Tag: ilimi

  • Yadda Ake Tahiyya

    Yadda Ake Tahiyya

    Attahiyyaatu lil-laahi was salawaatu waɗɗayyibaatu, assalaamu alaika ayyuhan nabiiyu wa rahmatul-laahi wabarakaatuhu, assalaamu alaina wa alaa idadil-laahis saalihiina. Ashhadu an laa ilaaha illallaahu, wa Ashhadu anna Muhammadan abduhu warasuulahu”.

    {Dukkan nau’in ban girma ya tabbata ga Allah, da kuma salloli da kyawawan kalmomi. Aminci ya tabbata gare ka ya Annabi. Da rahamar Allah da albarkatunsa. Aminci ya tabbata gare mu, da kuma ga bayin Allah salihai. Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasalam) bawansa ne kuma Manzonsa ne}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Salati Ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Bayan Tahiyya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sallar Kisfewar Rana Da Wata (Zazzaɓin Rana Da Wata) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa;id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’ar Sujjadar Tilawar Alƙur’ani

    Addu’ar Sujjadar Tilawar Alƙur’ani

    “Sujada wajhii lillazii khalaƙahu wa shaƙƙa sam’ahu wa basarahu bi haulihi wa ƙuwwatihi (Fatabaarakal-laahu ahsanul khaaliƙiina)”.

    {Fuskata ta yi sujada ga wanda ya halicce ta, kuma ya tsaga ji da gani a gare ta; da iyawarsa da kuma ƙarfinsa. (Allah mafi gwanintar masu halitta, ya girma, kuma alherinsa ya yawaita}.

    “Allaahummaktub lii bihaa indaka ajran, wa dha’a annii bihaa wizran waj’ilha lii indaka zukhran, wa taƙabbalhaa minni kamaa taƙabbaltahaa min abdika Dawuda”.

    {Ya Allah! Ka rubuta mini lada saboda ita (sujadar), ka kankare min zunubi saboda ita; ka sanya ta ta zamo taskar arziki gare ni a wajen ka, kuma ka karɓe ta daga gare ni kamar yadda ka karɓe ta daga bawanka Dawuda}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tahiyya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tafiya Sujudah danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’ar Wanda Ya Yi Sabon Aure, Ko Ya Sayi Abin Hawa

    Addu’ar Wanda Ya Yi Sabon Aure, Ko Ya Sayi Abin Hawa

    Idan ɗayanku ya auri mace, ko ya sayi bawa mai hidima, to ya ce:-

    Allaahumma innii as’aluka khairahaa wa khaira maa jabaltahaa alaihi, wa a’uzu bika min sharrihaa wa sharri maa jabaltahaa alaihi“.

    {Ya Allah! Ina roƙon ka alherinta da alherin da ka ɗabi’antar da ita a kansa; kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin da ka ɗabi’antar da ita a kansa}.

    Idan kuma ya sayi raƙumi, to ya kama tozon raƙumin ya faɗi kwatankwacin wannan (addu’ar).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’a Idan Mutum Ya Yi Fushi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Sakamakon Zalunci Yake danna nan.

  • Addu’ar Wanda Ya Yi Atishawa

    Addu’ar Wanda Ya Yi Atishawa

    Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce: Idan ɗayanku ya yi atishawa to ya ce:

    Alhamdu lillaahi“. {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah}.

    Ɗan uwansa kuma ko wanda yake zaune tare da shi ya ce masa:-

    Yarhamukal laahu“. {Allah ya ji ƙanka}.

    Idan ya gaya masa haka, shi kuma ya ce masa:-

    Yahdiikumul laahu wa yulihu baalakum“. {Allah ya shirye ku, Ya kyautata halinku}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abin Da Ya Kamata Mai Yin Sallah Ya Yi Bayan Ya Tafi Sujudah danna nan.

  • Dangantakar Harshe da Waƙa

    Dangantakar Harshe da Waƙa

    Harshe da Waƙa – Harshe wani muhimmin sinadari ne wanda al’umma take bayyana al’adunta da hali na zamantakewarta. Mutane a ɗaiɗaya ko a rukuni ko a ƙungiya na isar da muradansu a rayuwa ta hanyar harshe.

