauran abubuwan ƙasƙanci a cikin mutane, kamar wasa da gemu, kwararrasa yatsu, sakace, gyaran hanci, yawan tofe-tofe da kaki, karairaya jiki, yin hamma ko atishawa a fuskar mutane.

    16. Ka zauna cikin nutsuwa, a yi magana cikiņ tsari.

    17. Ka saurari abokin hirarka lokacin da yake magana mai ma’ana. Kada ka zaƙe wajen nuna masa ya burge ka, kada ka nemi ya maimaita maganar.

    18. Ka daina yawan faɗar labaran ban dariya.

    19. Ka daina yawan faɗar nasarorinka da na iyalinka ko wakarka da sauransu.

    20. Ka guji ƙyale-ƙyale da caɓa ado kamar mace, amma kada ka zauna busu-busu kamar baiwa.

    21. Ka guji yawan sa kwalli.

    22. Ka guji naci.

    23. Kada ka goyi bayan kowa a kan zalunci.

    24. Kada ka bari ‘ya’yanka da iyalinka su san yawan kuɗinka, saboda in sun ga ba su da yawa, sai su raina ka, idan kuwa suna da yawa, sai su ci burin da ba za ka iya gamsar da su ba.

    25. Ka rinƙa yin barazana ga iyalinka lokaci-lokaci.

    26. Ka sassauta musu amma kar ya kai yadda za su raina ka.

    27. Kada ka rinƙa yawaita wasa da barorinka, sai su raina ka.

    28. Yayin da husuma ta haɗa ka da wani ka nutsu, ka guji wauta da gaggawa. Ka yi nazari sosai kan hujjojinka, kada ka yawaita waiwaye-waiwaye.

    29. Idan wani mai mulki ya ja ka a jiki, to ka yi taka tsantsan, kada ka saki jiki da shi, ka tausasa masa irin tausayin ka ga ƙaramin yaro, ka faɗi abin da zai faranta masa rai, in dai bai saɓawa shari’a ba. Kada ka yi karambanin shiga cikin harkokınsa da iyalinsa ko ‘ya’yansa ko mataimakansa.

    30. Ka guji abokin ta-faɗi-gasassa, wannan shi ne cikakken maƙiyi lokacin da duniya ta juya maka baya.

    31. Kada ka fifita kuɗi a kan mutunci.

    32. Idan ka shiga cikin mutane ka yi sallama, kada ka ƙetare mutane. ka zauna duk inda ya samu ya samu, ka yi wa na ƙasa da kai sallama.

    33. Ka guji zaman hira a gefen hanya; sai fa in za ka baiwa hanya haƙƙinta, shi ne kau da kai daga kallon haramun, taimakon wanda aka zalunta, agaza wa mabuƙaci, kwatance ga ɓatacce, amsa sallama, taimakon mabaraci, umarni da kyakkyawan aiki da hani ga mummunan aiki da kuma tanadin wuri na musamman domin yin kaki, ban da tofarwa a alƙibla, ko barin dama ko hagu sai dai a ƙarƙashin ƙafarka ta hagu.

    34. Kada ka zauna da masu mulki, in kuwa aka jarrabe ka da zama da su, to ka guji yi da mutane da ƙarya. Ka riƙe sirri, ka karanta buƙatu da kakaci, kai dai ka yi kaffa-kaffa da su. Ban da bankaɗa a irin su ko sukar mulkin su, ko ci musu mutunci, domin masu mulki ba sa yafe waɗannan laifuka.

    35. Kada ka yawaita zama da gama-garin mutane, in zama ya haɗa ka da su, kada ka sa baki a cikin hirarsu, ka kau kai daga munanan lafazuzzukansu, ka ƙaranta haɗuwa da su da yawan kakaci. Saboda yawan kakaci yana zubar da mutunci, da haifar da gaba, da mutuwar zuciya yana sanya rafkana yana janyo ƙasƙanci,, da kashe zuciya. ldan ka zauna a wuri aka yi kakaci yana da kyau kafin a tashi a karanta wannan addu’a:

    “Subhana kallaa humma wa bi hamdika ash hadu an laa ilaaha illaa anta astagfiruka wa a tuubu ilaika”.

    Domin karanta cikakken bayani akan Zaman Lafiya Da Iyali danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Ziyarar Mara Lafiya danna nan.

    Wannan bayanin anciro shi ne daga Littafin Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali; wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

     

  • Shirye-Shiryen Gidajen Rediyo A Kano Da Tasirinsu Ga Tarbiya

    Shirye-Shiryen Gidajen Rediyo A Kano Da Tasirinsu Ga Tarbiya

    “Wanda ya mallaki bayanai, ya mallaki duniya”

    -Nathan Rothschild.

    Guglielmo Marconi, Reginal A. Fessenden da sauran waɗanda suka ba da gudumawa wurin samar da rediyo don wasu amfani da a tunaninsu bai taka kara ya karya ba. Amma bayan wasu ƙarnuka masu yawa da wucewar su, an samu ci gaba sosai a rayuwar mutane, wannan yasa an fahimci tasirin rediyo da kuma gidajen rediyo. Musamman idan muka kalli ƙasashen Turai a yaƙin duniya na biyu, sun yi amfani da gidan rediyo don yaɗa  farfaganda. Saboda sanin mahimmanci da tasirin rediyo ya sanya ƙasashe kamar su Birtaniya buɗe sashen Hausa da sauran sassa da ba na Turancin Ingilishi ba, don cimma manufofinsu.

    Gwamnatoci sun fahimci tasirin da rediyo take da shi a rayuwar waɗanda ake mulka, wannan yasa gwamnatoci kakkafa gidajen rediyo don isar da manufofinsu da ƙudurorinsu, wasu lokutan don isar da wata manufa ta ƙashin shugabannin. Haka ma manyan ‘yan kasuwa/attajirai da `yan siyasa sun fahimci wannan tasiri da rediyo take da shi, su ma sai suka fara kakkafa gidajen rediyo don tallata manufarsu na kasuwanci ko siyasarsu.

    Wannan tasiri za mu iya ganin shi a fili, idan muka kalli yadda mutane da yawa suka mai da rediyo makusanciya ta mussaman, wadda ba a iya rabuwa da ita, don harkar saye da sauran mu`amala da ita. Mutane sun mayar da gidajen rediyo wurin samun labaru da sanin abin da yake faruwa na yau da Kullum. Wasu lokuta yadda mutane suka yi amanna da duk abin da aka faɗa a gidajen rediyo, yakan zamo abu mai wahala kafin ka canza su. Ba wani abu ba ne, sai tasirin abin da aka faɗa ta hanyar rediyo da yawan nanata shi.

