Tag: ilimi

  • Rukunan Waƙafi

    Rukunan Waƙafi

    Waƙafi yana da rukunai guda huɗu kamar haka:

    – Mai waƙafi: sharaɗin mai yin waƙafi shi ne, ya kasance mai hankali; mai cikakken mulkin abin da zai yi waƙafi da shi na dukiya ko kadara, wacce za a iya amfana da ita, ko a bayar da ita haya, a yi amfani da kuɗin hayar.

    – Waƙafi ya zamo an yi shi ne da abin da za a iya aiwatar da shi.

    – Waƙafin ya kasance an yi shi ne da abin da yake akwai shi; don ba zai yiwu mutum ya yi waƙafi da abin da yake tunanin mallaka nan gaba ba.

    – Waƙafin ya kasance na har abada.

    – Amfanin da aka sadaukar na waƙafin ya kasance zai isa ne ga wata hanya ta neman kusanci ga Allah da biyayya a gare shi. Don ba ya halatta a sadaukar da amfanin waƙafi ga wata hanya ta saɓon Allah.

    – Yin waƙafin ya kasance ta hanyar furta wata magana da take tabbatar da niyyar mai yin waƙafi, ta yin waƙafin a bayyane.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sharuɗɗan Mai Kula Da Waƙafi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nau’o’in Masu Amfani Da Waƙafi Ko Hubusi danna nan.

    Wannan baya nin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmawar Waƙafi/Hubusi Da Tasirinsa Wajen Gina Tattalin Arzikin Al’umma; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Ma’anar Waƙafi

    Ma’anar Waƙafi

    Waƙafi kamar yadda kuma ake iya kiran sa da “hubusi” ko “tasbil” ko “tahbis”; a shari’ance na nufin sallama dukiya ko kadara, sallamawa ta har abada don neman yardar Allah Maɗaukakin Sarki; ga waɗanda mai waƙafin yake son su amfana da dukiyar ko kadarar.

    Wannan ya haɗa da gina masallatai don masu yin sallah, ko makarantu ko haƙa rijiya; don amfanar jama’a ko gina gidajen marayu ko gajiyayyu da dai sauran su.

    Domin karanta cikakken bayani akan Taƙaitaccen Tarihin Waƙafi A Musulunci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Takaiceccen Tarihin Rayuwar Dr. Yahaya Tanko danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmawar Waƙafi/Hubusi Da Tasirinsa Wajen Gina Tattalin Arzikin Al’umma; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Manufofin Waƙafi

    Manufofin Waƙafi

    Ana yin waƙafi saboda cimma manufofin ne guda biyu, waɗanda kuma suka yi rassa masu ɗimbin yawa, waɗannnan manufofi guda biyu su ne:

    1. Manufofi na addini

    Waƙafi babbar alama ce na ƙarfin imanin wanda ya yi shi; da kwaɗayin da yake da shi na aikata alheri da kyautatawa ‘yan uwansa.

    Ta hanyar waƙafi musulmi zai samu damar riskar abubuwan da zai iya rasawa na ladan aikata alheri, bayan ya bar duniya.

    Samun ladan bin umarnin Ma’aikin Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ta hanyar aikata abin da ya yi umarni da shi; wanda wannan ba shakka manufa ce babba.

    A cikin waƙafi da mutum ya yi wa ‘yan uwansa, akwai ladan sadar da zumunci.

    Haka kuma, a cikin waƙafi akwai ladan taimako bisa aikin alheri da kyautatawa; kamar yadda Allah maɗaukakin Sarki ya yi umarni a cikin Alƙur’ani mai girma.

    2. Manufofin Kyautata Zamantakewa A Tsakanin Mutane:

    Amfanar da al’ umma tare da magance matsalolinsu ta hanyar sadaukar da wani abin amfani a gare su.

    Magance matsalar nan ta taskace dukiya a hannun waɗansu ‘yan tsirari daga cikin al’umma da faɗaɗa amfaninta.

    Magance matsalar ajiye kadara tsawon lokaci ba tare da an amfana da ita ba.