    Idan aka dubi kowace irin al’umma ko ƙabila za a ga tana da harshe nata; wanda take amfani da shi a matsayin harshen sadarwa.

    Harshen Hausa, harshe ne wanda yake sarrafa ƙwayoyin sauti cikin gaɓoɓi da kalmomi da jumloli; ya shirya magana wadda za ta ƙunshi wata ma’ana ko saƙo; wadda idan an sadar da ita, mai sauraro yake ji, ya fahimta.

    Ɗantumbushi (2012: 37); ya nuna harshen Hausa yana girma da ɗaukaka da faɗaɗuwa a cikin shuɗewar lokuta. Wannan harshe na Hausa yana kuma da karuruwa (Ɗantumbushi, 1998 & 2004; Amfani, 2011), musamman yana da karin gabas da karin yamma; waɗanda sukan sami bambanci ta hanyar sauti da kalmomi da siga ko tsari na gina jumloli da sauran wasu sassa na nahawu.

    Karuruwan Hausa

    Karin Gabaci Karin Yammaci

    Kananci – Sakkwatanci
    Dauranci – Garewanci
    Zazzaganci – Katsinanci
    Bausanci – Gobiranci
    Gudduranci Kurfayanci
    Zamfaranci
    Arewanci

    Makaɗin Hausa ya ɗauki harshen Hausa abokin hulɗa, ta haka harshen ya zama mai tagomashi a gare shi; wanda yake aiki da shi a kowane lokaci ba tare da wata tankiya ba. Makaɗi yakan iya fyauce hankali da tunanin mutum a yayin da ya sarrafa harshe bisa tsari da yanayi na waƙar baka. Harshe yakan haɗa hulɗa tsakanin makaɗa da jama’a ba dangi na iya ko na baba.

    Alan waƙa ya amince da harshen waƙa, harshe ne mai shigar kutse a cikin zukatan jama’a. Ga abin da ya ce:

    Jagora : Hikkima ba ruhi ko jiki ba hangena,
    : Ba aibn kallo ko ɗauki duba tuna,
    : Hikkima ba Rauhanai ka bai ba dangina,
    : Hikkima Ilhamiyya nake karatuna,
    : Jakadiyata waƙa mai tafi da saƙona,
    : Jakadiyata ba ƙwuya a aika saƙona.

    Makaɗan baka sukan yi amfani da harshe a bisa wasu mabambantan halaye. Harshe yakan zama zubi na mutum, makaɗi; tun ma ba idan aka yi la’akari da yadda tunani yake ginuwa a ɗayan-ɗayan mutane ba. Haka kuma nauyin ilimi da yin nutso a falsafa da fasaha; da wayewa kan sanya hanyoyin amfani da harshe a wajen makaɗa su bambanta (Alhassan, 2012: 128).

    A lokacin da makaɗi ko mawaƙi yake shiryawa da aiwatar da waƙa shi yake da mulki da harshe; baiwa da azanci da zalaƙa suna yi wa mai waƙa, makaɗi, jagora a zubi na waƙa (Yahaya, 2012: 233).

    Kila wannan harshe na waƙa mai kaifafa ma’ana ya sanya waƙa take saurin isar da saƙo; da fitar da ma’ana a cikin kalmomi ƙalilan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Gudumawar Waƙoƙin Baka na Situdiyo Wajen Haɓaka Tattalin Arziki danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yabon Gusau A Waƙoƙin Baka danna nan.

    Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Waiwaye Kan Harshen Makaɗi A Zubin Waƙar Baka; wanda Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Addu’a Idan Mutum Ya Yi Fushi

    Addu’a Idan Mutum Ya Yi Fushi

    A’uzu bil laahi minas Shaiɗaanir rajiimi”.