    A Kano an fara kafa gidan rediyo mai zaman kansa ne a shekarar 2003,  tun daga wannan lokaci ya zuwa yanzu, ana hasashen gidajen radioyo masu zaman kansu sun kai sama da guda ashirin (20+). Mai karatu ya san duk waɗannan ba a banza ake buɗe su ba, amma babban abin lura shi ne an fahimci tasirinsu ne a cikin al`umma da rayuwarsu.

    Duk wanda ya buɗe gidan rediyo yana da dalilinsa da manufar da yake so ya isar ko ya cimma, ba manufar kaɗai ake gabatarwa a waɗannan gidajen radiyo ba, ana gabatar da wasu shirye-shirye na daban waɗanda su ma suke da tasirinsu a cikin  rayuwar mutane. Kamar shirye-shiryen abubuwa da suke faruwa na yau da kullum a cikin al`umma. Duk wanda yake Kano ko yake sauraron shirye-shiryen gidajen rediyoyin Kano, ya san irin waɗannan shirye-shiryen, waɗanda aka samo daga wani shiri daga gidan rediyon Kano mai suna “Taskar Labarai”.

    Waɗannan shirye-shirye suna da matuƙar tasiri a cikin rayuwar mutane fiye da yadda ake tsammani. A mafiya yawan lokuta, a waɗannan shirye-shirye ana yawan kawo labarukan manya-manyan laifuka, kamar fyaɗe ga ƙananan yara. Duk lokacin da aka yi wa masu gabatar da waɗannan shirye-shirye magana kan yadda suke faɗan waɗannan laifuffuka, sai su ce kaso mafi ƙaranci na irin abin da yake faruwa da suka samu haƙiƙanin labarai a kai suke faɗa.

    Tasirin irin waɗannan shirye-shirye ga tarbiyya, abu ne mai girma wanda ba a ganin tasirin abin a lokaci guda. Amma idan an lura sosai suna da tasiri mai yawa ga tarbiyya. Idan muka dubi abin ta ɓangaren tarbiyya, za mu ga irin waɗannan shirye-shirye suna da mummunan tasiri ga tarbiyya ta ɓangarori kamar haka:

    Na farko duk abin da ake faɗa a fili musamman ta hanyar rediyo, bisa dukkan dalilai yakan kai inda ba a zato, to a nan, ana sanar da wanda bai sani ba, sannan ana tunatar da wanda ya manta, ana kuma jaddada wa wanda ya sani wani abu. Shi kuma a shari’ance da tarbiyya, ba a son bayyana ɓarna. A hadisin Abi Hurairah ya ce, na ji  Manzon Allah (SAW) ya ce: “Dukkan al`umata waɗanda ake yi wa rangwamen zunubansu ne (wato ana yafe musu)  sai masu bayyana ɓarna” – ba masu aikin gidan rediyo ake nufi a nan ba, ana nufin waɗanda idan suka aikata ɓarna a ɓoye sai su fito fili suna faɗa. Waɗannan su ake nufi. Amma mene ne dalilin da ya sa aka ce ba a yi wa masu bayyana ɓarna rangwame? Saboda koya wa wasu suke yi, kuma nuna wa wanɗanda da ba su sani ba suke yi da kuma tunatar da waɗanda sun gafala daga aikata ɓarna suke yi. Wannan shi ne abin da suke yi kenan. Wanda bai san fyaɗe ba, an faɗa masa kenan sai ya fara tunanin aikatawa da hanyar da zai kauce, kada a kama shi kamar yadda aka kama na baya.

    Na biyu yawan fadin waɗannan laifuffuka, yakan dasa waɗannan laifuffuka a zuciyar mutane, musamman matasa. Shi yasa za a ga matasa sun fi kowa yawan faɗawa cikin ɓarna da laiffufuka musamman waɗanda ake yawan tallata su”

    Na uku yawan fadin laiffufuka yana ƙara yawaitar su, da ƙaruwarsu. Misali a yanzu zai yi matuƙar wahala a yini ba a ji labarin garkuwa da mutane ba, tun ana jin labarin a Kudancin ƙasar nan, yanzu ga shi har gida kuma ƙaruwa yake yi a kullum. Duk da akwai dalilai daban-daban na ƙaruwarsa, wanda rashin ɗaukar ƙwaƙƙwaran hukunci a kan masu aikitawa yake ƙara yaɗuwarsa da sauransu.

    Misali na biyu na irin shirye-shiryen da gidajen rediyoyi suke gabatarwa mai tasiri sosai a cikin al`umma su ne shirye-shiryen siyasa. Ta yadda ake bai wa mutane dama su faɗi albarkacin bakinsu. Mutane da yawa ba sa lura da mummunan tasirin abin ga tarbiyya. Idan muka duba sosai kafin yaɗuwar gidajen rediyo da waɗannan shirye-shiryen a Kano, malamai da  sarakuna da kuma manyan mutane suna da matuƙar ƙima da daraja a idon mutanen gari, amma a yanzu saboda waɗannan shirye-shirye ya sa mutane da yawa sun samu dama na cin mutuncin malamai da sarakuna da kuma shugabannin al`umma. A Kano kowa ya san a yanzu waɗannan mutanen da na faɗa a sama duk da ƙimar da suke da ita a baya, kowa yana iya shiga gidan rediyo ya faɗi maganar da yake so a kansu kai tsaye. Wannan tasirin waɗannan shirye-shiryen ne kai tsaye. 

    A bangaren tarbiyya, rashin girmama babba a al`umma alamu ne na rugujewar tarbiyya da taɓarɓarewar al’umma, kuma alama ce ta lalacewar wannan al’umma. Tasirin waɗannan shirye-shirye kenan ga tarbiyya.

    Wannan su ne kaɗan daga cikin tasirin gidajen rediyo a rayuwar al’umma da tarbiyyarsu. Saboda haka, ya kamata mu san irin shirye-shiryen da ya kamata mu dinga saurara. Sannan kuma lallai shugabannin addini su tashi su faɗakar da mutane game da irin waɗannan abubuwa da suke lalata tarbiyyar al’umma. 

  • Abubuwan Da Suke Hana Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

    Abubuwan Da Suke Hana Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

    Wannan muhimmin abu wanda kowa yake buri, yana gamuwa da cikas da matsaloli daga ɓangarori daban-daban. A gaskiya ma dai mutane da dama masu begen zaman lafiya da kwanciyar hankali, su da kansu suke janyo hargitsi da tashin hankali ga kawunansu da sauran mutane.

    Wannan kuwa yana faruwa ta hanyar aikata abubuwan da suke hana zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ga wasu daga cikin waɗannan abubuwa:

    Kafirci

    Kafirci shi ne babban abu da yake hana zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma wannan yana nufin kafirai su ne manyan maƙiya ga zaman lafiya da kwanciyar hankali. Allah Ta’ala ya ce “Kuma wanda Allah ya yi nufi ya ɓatar da shi, sai ya sanya ƙirjinsa a ƙuntace, kamar mai hauhawa cikin sama” (Suratul An’am: 125).

