Tag: ilimi

  • Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci

    Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci

    Alhamdu lil laahil lazii aɗ’amanii hazaa wa razaƙaniihi min gairi haulin minnii walaa ƙuwwatin”.

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ciyar da ni wannan (abincin); ya azurta ni da shi, ba tare da wata dabara ko ƙarfi daga gare ni ba}.

    Allamdu lil laahi hamdan kasiiran ɗayyiban mubaarakan fiihi gaira makfiyyi walaa muwadda’in walaa mustagnan anhu Rabbunaa“.

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo mai yawa, kyakkyawa, kuma abin sanya albarka a cikin sa; (Allah) wanda ba a ɗauke masa azurta bayinsa, kuma ba a rabuwa da shi (a bar nema daga wurinsa), kuma ba a wadatuwa ga barinsa; shi ne Ubangijinmu}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Baƙo Ga Wanda Ya Gayyace Shi Cin Abinci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Cin Abincin Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Shiekh Sa’id Ibn Ali Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Ramuwar Azumin Ramadan

    Ramuwar Azumin Ramadan

    Ramuwar Azumin Ramadan – Dukkanin wanda Azumin watan Ramadana ya kubce masa bisa dalilai na Shari’a, ramuwa ta wajaba a kansa. Game da ramuwar kuwa, ga yadda abin yake:

    1. Ka sani ɗan’uwana, ramuwar azumin da ya kubce na Ramadan ba wajibi ba ne ramawa nan take, babu laifi a jinkirta; saboda abin da ya zo daga Nana A’isha (Radiyallahu Anha) cewa: “Yana kasancewa akwai ramuwar azumin Ramadan a kaina, ba na samun damar ramawa sai a watan Sha’aban”. (Bukhari 4/166, Muslim 1146).

    Alhafiz Ibn Hajar yana cewa: “A cikin wannan hadisi akwai dalili a kan halaccin jinkirta ramuwar azumin Ramadan kai tsaye ko da uzuri ko babu”.

    Abu ne sananne, babu shakka a kai cewa ramawa take ya fi ramawa da jinkiri, saboda shigar hakan ƙarƙashin ayoyin da suke nuna gaggawa zuwa ga ayyukan alheri da rashin nawa wajen gabatar da su. Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: “Ku yi gaggawa zuwa ga gafarar Ubangijinku”. (Aali Imram 133). Da fadin sa: “Waɗannan su ne masu gaggawa cikin alherai kuma masu rige-rige”. (Mu’uminun: 61).

    Ba wajibi ba ne a yi ramuwa a jere, saboda Allah ya ce: “A yi ramuwa cikin wasu kwanaki daban”. Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Babu laifi idan an rarraba”. Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Ya dinga yin sa mara idan ya ga dama”.

    2. Malamai sun yi ijma’i kan cewa wanda ya mutu ana bin sa salloli; waliyyinsa ba zai rama masa ba, haka ma waninsa. Haka ma wanda ya kasa azumi babu wanda zai yi masa; matuƙar yana raye sai ya ciyar kowacce rana miskini ɗaya kamar yadda Anas Bin Malik (Radiyallahu Anhu) ya aikata. Sai dai wanda ya mutu ana bin sa azumin bakance; to waliyyinsa zai rama masa dalilin faɗin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) inda ya ce; “Wanda ya mutu ana bin sa azumi, to waliyyinsa ya yi masa”. (Bukhari 4/168, Muslim 1147).

    Bukhari da Muslim sun fitar da wani hadisi daga Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) cewa; wani mutum ya zo wajen Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Ya Manzon Allah, Mahaifiyata ta rasu alhali ana bin ta bashin azumin wata guda, zan iya rama mata? Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Eh, bashin Allah shi ya fi cancanta da a biya”.

    Waɗannan hadisan gamammu ne a zahiri wajen halaccin waliyyi ya yi wa mamaci azumi gaba ɗayan nau’o’in azumin; kuma da wannan wasu malamai cikin Shafi’iyya da Ibn Hazm suka yi fatawa. Sai dai waɗannan hadisan za su iya shiga gamammen da ake keɓancewa; saboda waliyyi ba zai yi wa mamaci azumi ba sai na bakance. Da wannan Imam Ahmad Ibn Hambal ya ce; “Ba za a iya wa mamaci azumi ba sai na bakance”. Sai na ce masa; “To ya ya azumin Ramadan? Sai ya ce; “Sai ya ciyar kawai”. (Masa’il na Abu Dawud 96).