    {Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan tsinanne}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Wanda Ya Yi Sabon Aure, Ko Ya Sayi Abin Hawa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ma’anar Aure A Ƙasar Hausa danna nan

  • Haƙƙoƙin Shugabanni A Kan Mabiyansu

    Haƙƙoƙin Shugabanni A Kan Mabiyansu

    Haƙƙoƙin Shugabanni – Kamar yadda iyaye suke da haƙƙoƙi a kan ‘ya’yansu; haka su ma Shugabanni suke da haƙƙi a kan mabiyansu; kai haƙƙoƙin shugabanni sun ma fi na iyaye nauyi da cancantar a kula da su, saboda su iyaye ‘ya’yansu kaɗai suke kula da su; amma su shugabanni gaba ɗayan al’umma suke kula da su.

    Illolin saɓa wa iyaye ba sa yin naso mai yawa ta yadda zai shafi kowa; amma musibar da take biyo bayan saɓa wa shugabanni da yi musu tawaye; babu wanda ba ta shafa ba.

    Haƙƙoƙin shugabanni a kan mabiya a taƙaice;

    1. Yi wa shugabanni biyayya a fili da ɓoye, sai dai in sun yi umarni da a saɓa wa Allah; ko kuma sun hana a bi Allah, to a nan ba za a bi su ba.

    2. Yi musu nasiha da ba su shawarwari na gari; a fili da ɓoye tare da girmamawa da tausasawa da kuma mutuntawa. Ba tare da aibatawa ko suka ko zagi ko gallazawa ba.

    3. Taimaka musu da ƙarfafar su da goya musu baya; saboda ƙarfinsu ƙarfin Musulunci ne; rauninsu rauni ne ga Musulunci da musulmai. Kada a soma mara wa ‘yan adawa baya don a cutar da shugaba. Ko a hana ko a lalata wani aikin alhairi da yake yi ko kuma yake yunƙurin aikatawa.

    4. Girmama shi da mutunta shi, da ba shi matsayinsa a fili da ɓoye

    5. Faɗakar da shi da sanar da shi duk abinda zai kawo gyara da maslahar al’umma; ka da a yi ƙwauron magana; amma a iya a cikin ladabi da girmamawa. Haka zalika da nusar da shi kurakuransa, domin ya gyara duk wannan a yi a cikin girmamawa da tausayawa.

    6. Ba shi kariya gwargwadon ikon daga sharrin maƙiyansa; da masu yi masa hassada da sanar da shi ƙulle-ƙulle da makirce-makircen da suke shiryawa.

    7. Taimaka masa da goya masa baya domin ya sauke nauyin da yake kansa.

    8. Wayar da kan ‘yan adawa da maƙiyansa da fanɗararru domin su fahimce shi; su daina adawar da kangarar da suke yi masa.

    9. Taimakon sa da dukiyarka da harshenka da matsayin ka da jikinka; da duk abin da za ka iya a fili da ɓoye.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Ƙasar Hausa danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Za su Taimaka wa Mutum Wajen Tsara Lokacinsa danna nan

  • Sahihin Sirrin Ƙulhuwallahu Ahad

    Sahihin Sirrin Ƙulhuwallahu Ahad

    Sirrin Ƙulhuwallahu Ahad – Suratul Ikhlas; ita ce sura ta (112) a jerin surorin Alƙur’ani mai girma, a wasu lokutan ana kiran ta da Ƙulhuwallahu Ahad, wato ana ambaton ta da ayar farko da ta fara da ita.

    Wannan sura mai albarka, tana cikin surorin da aka saukar a Makka, kuma ayoyinta (4) ne; kamar haka:

    Bismillahir Rahmanur Rahim
    Ƙulhuwallahu ahad(1), allahusamad(2), lamyalid walamyulad(3), walamyakullahu ƙufuwan ahad(4).
    Ka ce: shi Allah ɗaya ne (tak)(1). Allah wanda ake nufa da buƙata(2). Bai haifa, kuma ba a haife shi ba(3). Kuma babu wani wanda ya yi daidai da shi(4).