    Wannan aya tana siffanta irin damuwa da ƙunci da tsiya da kafiri yake ciki saboda kafircinsa. Ko da kuwa ya mallaki komai a duniyar nan. Dalilin wannan shi ne babu imanı tabbatacce a zuciyarsa, kuma ba shi da tabbatacciyar makomarsa.

    Ga rashin ƙa’idoji da ladabai na gaskiya masu tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    Misalai a nan suna da yawan gaske, amma gajeren nazari kan rayuwar kafiran Amurka da sauran ƙasashen Turai na yaɗuwar kowace irin ɓarna, kamar fashi, fyaɗe, kisan kai da baƙin zalunci da ɗimuwa da madawwamiyar firgita, zai nuna mana yadda kafirci ke hana zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya Allah ka ƙara kiyaye mu. Amin.

    Saɓon Allah da aikata miyagun laifuffuka

    Saɓo da mugunta su ne abubuwa masu daraja ta biyu da suke fatattakar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan abu a fili yake, saboda duk wani mai saɓon Allah cike yake da ɓacin rai tsoro da rashin kwanciyar hankali. Misali mazinaci yana cike da tsoro da firgita don kada a gan shi, kuma yana gamawa sai wani irin mummunan ɓacin rai ya turniƙe shi. To ka auna halin da ɓarayi, ‘yan fashi, manema maza da sauran masu saɓo suke ciki. Su da kansu sun san babu zaman lafiya da kwanciyar hankali a tare da su.

    Ga abin da kafirin Bamaguje Wani mashahurin masanin falsala wato “Socrates yake cewa: “Haƙiƙa duk mai laifi ba ya rabuwa da tashin hankali da tsiya, musamman wanda ba a yi masa hukunci ba”. Ubangiji Ta’ala ya ce “Duk wanda ya kau da kai daga ambatona (Shari’ a ta) to haƙiƙa rayuwa mai ƙunci za ta tabbata a gare shi, kuma za mu tashe shi ranar Ƙiyama makaho” (Suratu Taha: 122) A wannan aya Allah Ta’ala ya tabbatar da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali ga duk wanda ya keta hurumin shari’arsa, ya kama son zuciya ƙaunar nau’o’in saɓo da aiki da “kwance-tushe (constitution).”

    Hassada da ganin ƙyashi

    Hassada wani mummunan ciwo ne da yakan kama zukatan masu raunin imani da jayayya da ikon Allah. A duniyar nan babu wahalalle irin mahassadi. Saboda shi kullum baƙin ciki yake ga baiwar da Allah yake yi ga bayinsa, in tashi ne a kwace a ba shi, ko a fasa kowa ya rasa.

    Asara biyu ce ke afkuwa ga mahasadi, ta farko a duniya, domin a maimakon Allah ya kwace baiwarsa ga wanda yake yiwa hassadar, sai ma dai ya ƙara antayo masa ita, shi dai sai dai ya yi ta ci baya, haka zai ƙare a tsiya ce.

    A nan Bahaushe ya yi gaskiya, inda ya ce, “Hassada ga mai rabo taki ce”.

    Asara ta biyu ta shafi addini, da farko dai ga zunubin fushi da jayayya da hukuncin Allah, Ga zunubin gaba da musulmai, ga koyi da shugabannin mahassada wato Shaiɗan, Kabila da Arna, sannan kuma uwa-uba, hassada tana cinye lada kamar wuta da shiba. Ya ɗan uwa in dai kana son zaman lafiya da kwanciyar hankali, to ka wanke zuciyarka, ka saki ranka ka yarda da ikon Allah, in ka ga Allah ya yi ni’ima ga wani kada ka yi fushi, in kai ma kana so, ka roƙi Allah kuma ka bi halaltacciyar hanya domin neman abin. Sai ka huta da wahalar banza.

    Gaba da riƙo

    Gaba da mutane da matsanancin riƙo a cikin zuciya, su ma suna kandagarki ga samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan shi ya sa kafin muminai su shiga aljanna sai an wanke zukatansu tas, an kawar da duk wani fushi da gaba daga zukatunsu, saboda ita aljanna gida ne na zaman lafiya da kwanciyar hankaii, mai gaba da riƙo kuwa ba shi da wani rabo a cikin wannan babbar ni’imá ta Allah. Saboda haka ɗan uwa ka so ‘yan uwanka musulmai, ka yi musu afuwa ka mance baya, domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    Fushi

    Duk mutumin da ba shi da haƙuri, mai saurin fushi bini-bini ya tada jijiyar wuya yana huci, to haƙiƙa wannan mutum ba shi ba zaman lafiya ballantana kwanciyar hankali.

    Dalilin wannan kuwa a fili yake saboda ita wannan rayuwa cike take maƙil da abubuwan haushi a kewaye da ɗan Adam, dole ka ji ko ka gani ko ka shaƙa, a gida ko a hanya ko a kasuwa kai har a masallaci da makarantu, to in ba ka yi haƙuri ba yaya za ka yi? Sai dai in za ka iya zama kurma kuma makaho, in kuwa ba haka ba, to ka yi haƙuri, in duk ka ƙi wannan to ka yi sallama ke nan da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    Zalunci

    Allah Ta’ala ya ce: “Haƙiƙa azzalumai ba za su rabauta ba (Suratu Yusif: 23). Wannan aya ta tabbalar ƙarara cewa ko a duniya ko a lahira da azzalumai ba su taba samun zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.

    A halin yanzu babu buƙatar dogon bayani a kan wannan magana. Babbar shaida ita ce irin matsanancin tashin hankali da firgita da manyan azzalumai suke ciki a ko’ina a duniya. Duk inda za su za ka gansu a guje, suna kulli-kurciya da wasan ɓuya da jama’a. kai da dama daga cikinsu ba sa iya barci, sai sun sha ƙwaya, kuma duk inda za su, sai ka ga tsaro da muggan makamai kamar za a yaƙin duniya. Daga ƙarshe Allah yakan ƙarbi rayukan azzalumai cikin ƙasƙanci da wulaƙanci da tozarta. Kai Allah wadaran azzalumi. ɗan uwa a guji zalunci babba da ƙarami domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali

    Tsoron wanin Allah

    Duk mutumin da baya tsoron Allah, to lallai zuciyarsa za ta cika da tsoro da fargaba, mai dalili da mara dalili. Duk lokacin da mutum ya shiga cikin irin wannan hali to shi da zaman lafiya da kwanciyar hankali sai yadda ta yiwu.

    Imamu Malik (Radiyallahu Anhu) ya ce “Ka ji tsoron Allah sai komai ya ji tsoron ka, in kuwa ba haka ba sai ka yi ta jin tsoron komai har inuwarka”
    To ɗan uwa ina ka nutsuwa ga wannan mutum?