    Aiki da wannan fatawa shi ne daidai, kuma a nan dalili ke rinjaya; saboda cikinta akwai amfani da gaba ɗaya hadisan da suka zo ba tare da an ki karɓar ko ɗaya daga cikinsu ba, tare da fahimta ingantacciya, musamman hadisin farko; Nana A’isha (Radiyallahu Anha) ba ta fahimci cewa wannan izlaƙin ya game azumin Ramadan da waninsa ba, ita dai ta tafi kan cewa za a ciyar ne. Domin ita ce ta rawaito shi saboda abin da Amrata ta rawaito cewa; “Mahaifiyata ta rasu kuma ana bin ta azumin Ramadan, zan iya rama mata? Sai Nana A’isha ta ce; “A’a, kawai ki yi sadaka muhallin kowanne yini rabin sa’i ga kowane miskini”. (Mushkili Aathar na Zahawiy 3/142).

    Abdullahi Ibn Abbas shi ya rarrabe tsakanin azumin bakance da na Ramadan, domin yana ganin idan na bakance ne; za a rama, amma idan na Ramadan ne ciyarwa ta wadatar, kamar yadda ya ce; “Idan mutum ya yi rahin lafiya a watan Ramadan; sannan ya mutu ba tare da ya yi azumi ba, sai a ciyar masa ba sai an rama masa ba”. Amma idan bakance ne sai a rama masa.

    Abu ne a zahiri cewa Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu); shi ne ya rawaito hadisin da ya gabata, musamman ma kuma ya rawaito wani hadisi wanda a cikinsa akwai nassin cewa waliyyi ya yi wa mamaci azumin bakance, ya ce; “Sa’ad Bn Ubadata (Radiyallahu Anhu) ya tambayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) cewa: “Mahaifiyata ta rasu ana bin ta azumin bakance? Sai ya ce: “Ka rama mata shi”. (Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi).

    Wannan rarrabawar shi ne ya fi dacewa da ƙa’idojin shari’a da asalanta kamar yadda Babban Malami Ibn Ƙayyim ya bayyana cikin littafinsa “I’ilaamul Mauƙi’eena”; sannan ya ƙara bayani sosai a cikin littafinsa “Tahzeebi Sunani Abee Daawud”, mujalladi na 3, shafi na 279 – 282.

    3. Sannan wanda ya mutu ana bin sa bashin azumin bakance; to ya halasta mutane adadin kwanakin da ake bin sa su yi masa azumin. Hasanul Basri ya ce; “Idan mutane talatin suka yi wa mutum, kowane mutum ya yi na kwana ɗaya, ya isar masa”. Amma ciyarwa idan waliyyinsa ya tattara miskinai adadin kwanakin da ake bin sa ya ciyar da su ya halasta. Haka Anas Bn Malaik (Radiyallahu Anhu) ya aikata. Wallahu a’alam.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Kaffarar Azumin Ramadan danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ƙara Yawaita Ibadu Da Alhairi A Goman Ƙarshe Na Ramadan danna nan.

    Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Don karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Addu’ar Da Ake Yi Yayin Shigar Da Mamaci Ƙabari

    Addu’ar Da Ake Yi Yayin Shigar Da Mamaci Ƙabari

    Bismil laahi wa alaa sunnati Rasulil laahi

    {Da sunan Allah, kuma a kan sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam)}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Da Ake Yi Bayan An Binne Mamaci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sahihin Sirrin Ƙulhuwallahu Ahad danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; Wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yadda Ake Addu’ar Ta’aziyya

    Yadda Ake Addu’ar Ta’aziyya

    “Inna lil laahi maa akhaza, walahu maa a’aɗaa wa kullun shai’in anhu bi ajalin musammaa…..faltasbir wal tahtasibu”.

    {Haƙiƙa abin da Allah ya ɗauka nasa ne, kuma abin da ya bayar shi ma nasa ne, kuma kowane abu a wurinsa yana da ajali abin ambato…..sai ta yi haƙuri ta nemi lada (na haƙurin rashin da ta yi).