    An saukar da wannan sura ne don tabbatar da:

    1. Ɗayantakar Allah ta zati da siffa da kuma aiki.
    2. Sanar da bayi wadatuwar Allah daga komai, tare da buƙatuwar komai zuwa ga falalarsa da jinƙansa.
    3. Rushe aƙidar danganta wa Allah uba ko kuma ɗa.
    4. Kore daidaita wani bawa da Allah.

    Domin Karanta cikakken bayani a kan Falalar Ƙulhuwallahu Ahad danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tafiya Sujudah danna nan.

    FALALARTA: 

    An karɓo hadisi daga Abu Sa’idil khudri Allah ya yarda da shi ya ce: Ɗan ‘uwana Ƙatada ɗan Nu’uman ya ce: 

    Haƙiƙa wani mutum ya yi tsayuwar dare a lokacin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam), sai ya yi ta karanta ƙulhuwallahu Ahad (Bayan Fatiha), bai ƙara wata sura ba, da gari ya waye sai ya zo wajen Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ambata masa tsayuwar daren da ya yi da ƙulhuwallahu Ahad, yana ganin kamar surar ta yi kaɗan. 

    Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: 

    “Na rantse da wanda raina yake hannunsa tabbas tana daidai da ɗaya bisa uku (1/3) na Alƙaur’ani”. (Wato wajen samun lada). Bukhari ne ya rawaito shi. 

    Kuma an Karɓo daga Anas ɗan Malik, Allah ya yarda da shi ya ce: Ya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ina matuƙar son wannan sura: “Ƙulhuwallahu Ahad”. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “son da kake yi mata ya shigar da kai Aljanna”. Tirmizi da Ibn Hibban ne suka rawaito shi. 

    Sannan an karɓo wani hadisin daga Buraida ɗan Husayyib Allah ya yarda da shi ya ce: “Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ji wani mutum yana cewa: 

    “Ya Allah ina roƙon ka, ina mai tabbatar da na shaida tabbas kai kaɗai ne abin bauta, babu wani abin bautawa (na gaskiya) sai kai kaɗai, ɗayan da ake nufa da buƙata, wanda bai haifa ba, kuma ba a haife shi ba, kuma babu wani wanda ya yi daidai da shi”. 

    Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Tabbas ka roƙi Allah da sunansa wanda in har aka roƙe shi, to zai bayar da abinda aka roƙa, kuma idan aka kira shi da shi, to zai amsa”. Imam Ahmad, Abu Dawud, Tirmizi da wasunsu ne suka rawaito shi.

    Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

    MUHIMMANCIN ƘULHUWALLAHU AHAD DA BAYANIN GURAREN DA MANZON ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) YAKE KARANTA TA: 

    Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi umarni da karanta ƙulhuwallahu Ahad, kuma shi ma ya kasance yana 

    karanta ta a gurare daban-daban, saboda muhimmancin da take da shi. 

    1. Ya yi umarni a karanta ta bayan idar da sallar Farilla, kamar yadda Abu Dawud Tirmizi, Nasa’i da wasunsu suka rawaito daga Uƙbatu ɗan Amir, Allah ya yarda da shi. 
    2. Manzo (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana karanta ta a wuturin sallar dare da yake yi. Kamar yadda Imamul Nasa’i, da waninsa suka rawaito. 3. Kuma yana karanta ta a raka’a ta biyu ta nafilar da yake yi kafin Sallar Asuba (Wato Raka’atal Fajri), kamar yadda Imam Muslim ya rawaito. 
    3. Sannan kuma yana karanta ta a raka’a ta biyu bayan kammala ɗawafi. Muslim ya rawaito. 
    4. Sai kuma a raka’a ta biyu ta bayan sallar Magariba. Tirmizi ya rawaito. 6. Kafin kwanciya bacci yana karanta ta tare da Falaƙi da Nasi ya shafe jikinsa sau uku. Bukhari ya rawaito. 
    5. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce wanda ya karanta ƙulhuwallahu Ahad sau goma (10), Allah zai gina masa ƙerarren gida a Aljanna. Ahmad da wasunsu ne suka rawaito. 

    Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

    To ‘yan uwa Musulmai, duk mai son ya ribaci alhairan da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da sahabbansa suka ribata daga wannan sura ta ƙulhuwallahu Ahad, to ya yi koyi wajen yin amfani da ita a guraren da suka yi amfani da ita , Allah dai ya ce idan har muka bi Manzo za mu shiriya. Duba suratul Nur, aya ta (54).

    Ya ‘yan uwa Musulmai ku sani cewar da ake yi a rubuta ƙulhuwallahu sau ɗari kaza da sha kaza, na tsawon sati a riƙa wanke wa ana sha bai da asali, domin kuwa ba koyarwar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ba ce. 

    Kuma babu wata madogara ingantacciya game da cewa ayi laya da ƙulhuwallahu Ahad a saka a kwalaba a binne a kusurwoyin gida ko ofis ko rumfar kasuwa a matsayin maganin sata. Da sauran abubuwa makamantan waɗannan marasa dalili, don haka, mu lura da kyau mu yi hattara mu sani ɓata ba zai taɓa yin daidai da shiriya ba. 

    Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

  • Halaye Da Siffofin Shugaba Nagari

    Halaye Da Siffofin Shugaba Nagari

    Shugaba Nagari – Ya kamata kowane Shugaba daga sama har ƙasa ya sifantu da waɗannan halaye:

    1) Adalci shine tushen samun nasarar kowane Shugabanci adalcin Allah Ta’ala shi ne yake riƙe da sammai da ƙassai; da duk wanda yake ƙarƙashinsa yake bai wa kowa haƙƙinsa babu nuna wani bambanci.

    Amr ibnul As Radiyallahu anhu yana cewa; mulki ba ya yiwu wa sai da tsayayyun jami’ai, su kuma ba za su samu ba sai da kuɗi, kuɗi kuma ba ya samuwa sai ana raya ƙasa, raya ƙasa ba ya yiwuwa sai da adalci.
    Yana daga adalci shugaba ya hana azzalumai zalunci yana hana maɓarnata ɓarna, kada ma ya bari sai talakawa sun fara kokawa, saboda in har aka kai matsayin da suka fara kokawa to za su iya ɗaukar doka a hannunsu.

    2) Lallai ne shugaba ya kasance mai nisantar zubar da jinin mutane kada ya yi kada ya bari a yi.

    3) ya kasance mai magana ɗaya babu ƙarya babu yaudara.

    4) ya zauna lafiya da mutanen kirki masu tsoron Allah; kada ya saki fuska ga azzalumai da ashararai kada su samu sakewa a ƙarƙashin ikonsa.

    5) Shugaba ya kasance mai cika alƙawari mai faɗar gaskiya in ya san ba zai yi ba; kada ya ce zaiyi, kada kuma bai yi ba ya ce ya yi.

    6) Kada ya raina abokin gaba komai rauninsa ya yi masa maka ido.

    7) Lallai ne ya sami likita na musamman ƙwararre mai amana masoyi na haƙiƙa; kuma kada ya dogara da likita guda ɗaya, a’a ya sami wadatattun likitoci waɗanda in wani gagarumin ciwo ya same shi za su haɗu a kansa in bakinsu ya zo ɗaya akan irin maganin da za’ayi masa to sai a yi bayan shawartar waɗansu amintattunsa keɓaɓɓu.

    8) ya bai wa mataimakinsa muhimmanci sosai, kada ya ture shi gefe guda ta yadda zai zama kamar ɗan kallo a harkar mulki; amma kuma kada ya bari ya sake ya miƙe ƙafa har ya fi shi ƙarfi ya zama kamar shine shugaban shi kuma ya zama hoto.

    9) Haka kuma ya samar da kyakkyawar jituwa tsakaninsa da ‘yan majalisarsa ya ringa zama dasu akai – akai yana shawartarsu kowa ya ji cewa ana yi da shi; babu ɗan mowa a cikinsu, babu kuma waɗansu fulogai waɗanda su kaɗai ne suke jan mai kuma in babu su babu inda za a je. Wannan zai haifarwa da shugaba babbar matsala.