    Camfi

    Wani Shaihin malami mai nazari kan ɗabi’ar ɗan Adam Dokta Aziz Farid ya ce: “Mai imani da camfe-camfe yana faɗawa cikin musibu fiye da waɗanda yake tsoro”!

    Wato duk mutumin da ba zai yarda da tsarin Allah ba cikin rayuwarsa, a’a ya miƙa wuya ga camfe-camfe sai an yi kaza-kaza zai faru, in ba a yi kaza ba kaza ba zai faru ba, to wannan shi ma ya yi sallama da zaman lafiya da kwanciyar hankali. In kana so ka tabbatar da wannan magana, ka yi nazarin rayuwar mutumin da ya yi imani da camfi ka ga ruɗu da firgici, ɓacin rai, wahala, tashin hankali iri-iri rashin zaman lafiya da kowa. Ya Allah ka tsare mu.

    Mummunan zato

    Allah Ta’ala ya ce “Ya ku waɗanda suka yi imani, ku nisanci yawancin zato saboda wani sashi na zato zunubi ne” (Surat Al-Hujrat: 12). Kuma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ku guji zato, saboda zato shi ne mafi ƙaryar zance” (Bukhari da Muslim ne suka rawaito).

    Idan mutum ya kasance kullum cikin mummunan zato ga kowa to zai rasa abokin zama, saboda da haka sai ya kasance cikin tsoro da tashin hankali, daga nan sai ya yi ban kwana da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    Girman kai

    Mai girman kai yana rayuwa cikin tsiya, nunƙufurci da ɗacin rai, kafin kuma ya tunkuyi burjı (mutuwa) ya madawwamiya. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: game da rayuwar ƙasƙanci “Wanda yake ɗauke da ƙwayar zarra na girman kai a zuciyarsa, ba zai shiga Aljannah ba” (Bukhari).

    Mutum mai girman kai, yakan take gaskiya, ya rinka wulaƙanta mutane, kuma duk da haka shi yana so a girmama shi, amma sai burinsa ya kasa cika, daga nan sai fushi da damuwa ya kama shi, sai zalunci shi ke nan shi ma sai ya nemi zaman lafiya da kwanciyar hankali ya rasa. Allah ya jiƙan Ɗan Maraya inda yake cewa “Girman kai rawanin tsiya”.

    Rataya zuciya da wanin Allah

    Wannan ya haɗa ka ƙwallafa rai, ka da wannan ya haɗa sakankancewa da samun wani abu daga wani mutum ko abu, ko makauniya kuma matsananciyar soyayya ga wanin Allah. Yin haka yana jawo ɗimbin wahala da ɓacin rai da tashin hankali. Ya ɗan uwa domin tabbatar da haka yi ƙoƙari ka karanta labarin nan na soyayya na Majnun Laila ka ga irin rayuwar wahala da tsiya da ya yi, kuma duk a banza. Ko kuma ka yi nazarin rayuwar wani wanda ya ƙwallafa ransa kan wani mutum ko albashi ko sana’a ya mance da Allah, ka ga yadda suka yi hannun riga da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    Shan abubuwa masu sa maye.

    Waɗansu ƙidahumai sokwaye sukan danƙarawa kansu ƙwayoyi da sauran abubuwa masu daɗin rai da nutsuwa, sa maye wai don su sami daɗin rai da nutsuwa, amma ina! Sai ka ga kamar mai ihun gobara ne, kuma ya tuttula fetur a cikin wutar. To yanzu mai karatu ka taɓa ganin wani ɗan ƙwaya cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali? A yi hattara.

    Waɗannan kaɗan ne daga cikin abubuwan da suke hana zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma.

    Wataƙila mai karatu ya ce, to shin waɗanne abubuwa ne suke tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na gaskiya? To mai karatu ya gyara zama ka sha karatu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Suke Kawo Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Sakamakon Zalunci Yake danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali; wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Ruɗani Game Da Hanyoyin Samun Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali.

    Ruɗani Game Da Hanyoyin Samun Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali.

    1. Kuɗi

    Waɗansu mutanen gani suke yi, ba mai more rayuwa a duniyar nan da samun natsuwa sai mai kuɗi. Shi ne kawai yake iya huce haushin duniya, ai in ka sami kuɗi ka sami komai, ka haye ka wuce tsara, ka fi ƙarfin raini, haka suke gani.

    To amma shin kuwa abin haka yake mai kuɗi shi ne yake samun zaman lafiya da kwanciyar hankali?

    Bari mu ga waɗannan ‘yan misalai guda biyu:

    Ƙaruna biloniyan biloniyoyin duniya.

    Tun da Allah ya yi duniya ba a taɓa mutum mai mahaukaciyar dukiya ba irin Ƙaruna.

    Alƙur’ani ma da kansa ya jinjina irin tarin dukiyar da Allah ya mallaka masa. Ya zama tauraron duniya son kowa ƙin wanda ya rasa. Duk inda ya yi, sai sha’awarsa ake yi, ana haɗiyar yawu, ana ina ma ni ne Ɗanƙaruna. Yana takawa ɗaiɗai, yana hura hanci yana ganin ya fi kowa, babu wanda ya isa sai shi.

    Amma a ƙarshe kuɗinsa ne suka jawo masa halaka. Saboda irin girman kai da ɗagawa da ya rinƙa yi Allah ya halakar da shi da dukiyarsa. Karanta sura ta 28, suratul Ƙasas ka sha labari.

    Christina Aunasis

    Wata hamshaƙiyar biloniya ce yar ƙasar Jamus, wacce ta gaji dukiya ta fitar hankali daga iyayenta. Ubanta ya mutu ya bar mata tsabar kuɗi wuri na gugar wuri Dala miliyan dubu biyar da jiragen ruwa maka-maka, da na sama jibga-jibga, kai har tsibirai ubanta ya bar mata, ba a ma maganar gidaje gonaki da filaye. To shin wannan dukiya ta kawo mata zaman lafiya da kwanciyar hankali?

    Ga taƙaitaccen labarinta. Uwarta dai ta mutu cikin baƙin ciki da mummunan yanayi, bayan ubanta ya wulaƙanta ta ya sake ta. Yayanta kuma jirginsa na sama ya hau yana ta wasan asha-ruwan-tsintsaye a kai, sai kawai ya rikito da shi ya mutu. Shi Kuma ubanta neman suna ne ya kai shi ya auri tsohuwar matar tsohon shugaban Amurka “John Kennedy”. Duk da ta kafa masa sharaɗin ba za ta yarda ya kwanta da ita ba, kuma ba wani umarni nasa da za ta ɗauka ga kuma miliyoyin daloli da ya kashe-kashe, amma ka san mai jan kunne da neman suna….. duk da haka zaman bai yi daɗi ba ya sake ta. Haka dai ya mace cikin damuwa da alhini.