    Haka nan waƙafi hanya ce ta samar da ayyukan yi ga mutane masu yawa; waɗanda za a ɗauka aiki don yin hidima ga ayyukan waƙafin da sauransu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Rukunan Waƙafi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tattalin Arziki A Nijeriya danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmowar Waƙafi/Hubusi Da Tasirinsa Wajen Gina Tattalin Arzikin Al’umma; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Dangogin Waƙafi

    Dangogin Waƙafi

    Ana iya yin waƙafi a ɓangarori da dama da suka haɗa da:

    Ɓangarorin yaɗa addini da ilmantarwa:

    1. Gina masallatai da samar da abubuwan Jin daɗin masallata:

    A cikin su waɗanda suka haɗa da rijiyoyi don samun ruwan alwala da sauransu. Ba shakka musulmai magabata sun yi ƙoƙari matuƙa ta yadda suka samar da masallatai daban-daban; tare da ƙawata su da fitilu, da cika su da Alƙur’ani da shimfiɗu, tare da ɗaukar nauyin ɗawainiyar kulawa da su, da biyan albashin masu yi musu hidima; ta hanyar karantarwa da ilmantarwa da kiran sallah da sauransu.

    Kaɗan daga cikin misalan waɗannan sun haɗa da abin da masana tarihin Musulunci suka bayyana a litattafansu cewa; yawan masallatan da suke birnin Kurɗubah ta ƙasar Andalus a ƙarni nan a uku bayan Hijira (ƙarni na goma a shekarar Miladiyya) sun kai kimanin ɗari shida. Kowannen su an samar masa duk wani abu da ake buƙata don jin daɗin masu amfani da shi.

    Kamar yadda sanannen abu ne cewa har zuwa wannan zamani namu, akwai ragowar irin masallatai daɗaɗɗu; irinsu masallacin Azhar da ke birnin Alkahira da Masjid al-Amawiy dake birnin Dimashk; da Masallacin Kairawan da a halin yanzu yake Tunisiya da sauran ire-irensu a sauran wurare daban-daban a faɗin duniya.

    2. Gina makarantu da samar musu da kayan aiki:

    Ba shakka tarihin Musulunci cike yake da labarai na waƙafi a ɓangarorin gina makarantu da samar da cikakkun kayan aiki a cikinsu; waɗanda suka haɗa da wuraren kwanan ɗalibai da wuraren hutawar su da lafiyarsu da sauran su. Kaɗan daga cikin misalan waɗannan sun haɗa da abin da aka samo a littattafan tarihi cewa yawan makarantu da aka yi waƙafin su a birnin Skilliya (ƙasar Italiya a wannan a zamani namu); a ƙarni na huɗu shekarar Hijiriyya, wanda yayi daidai da ƙarni na goma sha ɗaya na Miladiyya, sun kai kimanin makarantu ɗari uku; kowacce a cikinsu cike take da ɗalibai a fannoni daban-daban na matakan karatu daban-daban, da jin daɗin na kyautatawa.

    Wannan nau’i na makarantu za a gan shi a ko ina a manyan biranen Musulunci irinsu; Makkah da Dimashƙ da Halab da birnin Ƙudus da Bagdad da Alƙahira da Istanbul da kuma sauran garuruwa.

    3. Waƙafin ɗakunan karatu da na bincike:

    A irin wannan nau’i na waƙafi za ka iske an samar da ɗakunan karatu an kuma cika su da littattafai na fannonin ilmi daban-daban; kamar yadda akan samar musu da ma’aikata ƙwararru da za su rinƙa kulawa da su da suka haɗa da kwararru a fannin fassara da rubutu da kwamiti na amintattu da dai sauransu.