    10) Shugaba ya kula da tattalin arziƙi sosai musamman sana’o’i da harkokin kasuwanci ya buɗawa mutane hanyoyin samun arziƙi da ayyukan yi musamman ga matasa; ya ringa tallafawa ‘yan kasuwa, kada ya ɗora musu haraji mai yawa ko ya basu bashi da kuɗin ruwa. Lalle ne shugaba ya kiyayi abin hannun mabiyansa. Ya guji karɓe- karɓe da cin hanci da rashawa.

    11) Ya kasance mai tattali da tsimi da tanadi da shirin ko- ta- kwana; musamman tanadin abinci da kayan masarufi saboda ba da agajin gaggawa a lokacin da wata musiba ta afko kwatsam ta; yadda ba sai an fita waje da ƙoƙon bara ba.

    12) Ya kasance mai alƙawari ya yi kyakkyawan sakamako ga duk wanda ya taimaka masa; musamman a lokacin da yake neman mulki. Kada su tura mota ta tashi ta bar su da hayaƙi.

    13) Kada ya bari wani talaka ya san wurin hutunsa da shaƙatawarsa ballantana ya je wurin; wannan zai janyo raini manyan mutane kaɗai zai bari su ringa halartar irin wannan wurin; in ya buƙaci zuwansu domin tattauna muhimman al’amari cikin nutsuwa.

    14) Ya yi ƙoƙarin aikata duk abinda zai jawo masa baƙin jini da maƙiya.

    15) Kada ya naɗa ‘yan uwansa a manyan muƙamai saboda gudun hassadar ‘yan uwa. Amma ya kai matuƙa wajen kyautata musu da mutunta su; sannan kuma ya sa ido a kansu ya yi kaffa – kaffa da su, ya yi haƙuri kan cutarwarsu.

    16) Lallai ne shugaba ya riƙe halaye guda uku;
    1. kyauta 2. Haƙuri 3. Da tabbatar da gaskiyar komai kafin ya ɗau mataki akansa.

    17) Ya ringa yabo da zargi daidai ƙurji daidai ruwa. Wato kada ya yi yabo fiye da ƙima kada ya yi ta zargi, faɗa, ko mita fiye da ƙima. Haka kuma ya daidaita tsakanin alƙawarurrukansa da barazanarsa. Kada barazana ta fi yawa, kada kuma alƙawari yafi rinjaye.

    18) Ya kasance mai halin ba-sani-ba- sabo duk wanda ya taka doka, doka ta taka shi.
    A dunƙule dai abubuwa uku ne suke tabbatar da nagartar mulki;
    1- Ɗaukaka da inganta addinin mutane
    2- Tabbatar da tsaro da zaman lafiya
    3- Inganta rayuwar al’umma.

    Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan 

  • Tushen Zaman Lafiya Da Hanyoyin Tabbatar Da Adalci

    Tushen Zaman Lafiya Da Hanyoyin Tabbatar Da Adalci

    Hanyoyin Tabbatar Da Adalci – Majaddid shaihuna Usman ɗan Fodiyo Allah ya ƙara rahama a gare shi; ya rubuta littafi mai suna; “Usulul adli liwalatil umuri wa ahlil fadli” – wato Ginshiƙan kafuwar adalci domin shugabanni da manyan mutane.

    A cikin wannan littafi, ya yi bayanin hanyoyi goma waɗanda in dai shugabanni daga sama har ƙasa za su yi bi su; babu makawa za su kasance masu adalci a shugabancinsu.

    A taƙaice ga waɗannan ginshiƙai na hanyoyin tabbatar da adalci;

    Tushe Na Ɗaya

    Shugaba ya san matsayi da darajar shugabanci da yake yi. Ya sani cewa shugabanci ni’ima ce babba; wacce in ya yi gaskiya da adalci za ta kai shi ga samun ni’ima madawwamiya a lahira da kyakkyawan suna a duniya. Idan kuwa aka samu akasi to zai gamu da matsananciyar azaba a duniya da lahira; saboda haka kada ya yi wasarere da shugabanci ya riƙe shi ƙam ƙam ya yi da gaske ba wasa.