    Yanzu saura “Christina” ita kaɗai tare da ɗimbin dukiyarta. Da farko ta auri wani ɗan Amurka, amma ba a shekara ba ta sake shi. Sai ta tafi “Grecce” ta sake yin aure, shi ma abin bai yi daɗi ba, ta sallame shi.

    Daga nan sai ta nufi Rasha Kasar gurguzu, inda ba a yarda mutum ya zamo mai kuɗi ba, duk da haka ta yarda ta auri wani ɗan Rasha ta zauna ita kaɗai, ko yar aiki ba ta da ita, da ‘yan jarida suka tambaye ta yaya haka kuma? Sai ta ce, “Lalube nake ko na sami kwanciyar hankali”. Shekararta ɗaya a Rasha ta saki wannan miji. Sai ta nufi Faransa.

    A can ta auri wani Bafaranshe, aka yi gagarumin biki, ‘yan jarida suka tambaye ta game da dukiyarta sai ta ce: “Ni ce macen da ta fi kowa kuɗi a duniya, kuma ni ce macen da ta fi kowa hankali a duniya!”

    Bayan sun haifi ‘ya mace da wannan bafaranshe sai ta sake shi. Kai a ƙarshe dai tsintar gawar ta aka yi a Ajantana har yau ba a san dalilin mutuwarta ba.

    A gaskiya kuɗi dai shi kaɗai bai isa ya tabbatarwa da mutum zaman lafiya da kwanciyar hankali ba. Shi dai neman sa wahala, in an samu ba hutu, saboda tsoron kada su ƙare. Ga yawan tunani da damuwa. Ga tsoron ‘yan fashi ɓarayi da ‘yan ina-da- kisa, da zalunci a gwamnati, ba cikakken zama, ballantana isasshen barci, abinci ma ba shi da cikakken lokacinsa, ballantana iyali. Kai tashin hankalin yana da yawa. Allah ya kyauta, ya kuma ba mu na rufin asiri.

    2. Suna

    Waɗansu kuwa sukan ɗauka cewa kwanciyar hankali yana cikin yin suna. A ɓangaren wasan kwaikwayo da wasannin motsa jiki kamar ƙwallon ƙafa kokawa da sauransu. Masu irin wannan tunani za ka ga suna matuƙar sha’awar taurarin ‘yan wasa da shahararrun gwanaye a ɓangaren wasannin motsa jiki.

    To amma masu wannan tunani sun tafka kuskure, saboda babu waɗanda suka fi taurarin ‘yan wasa tashin hankali da rashin zaman lafiya. Ka ɗauki ƙwallon ƙafa, misali irin faman wahala da suke sha wajen gwaji (training) da wulaƙanta da suke kafin su cancanci zama zakaru, ga rashin zama wuri ɗaya, da dama daga cikinsu sukan salwantar da karatunsu saboda ƙwallo. Sukan shiga halin tsoro da faɗuwar gaba duk lokacin da za su kara da wani kulob. Idan kuwa ba su yi nasara ba, ai sun shiga uku a wajen magoya bayansu, za su sha la’ana da zagi, wani lokacin ma har da duka.

    Kuma ba wuya an mance da mutum, an koma kan wani gwarzon, shi kuma an jefa shi a kwandon shara. Daga nan sai ya shiga rayuwar takaici da ɓacin rai, musamman ganin ana yi babu shi. Haka dai zai ƙare ya mace a wulaƙance.

    To don Allah ɗan uwa ina abin sha’awa a nan.

    To in ka ɗauki ‘yan wasan kwaikwayo su ma haka suke, farkonsu shaye-shaye da lalata da rashin zama wuri ɗaya, rashin mutunci, rashin kunya ga zunubin ɓata tarbiyya, sannan kuma da tauraron mutum ya disashe, sai a tattara shi a koma wani. Ya mutu a banza ba addini ba adila. Shin yau ina su Pele James Brown, Amita, Dram, Danhaki, Gaso-rogo da sauransu?

    To haka ma kwanan nan za ka daina jin su wane da wance, an koma gefe ana nadama marar amfani. A gaskiya babu wata nutsuwa da kwanciyar hankali cikin waɗannan wasanni. Allah ya ganar da mu amin.

    3. Mulki

    To ko a cikin mulki da riƙon muƙamai sirrin zaman lafiya yake?

    Waɗansu da dama suna ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali na ga mulki, haka suke gani. Amma ga mai lura ya san abin ba haka ba ne. Ɗauki masu riƙe da muƙamin siyasa a yau, ga dai kuɗin kamar na Ƙaruna, ga su ɓulɓul da manyan riguna, gidaje da motoci da sauran kayan alatu. Amma shin suna iya watayawa cikin ‘yanci kamar kowa?

    Ai ko wawa ya san wannan guje-guje da rundunar yaƙi da take biye da su, ba na lafiya ba ne. Kuma wace irin wahala ce ba a sha ba kafin a samu mulkin? Sannan in an samu, sai a kasa zaune a kasa tsaye ana tsoron sharrin ‘yan adawa da kuma gushewar mulkin. Daga nan sai cutar tazarce ta kama mai mulki.

    Sai hauma-hauma da danniya ko ta-zarce ko ta-kauce. In ta-zarce ƙarin matsala in kuwa ta-kauce to sai dai a lallaɓa “Chairman” domin har hauka ta-kauce kan haifar, komai zai iya faruwa.

    Akwai ɗimbin misalai a kan wannan batu nawa. Shin ina su Fir’auna da Hamana? Ina su Shah na Iran, Ferdinand Marcos na Filfin, da Mabutu na Zaire da Abacha na Nijeriya. To ai duk ba a nan take ba, in fa ba a shimfiɗa adalci ba, to tashin hankali sai an je lahira. Allah ya tsare mu. Amin.

    To kaga dai zaman lafiya da kwanciyar hankali na gaskiya babu shi a cikin mulki sai in a lahira ga shugaban da ya yi adalci.

    4. Wayewar kai da ci gaba

    In haka ne za mu iya cewa wayayyun mutane waɗanda suka ci gaba suke da fasahar ƙere-ƙere da ƙirƙire-ƙirƙire su ne masu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wato dai kamar irin su Amerika da ƙasashen Turai da ‘yan boko-addini. To amma bari mu yi nazarın su, su ma mu gani.

    A gaskiya duk ɗan boko da ya amsa sunansa ya san irin firgici da tashin hankali da Turawan yamma da na gabas suke ciki abin sai su. Tarbiyya ta daɗe da yin ƙaura daga wannan yanki har an mance da sunanta. Mutunci ba a yayin sa. Tuni mutanensa suka faku. Rayuwar ƙunci kuwa da fatara da rashin sanin inda aka dosa, sai wanda ya zauna da su ko yake karanta littattafai da mujallu da suke fitowa daga can.