    Zai kuma iya cewa:

    A’azamal laahu ajraka wa ahsana azaa’aka wa gafara li mayyitika”.

    {Allah ya girmama ladanka, ya kyautata haƙurinka a kan abin da ka rasa, ya gafarta wa mamacinka}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Da Ake Yi Ga Mamaci A Cikin Sallar Jana’iza danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Sakamakon Zalunci Yake danna nan

    Wannan bayanin an ciro shine daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Addu’ar Da Ake Yi Ga Mamaci A Cikin Sallar Jana’iza

    Addu’ar Da Ake Yi Ga Mamaci A Cikin Sallar Jana’iza

    Addu’a Ga Mamaci – “Allaahummagfir lahu warhamhu, wa aafihi; wa afu anhu wa akrim nuzulahu wawassi’i mudkhalahu, wagsilhu bil maa’i wassalji wal baradi; wa naƙƙihi minal khaɗaayaa kamaa naƙƙaitas saubal abyadha minad danasi; wa abdilhu daaran khairan min daarihi wa ahlan khairan min ahlihi wa zaujal khairan min azabil ƙabri wa azabin naari”.

    Addu’a Ga Mamaci – {Ya Allah! Ka yi masa gafara, ka ji ƙansa, ka amintar da shi daga bala’i, ka yi masa rangwame; kuma ka girmama liyafarsa, ka yalwata mashigarsa (ƙabarinsa); kuma ka wanke laifuffukansa kamar yadda kake tsaftace farar tufa daga dauɗa, kuma ka musanya masa gidan da ya fi gidansa alheri; da mata da ta fi matarsa alheri, kuma ka shigar da shi Aljannah , ka tsirar da shi daga azabar kabari da azabar Wuta}.

    Allaahummagfir li hayyinaa wa mayyitinaa wa shaahidinaa, wa gaa’ibinaa, wa sagiirinaa wa kabiirinaa, wa zakarinaa wa unsanaa. Allaahumma man ahyaytahu minnaa fa’ahyihi alal Islaami waman tawaffaitahu minnaa fatawaffahu alal imani, Allaahumma laa tahrimnaa ajrahu walaa tadhillanaa ba’adahu”.

    {Ya Allah! Ka gafarta wa rayayyunmu da matattunmu, da waɗanda suke halarce tare da waɗanda ba sa nan; da yaranmu da manyanmu, da mazajenmu da matayenmu. Ya Allah! Wanda ka rayar da shi daga cikinmu, to ka rayar da shi a cikin Musulunci; wanda kuma ka ɗauki ransa, to ka ɗauki ransa a kan imani. Ya Allah! Kada ka haramta mana ladan (haƙurin rashinsa), kada kuma ka ɓatar da mu bayansa}.

    Allaahumma inna fulaana bin fulaanin fii zimmatika, wahabli jiwaarika, faƙihi min fitnatil ƙabri wa azabin naari, wa anta ahlul wafaa’i wal haƙƙi fagfir lahu warhamhu innaka antal gafuurur rahiimu”.

    {Ya Allah! Haƙiƙa wane ɗan wane yana cikin alƙawarinka (na kiyayewa) da amanarka; don haka ka tserar da shi daga fitinar ƙabari da azabar wuta. Kai ne ma’abocin cika alƙawari da gaskiya; ka gafarta masa, ka ji ƙansa. Haƙiƙa kai, kai ne mai yawan gafara, mai yawan jin ƙai}.

    Allaahumma abduka wabnu amatika taaja ilaa rahmatika, wa anta ganiyyun an azabihi, in kaana muhsinan fazid fii hasanaatihi wa in kaana musii’an fatajaawaz anhu”.

    {Ya Allah! Bawanka kuma ɗan baiwarka ya buƙatu ga rahamarka, kuma Mawadaci ne ga barin azabarsa. Idan mai kyautata aiki ne, ka yi ƙari a cikin kyawawan ayyukansa; idan kuma mai mummunan aiki ne, ka yafe masa}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’a A Yayin Da Ake Rufe Idanun Mamaci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Samun Lafiya Ga Cututtuka danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin Danna nan.