    Tushe Na Biyu

    Lallai ne shugaba ya ja malamai masu tsoron Allah da aiki da iliminsu masu son alhairi ga al’umma masu faɗar gaskiya marasa tsoro marasa kwaɗayi, ya ja su a jikinsa ya rinƙa neman shawarwarinsu da fatawa akan al’amuran shugabancinsa; ya kuma rinƙa amfani da shawarwari da nasihohi da suke yi masa.

    Haka kuma ya nemi masana ƙwararru a kowane fanni na rayuwa kamar manyan ‘yan kasuwa; tsofaffin shugabanni, da ma’aikata na kowane ɓangare dattawan gari har ma da matasa maza da mata masu tsoron Allah da kishin ƙasa domin ya amfana da iliminsu da ƙwarewarsu a fannonin rayuwa da sauransu.

    Tushe Na Uku

    Kasancewarka mai gaskiya da riƙon amana da adalci ba zai kuɓutar da kai ba a wurin Allah; sai ka tabbatar mai ma’aikatanka da jami’an gwamnatinka suna da hali irin naka. Amma idan kana ganin ɓarna ka yi shiru; to haƙiƙa sai ka ba da amsa akan wannan ɓarnar; kuma sai an tuhume ka akan duk ɓarnar da akayi kana sane ka yi shiru ayi maka azaba a kanta ranar ƙiyama.

    Tushe Na Huɗu

    Lallai ne shugaba ya kasance mai yawan haƙuri; afuwa da kau da kai ya guji saurin fushi da yanke hukunci cikin ɓacin rai.

    Tushe Na Biyar

    A duk lokacin da za ka ɗauki wani matakai ko yanke hukunci ko shawara ko sanya hannu akan wani ƙudiri; waɗanda suke ƙarƙashinka ka ɗauki kanka a matsayin ɗaya daga cikin talakawa duk abinda ba za ka so a yi maka ba to kada ka yi wa waninka, duk abinda za ka so ayi maka to ka zartar da shi.

    Tushe Na Shida

    Kada ka wulaƙanta talaka da sauran mutane masu kawo buƙatunsu gare ka da koke – kokensu; saboda babban amfanin shugabanci shine sharewa mabiya hawayensu da sauran buƙatunsu da yin abinda ya kamata akansu.

    Tushe Na Bakwai

    Ka yi rayuwa matsakaiciya tare d tsantseni da wadatar zuci kada ka sabawa kanka da zurfafawa da al’mubazzaranci; a wajen jin daɗi da kece raini wannan zai sa ka mance da wahalhalun da talakawa suke ciki zuciyar ka ta bushe; in suna kuka ka rinƙa jin kamar kukan daɗi suke yi. Kana sheƙa dariya abinka.

    Tushe Na Takwas

    Dukannin abinda zai yiwu cikin sauƙi da lumana, kada ka bi hanyar tsanani ne da tursasawa wajen tabbatar da shi. Ana amfani da tsanani kawai a lokacin da sauƙi ba zai yi amfani ba.

    Tushe Na Tara

    A kowane lokaci ka rinƙa tunanin mutuwarka da kwanciyar ƙabari da tashin alƙiyama da musiba da azabobin da suke cikinta; da kuma ni’ima da rahamar da Allah ya tanada ga masu binsa. Ka rinƙa tunanin shin kai a wane ɓangare za ka kasance idan Allah ya tashi alƙiyama.

    Tushe Na Goma

    Ka sanya tsarin shugabanci na Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance madubinka, ma’aunin shugabancinka ka rinƙa kwaikwayonsa gwargwadon ikonka.

    Bayan waɗannan tuwassa goma waɗanda Shaihu Usman ɗan Fodiyo; ya ambata ya kuma ce imamul Gazzali ne ya faɗe su a cikin wani littafinsa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Halaye Da Siffofin Shugaba Nagari danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Raka’a Biyu Kafin Magariba danna nan