    Wannan shi ne ya sanya a koda yaushe suke kashe kansu ta hanyar rataye kai, ko shan guba ko kuma bindige kai, to don Allah ɗan uwa ina zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin wannan rayuwa.

    Mai karatu ruɗani game da hanyoyin samun nutsuwa yana da yawa ta yadda waɗansu Wawayen ma gani suke yi ta hanyar shaye-shaye da aikata miyagun laifuka kamar zina, liwaɗi, fashi da sauransu, wai ta waɗannan hanyoyi za su iya cimma burinsu. Amma ina! Sai ka ga waɗannan mutane su suka fi kowa shiga tasku cikin rayuwarsu. Haka nan sukan rayu cikin tsiya da wahalar zuciya kuma su yi mummunar mutuwa, su je su tarar da mummunar makoma.

    Allah ya tsare mu.

    To mai karatu tun da dai mun ga babu ci cikin waɗannan abubuwa to mene ne haƙiƙar abin da ya ke hana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali? Karanta waɗannan babi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Su Ke Hana Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ziyarar Mara Lafiya danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali; wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

  • Zaman Lafiya Da Iyali

    Zaman Lafiya Da Iyali

    Allah Ta’ala ya ƙaddara rayuwar mace da namiji a tare cikin tsananin buƙatar juna; babu wanda zai iya rayuwa shi kaɗai a cikin su. Saboda haka ya zama wajibi mutum ya nemi hanyoyin zaman lafiya da abokin zamansa.

    A ɓangaren maza, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya yi umarni da juriya da haƙuri da kau da kai, da auna kirkin mace da rashin kirkinta, sai a dubi ɓangaren kirkin a kau da kai daga ɗaya ɓangaren. Kuma a aikace rayuwarsa (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) cike take da misalai kan haƙuri.

    Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam)ya ce; “Ku kyautata wa mata, saboda su an halicce su daga karkataccen ƙashin haƙarƙari, in ka ce za ka miƙar da shi, sai ya karye, karyewar sa shi ne saki”. (Bukhari da Muslim).

    Kuma (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce; “Kada mumini ya ƙi (matarsa) mumina, in tana ɓata masa da wasu halayen, ai tana faranta masa da waɗansu”. (Muslim).

    Wannan Hadısi ya nuna wa ma’aurata da su zama masu godiya da afuwa ga juna; kada a rinƙa kallon juna da ido ɗaya, ai idan rai ya ɓaci, to a yi amfani da hankali a duba amfanin juna ga juna, wannan sai ya shafe kowane irin laifi.

    Sannan kai miji duk abin da za ka yi wa matarka, ka yi mata shi saboda Allah kawai! kada ka ɗau don ba ta gode ba, ko ba ta yaba maka ba, mafi yawancin mata ba su san su yi godiya ga alherin mazajensu ba. In ka fahimci haka, sai ka zauna lafiya.
    lta kuma mace, babban abin da yake kanta shi ne, cikakkiyar biyayya da nuna ƙauna ta gaskiya ga mijinta. Tsaftar jiki da tufafi da mahalli da tattali da iya girki da sakin fuska da kuma magana mai daɗi; Sinadarai ne na zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin miji da mata.

    Wani masanin halin ɗan Adam a littafinsa mai suna: “Maganin Farir Jini Da Mallaka” wanda aka fassara shi da Larabci ya lissafa ƙa’i’dojin zaman Lafiya tsakanin miji da mata, ga su a dunƙule kamar haka:

    1. Ki guji saurin fushi da muskilanci da kuma nunƙufurci. Yawancin mata da zarar miji ya dawo sai su haɗe fuska, babu sauran walwala, sai kaushin magana da galatsi. Waɗansu mazan ma haka suke in sun shiga gida, sai fushi da ɓacin rai, kamar ‘yan wuta, amma da sun fita waje sai ka ga murna kamar suna aljanna. Domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a rayuwar aure, ya kamata kowa ya ajiye makamin a sakarwa juna fuska.

    2. Ku yi ƙoƙarin fahimtar halayen juna. In ka san halın mutum, shi ke nan ka ci maganin zama da shi, Ka da ka ce a dare ɗaya za ka canja halayen matarka, waɗanda ba ka so, ke ma ki ƙyale shi ya rayu yadda yake. Canjin hali sai a hankali. Kai a gaskiya mai wani halin zanen dutse ne, babu abin da zai iya kankare shi, to kuwa tun da haka ne, ai kowa sai dai a zauna da shi da halinsa.

    3. idan wani sabani ya faru tsakanin miji da mata, bai kamata a zargi juna ko faɗa ba a gaban yara, ko waɗansu baƙi. Wato bai kamata ka balbale matarka ko ki fada wa mijinki da mita ba, a gaban ‘ya’yanku ko waɗansu baki, ko da kuwa iyaye ne ko ‘yan uwa. A maimako haka, sai ku zauna bayan kowa ya huce ku sasanta da junanku.

    Wannan shi ma tushe ne babba na zaman lafiya.

    4. Duk mutum yana son in ya yi abin kirki a nuna ya yi, kuma a yaba masa, wannan sai ya ƙara masa ƙarfin gwuiwa, ya ninka abin da ya yi, ballantana mace, wacce take da ɗabi’ar son yabo da koɗa kai, koda kuwa kan ƙarya ne. saboda haka yayin da ka ga ta caɓa ado ko ta tsantsara girki to ya kamata ko yaya ka furta kalmomin yabo. Haka ke ma uwargida bai kamata ki mayar da mijinki kamar bawa ba, ko wanda kika baiwa ajiya, ko mai ya kawo ki karɓe ki yi shiru ba na gode, sai kuma in ba a yi ba ki ɗau fushi, yin haka ƙidahumanci ne da toshewar basira.

    5. Wani muhimmin abu mai tabbatar da zaman lafiya tsakanin ma’aurata shi ne, nuna farin ciki lokacin farin cikin abokin zama, kamar bikin ‘yar uwarta ko ƙawarta ko kuma na ‘yan uwan miji, kai ko bikinsa na ƙarin aure. Saboda idan ɗaya ya yi fushi yayin ɗayan yake farin ciki, lallai kam ba zaman lafiya. Saboda haka yana da kyau miji da mata su taya junansu murnar ko baƙin cikin abin da ya samu ɗayansu.

    6. Ya kai mai gida kasance mai hikima wajen nuna wa matarka kuskuranta. Misali idan ka ce ta kawo maka ruwa, sai ta tsaya wani wuni-wuni kuma ba wani aiki ne ya ɗauke ma ta hankali ba; to kawai ta gan ka a bakin rijiya ko famfo ka ɗebo ruwanka.