  • Addu’a A Yayin Da Ake Rufe Idanun Mamaci

    Addu’a A Yayin Da Ake Rufe Idanun Mamaci

    Allaahummagfir li fulaanin (bismihi) warfa’a darajatahu fiil mahdiyyina, wakhlufhu fii aƙibihi fil gaabiriina, wagfir lanaa walahu yaa Rabbal aalamiina, wafsah lahu fii ƙabarihi wa nauwir lahu fihi“.

    {Ya Allah! Ka yi masa gafara (Sai ya ambaci mamacin da sunansa), ka ɗaukaka darajarsa a cikin shiryayyun bayi. Kuma ka maye masa bayansa a cikin waɗanda ya bari; ka gafarce mu da shi, ya Ubangijin talikai! Kuma ka yalwata masa a cikin ƙabarinsa, kuma ka haskaka shi gare shi}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Da Ake Yi Ga Mamaci A Cikin Sallar Jana’iza danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Karatun Surah A Cikin Sallah danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Falalar Ziyarar Mara Lafiya

    Falalar Ziyarar Mara Lafiya

    Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; Idan mutum ya ziyarci ɗan uwansa musulmi (da ba shi da lafiya); to yana tafiya ne cikin lambunan Aljanna yana tsinkar ‘ya’yan itaciyar su, idan ya zauna sai rahama ta lulluɓe shi.

    Idan da safe ne mala’iku dubu saba’in za su yi ta yi masa salati har ya shiga maraice. In kuma da maraice ne mala’iku dubu saba’in za su yi ta yi masa salati har ya wayi gari.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Nema Wa ‘Ya’Ya Tsari danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’o’i Domin Neman Tsari Daga Azzalumai danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Addu’ar Nema Wa ‘Ya’Ya Tsari

    Addu’ar Nema Wa ‘Ya’Ya Tsari

    Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya kasance yana nema wa Hassan da Husain tsari da wannan addu’ar:

    U’iizu kumaa bi kalimatil laahit taammati min kulli Shaiɗaanin wa haammatin wamin kulli ainin laammatin”.

    {Ina neman muku tsari da kalmomin Allah Cikakku daga dukkan Shaiɗan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai kambun baka, mai cutarwa}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ziyarar Mara Lafiya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ma’anar Sallar Tuba Da Falalarta danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yadda Ake Gaisuwar Barka Ga Wanda Aka Yi Wa Haihuwa

    Yadda Ake Gaisuwar Barka Ga Wanda Aka Yi Wa Haihuwa

    Baarakal laahu laka fiil mauhuubi laka, wa shakartal waahiba, wa balaga ashuddahu, wa ruziƙta birrahu”

    {Allah ya yi albarka ga abin da aka azurta ka da shi, kuma ya saka godewa wanda ya ba ka (shi); kuma Ya sa shi ya rayu har zuwa ga matuƙar ƙarfinsa, kuma a azurta ka da biyayyarsa}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Nema Wa ‘Ya’Ya Tsari danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tarbiyyar Yara danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yadda Ake Salati Ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Bayan Tahiyya

    Yadda Ake Salati Ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Bayan Tahiyya

    “Allaahumma salli alaa Muhammadin wa alaa aali Muhammadin; kamaa sallaita alaa Ibrahima innaka hamiidun majiidun; Allaahumma baarik alaa Muhammadin wa alaa Muhammadin; kamaa baarakta alaa Ibrahima wa alaa aali Ibrahima innaka hamidun majiidun”.

    {Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, kamar yadda ka yi salati ga Ibrahimu da alayen Ibrahimu; lallai kai abin godewa ne, mai girma. Ya Allah! Ka yi albarka ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka ga Ibrahimu; da alayen Ibrahimu, lallai kai abin godewa ne, Mai girma}.

    Allaahumma salli alaa Muhammadin wa alaa azwaajihi wa zurriyyatihi kamaa sallaita alaa aali Ibrahima. Wa baarik alaa Muhammadin wa alaa azwaajihi wa zuriyyatihi kamaa baarakta alaa aali Ibrahima, innaka hamiidun majiidun”.

    {Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu, da kuma ga matansa da zuriyarsa; kamar yadda ka yi salati ga alayen Ibrahim, kuma ka yi albarka ga Muhammadu, da kuma ga matansa da zuriyarsa; kamar yadda ka yi albarka ga alayen Ibrahimu, lallai kai abin godewa ne,mai girma}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tahiyya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sallar Tahiyyatul Masjid danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.