    Ko kuma ba ta shara da wuri, kai kuma ba ka son ganin wurin kaca-kaca, to tunda sanyin safiya ka ɗau tsintsiya ka kama shara, shi kenan, ka huta da ɓacin rai, ita kuma in dai mai hankali ce, sai ka ga ta gyara halinta. Ka daure ka gwada wannan maganin akwai huce haushi sosai a cikin sa.

    7. Akwai littattafai da dama da aka rubutu waɗanda suke bayanin rayuwar aure musamman ga waɗanda ba su taɓa yi ba. To me zai hana ka karanta ɗaya daga cikin waɗannan littattafan da kai da matarka domin kanku ya waye, ku fita daga duhun jahilci da ƙidahumanci. Saboda bincike ya nuna yawancin rigıngimu tsakanin ango da amarya jahilci ne yake haifar da su.

    Waɗannan ƙa’i’doji guda bakwai, suna da matuƙar amfani ga wanda ya yi aiki da su; wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin ma’aurata.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Mene Ne Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Cin Mutuncin Mutane Da Sunan Hamayyar Siyasa. danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali; wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Wasu Birane Da Garuruwa Da Makarantu Da KumaTsangayu A Arewacin Najeriya

    Wasu Birane Da Garuruwa Da Makarantu Da KumaTsangayu A Arewacin Najeriya

    Akwai wasu al’amura da ke jawo karkatar makaranta ko masu neman karatun Alƙur’ani zuwa wasu larduna ko biranen fiye da karkatarsu ga wasu lardunan ko biranen.

    Ƙaura daga wuri zuwu wani Wurin daban, abu ne da aka san makarantan tsangaya da shi, tun kaka da kakanni. Da yawa za ka ga Wata tsangaya cike da gardawa ko almajirai a lokacin rani; amma da zarar damina ta sauka sai ka neme su ka rasa. Irin wannan na faruwa ne saboda noma da aikin gona don samun ishasshen abinci.

    A wani lokaci kuma, makaranci kan yi ƙaura da almajiransa ko kuma gardi a karan kansa, idan ya sami labarin wata tsangaya mai tashen tara makaranta; ko kuma labarin wani mashahurin alaramma mai baiwa don ya fa’idanta daga baiwar da yake da ita. Yanayin wuri da ni’imarsa ko yalwar ruwa da wadatar ƙasar noma shi ma wani dalili ne da ke jawo taruwar makaranta.

    Irin wannan al’ada ita ake kira yawon bundi a wasu sassa na Arewacin Najeriya, musamman ma Sakkwato da kewayenta. Don ƙarin haske game da asalin wannan al’ada, sai a duba Babi na Huɗu cikin Sashe na Biyu kan ɗabi’un makaranta da halayensu cikin zamantakewar tsangaya.

    Wata tsohuwar al’ada tsakanin makarantan Arewacin Najeriya ita ce, tafiya Gabas, ma’ana ƙasar Barno don samun karatu. Don haka ne ma zai yi wuya ka sami wani makaranci a faɗin wannan nahiya ta Arewa; wanda bai dangana da Barno ko kewayenta ba ya yin neman karatu. Wannan na komawa ga irin rigayen da Kanem Barno ke da shi wajen karɓar Musulunci da tsohowar alaƙar wannan daula; da ƙasshen Larabawa, ƙarnuka masu yawa da suka shuɗe.

    Ƙasar Barno ta zamo tamkar wata Ka’aba ce ga manema Alƙur’ani. Makaranta, a bisa ɗabi’arsu, sun fi son wurin da za su keɓance kansu nesa da jama’a; kodayake buƙatun rayuwa na yau da kullum musamman buƙatar abinci ya jawo yawaitar almajirai da makaranta cikin birane da garuruwa masu cigaban kasuwanci da tashoshin mota da kasuwanni.

    Za mu iya ayyana wasu garuruwa da suka yi fice tuntuni da tara makaranata a Arewacin Najeriya kamar haka:

    – Ngazargamu
    – Gaidam
    – Gashuwa
    – Gubuci
    – NGuru
    – Damaturu
    – Takai
    – Bama
    – Ganjarma
    – Birniwa
    – Kebberi
    – Hadejiya
    – Kondiga
    – Paki
    – Kahutu
    – Hunƙuyi
    – Matazu
    – Tsakuwa
    – Maƙarfi
    – Kura
    – Zangon Daura
    – Ningi
    – Bunkure
    – Illela a Nijar
    – Kance a Nijar
    – Mutame a Nijar
    – Insharuwa da dai sauransu.

    Abu ne mai matuƙar muhimmanci sanin yawan tsangayunmu na Alƙur’ani, da yawan malamansu da almajiransu. Wannan ya sa tsohowar gwamnatin jihohin Arewa ƙarƙashin jagorancin Marigayi Sir Ahmadu Bello; Sardaunan Sakkwato ta aiwatar da wannan ƙididdiga a Makarantun Alƙur’ani Bisa ƙididdigar Gwamnatin Arewacin Najeriya (1960)

    Domin karanta cikakken bayani a kan Gudunmawar Tsangayun Alƙur’ani Wajen Cigaban Al’umma danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Mutane Biyar Da Suka Yi kama Da Manzon Allah (S.A.W) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Zuwan Tajwidi Da Musabaƙa Da Tasirinsa Cikin Tsarin Tsangaya

    Zuwan Tajwidi Da Musabaƙa Da Tasirinsa Cikin Tsarin Tsangaya

    Tajwidi dai ba sabon al’amari ba ne wajen ma’abota tsangaya, domin kuwa, makaranta da yawa a Maiduguri da Kano sun karɓe shi, kuma sun koye shi tun farko-farkon ƙarni na goma sha tara.

    Misali a nan shi ne, Malam Rabi’u Ɗantinki da Malam Ɗankwandarai, waɗanda duka alamajirai ne wajen mashahurin masanin ilmin Tajwidi da ƙira’o’in nan, watau Gwani Hamad.

    Hakan kuwa ya yi tasiri da gaske wajen kyautata karatun Alƙur’ani a Kano. A Maiduguri kuwa za mu ga cewa, al’amarin Tajwidi da ilmin ƙira’o’i ya ƙara bunƙasa ne bayan zuwan wasu malamai daga ƙasar Chadi, waɗanda suka yi karatu a wurin Shehun Azahar da ke ƙasar Masar. Waɗannan sun haɗa da Sheikh Daha da kuma Sheikh Hassan bn Umar Almuƙuri.

    Duk da wannan alaƙa tsakanin ma’abota tsangaya da Tajwidi tun kimanin shekaru tamanin baya; Tajwidi da ilmin ƙira’a bai yaɗu ya yi tasiri ba, sai bayan zuwan Musabaƙa. A nan ne makaranta masu tilawa mai ƙarfi daga tsangaya; suka riƙa koyon Tajwidi suna yin fice a musabaƙar cikin gida da ma duniya baki ɗaya.

    Babu shakka, hakan ya zama sababin tsundumar makaranta fagen neman ilmin fannin Musulunci; wasu ma suka fara danganawa da jami’o’in gida da ma wajen Najeriya, Fitaccen kwatance a nan shi ne Sheikh Ja’afar Mahmud Adam; wanda asalin karatunsa tsangaya ce.

    Daga bisani kuma, har ya dangana da Jami’o’in Musulunci da ke Madina da Sudan; don samun digiri na farko da na biyu wato Majistera. A halin yanzu kuma yana ƙoƙarin yin digiri na uku (Doctorate).

    Malam Ja’afar a yau ɗaya ne daga fitattun malamai, ba a Kano kawai ba, har ma Najeriya gaba ɗayanta. Baya ga ɗaiɗaikun makarantan da suka faɗa wasu fannoni a sababin Tajwidi da Musabaƙa; da yawan tsangayu a Maiduguri da Kano da kewayensu, sun buɗe ɓangaren Tajwidi wanda aka fi sani da ɓangaren Tahfeez. Babban misali a nan shi ne, Gwani Saleh Ɗanzarga Tahfeez da ke Kano; da kuma Tahfeez ta Sheikh Ghibirima; wadda ake kira Institute for the Memorisation of the Holy Qur’an Nguru.

    Duk da irin wannan tasiri da Tajwidi da Musabaƙa suka yi ga tsarin tsangaya a Arewacin Najeriya; har yanzu mafi yawan tsangayu da makaranta suna kan tsohon tsarin karatu bisa ƙarin harshenmu na gargajiya.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ma’anar Tsangaya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ma’anar Waƙafi danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Gudunmawar Tsangayun Alƙur’ani Wajen Cigaban Al’umma

    Gudunmawar Tsangayun Alƙur’ani Wajen Cigaban Al’umma

    Za mu iya cewa tsangayun Alƙur’ani da cibiyoyin ilmin Addinin Musulunci su ne tushen wayewa a wannan nahiya ta Afrika; wadda al’ummar duniya ke kallo a matsayin koma baya (har ana yi mata laƙabi da “Dark Continent” – Turawa, irin su Captain Hugh Clapperton da Major Dixam Denham da Dr. Waller Oudney; da Richard Lander ganau ne su, ba jiyau ba.

    Domin kuwa a lokacin da suka fara shigowa Wannan nahiya (Niger-area) a 1820 sun ga bambanci a bayyane tsakanin al’ummar Musulmi, idan aka kwatanta mu da mutanen Kudanci masu tafiya cikin tsiraici da rayuwa mai kama da rayuwar dabbobi. Domin kuwa sun tarar da cibiyoyin ilmi a tsangayu sama da dubu ashirin (20,000) a Arewacin Najeriya, ga Cikakken tsarin shugabanci da zamantakewa, ga mu da kotuna da wasiƙun hulɗar jakadanci da Larabci da Ajami da Limamai da masana daban-daban. Babban abin alfaharin Arewacin Najeriya a yau shi ne, zai yi wuya a haifi yaro ya girma ya balaga ba tare da ya dangana da makarantar allo ba.

    Tsangayun Alƙur’ani ba su gushe suna bayar da gudunmawa wajen cigaban al’ummar Najeriya ba; har sai da ta kai ta kawo cewa, idan ta fuskar noma da kasuwanci ne, to ana cin arziki da ƙwazo da himmar ma’abota tsangaya. Alal misali, tun kafin a samu man fetur a Najeriya; tattalin arzikinmu ya ta’allaƙa ne kan noman auduga da gyaɗa da sauransu. Kuma mun san irin yadda makarantan tsangayu suka yi fice wajen noma da gogayya da masu sayan gyaɗa da auduga tun a wancan lokaci.

    Ta fuskar kasuwanci kuwa, tsangayun Alƙur’ani sun shahara wajen yaye gardawa da matasa masu kishin kai da neman na kansu. Babban misali a nan shi ne irin hulunan Zanna Bukar da aikin Kwaɗo-da-linzami da Asake da ‘yan tsangaya ke yi. Waɗanda sun sami matuƙar karɓuwa, har ana safarar su zuwa wasu ƙasashe da ke Afrika ta Yamma.

    Cinikayya kuwa ba ta yiwuwa sai da kyakkyawar tarbiyyar ruhi da amana.

    Wannan ya sa irin almajiran da tsangayun Alƙur’ani suka yaye su suka mamaye kasuwanninmu na Kwari da Dawanau da Sabon Gari da sauransu. Rashin irin wannan tarbiya ta sanya ‘yan makarantun boko manya kamar jami’o’i ba sa iya gogayya a fagen kasuwanci. Dalili a nan kuwa shi ne, su sun fi so su ci da biro cikin ofisoshi.

    An ce kusan cikin kowaɗanne ‘yan kasuwa goma da ke Kasuwar Kwari; za ka iske fiye da biyar (5) asalinsu almajiran tsangaya ne. Cikin waɗanda suka yi fice akwai Alaramma Alhaji Malam Ibrahim Tal’udu; da Alhaji Rabi’u Mai Shadda da Alhaji Ahmadu Kofa da Malam Sa’idu. Idan kuwa muna zancen odar kaya daga ƙasashen waje ne ko mallakar kamfanoni ne; to ‘yan tsangaya irin su Alhaji Is’haƙa Rabi’u ba sa buƙatar sharhi.

    A taƙaice dai, tsangaya na tarbiyyantar ‘ya’yanta kan dogaro da kai komai ƙanƙantarsa. Shi ya sa ba za ka taɓa jin labarin ɗanta ɗaya ya gudu da kayan ‘yan’uwa cikin tsangaya ba; ko kuma a ce alarammomi sun yi yajin aiki don ba albashi.

    Amma ina iyakar adadin ‘ya’yan da boko ta yaye da suka wawashe kuɗaɗen ma’aikatunsu; ko na jihohinsu ko ma na ƙasar baki ɗaya?

    Daga ƙarshe, kada mu manta rawar da makaranta AIƙur’ani ke takawa wajen suturta kowannenmu in ya riga mu gidan gaskiya; da ɗaurin aure da raɗin suna da sulhu tsakanin Al’umma, ga uwa-uba; jagorancin Salloli da kuma yin addu’o’in zaman lafiya da koyar da Alƙur’ani ga ƙananan yara da manya dare da rana.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Zuwan Tajwidi Da Musabaƙa Da Tasirinsa Cikin Tsarin Tsangaya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sahabban Da Suka Fi Kowa Rawaito Hadisai danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.