    Ɓangaren kula da jin daɗin al’umma

    1. Wannan ya haɗa da gina asibitoci da wuraren shan magani:

    Haka nan tarihin Musulunci cike yake da labarai na waƙafi a fannin kulawa da lafiya; ta hanyar gina asibitoci da kulawa da ma’aikatansu da samar da cikakkun kayan aiki da bayar da kyakkyawar kulawa ga marasa lafiya. Asibiti na farko da aka gina a tarihin Musulunci shi ne wanda aka gina a zamanin halifancin Walid ɗan Abdul-Malik wanda ya keɓance shi musamman don masu fama da larurar kuturta, aka kuma ɗauki likitoci ƙwararru, aka kuma ware musu albashi.

    Bugu da ƙari kuma, hatta su kansu marasa lafiya aka yanka musu kuɗaɗen alawus na kula da su. Waɗansu daga cikin misalai na irin wannan nau’i na waƙafi sun haɗa da asibitin Mustashfa Al ‘adudiy dake birnin Bagdad; wanda aka gina ƙarni na huɗu bayan Hijira (ƙarni na goma sha ɗaya na Miladiyya); da Almustashfa Annuriy dake birnin Dimashk wanda Sultan Nuruddin ya gina a shekara ta 549 bayan Hijira da Almustashfah Almansuriy dake birnin Alƙahirah.

    Kuma wani abin ban sha’awa a nan shi ne, tun tsawon wancan lokaci, an samu waɗanda suka yi waƙafi na waɗansu asibitoci na musammman kamar ciwon ido; da na ƙashi, da na fata da cututtukan taɓin kwakwalwa, da sauransu. Kamar yadda kuma aka gina asibitoci aka kuma yi waƙafi da su musamman ga waɗansu makarantu; don amfanin malamansu da ɗalibansu da kuma na talakawa da miskinai.

    2. Gina Wurare Na Musamman Don Kulawa Da Gajiyayyu:

    Ma’anar gajiyayyu da aka ambata a nan sun haɗa da marayu da ‘yan tsintuwa da nakasassu da makafi; kai har ma da tallakawa gidajen marasa ƙarfi wajen ɗaukar nauyin aurar da ‘ya’yansu da hidimomi masu dangantaka da waɗannan.

    3. Samar Da Ruwan Sha Da wurare Kwana Ga Dukkan Masu Buƙata:

    Ba shakka addinin Musulunci ya kwaɗaitar da mabiyansa wajen sadaukar da dukiya ta hanyar waƙafi a wannan bangare; haka nan musulmi sun yi namijin ƙoƙari matuƙa wajen aiwatar da wannan umarni; kamar yadda muka gani a baya na sayen rijiya da sayyidina Uthman ya yi, ya kuma sadaukar da ita ga ɗaukacin al ‘umma.

    4. Taimakon Talakawa Da Masu Ƙaramin Ƙarfi:

    Wannan ɓangare ya shafi sadaukar da amfanin wata dukiya ko kadara ga mabuƙata; kamar yadda sayyidina Umar Allah ya yarda da shi ya yi da gonarsa dake Khaibara, kamar yadda muka gani a baya; marasa lafiya ko talakawa ko matafiya ko ɗaliban ilmi da sauransu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nau’o’in Masu Amfana Da Waƙafi Ko Hubusi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarbiyyar Addini danna koren rubutun nan.

    Wannan baya nin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmawar Waƙafi/Hubusi Da Tasirinsa Wajen Gina Tattalin Arzikin Al’umma; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Mu Yi Alhairi, Mu Guji Rowa

    Mu Yi Alhairi, Mu Guji Rowa

    An Karɓo daga Abu Hurairata (Radiyallahu anhu) ya ce: Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce:

    “Kullum da safe waɗansu Mala’iku biyu suna sakkowa, sai ɗayansu ya ce: “Ya Allah ka mayarwa da mai abin da ya bayar, ɗayan kuma sai ya ce; “Ya Allah kawo asara ga mai hanawa (Marowaci)” (Bukahri 1442, Muslim 1010).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Yin Sadaka A Asirce danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Koyi Da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

    Wannan bayani an ciro shine daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Sassauci Ga Wanda Ake Bi Bashi

    Falalar Sassauci Ga Wanda Ake Bi Bashi

    An karɓo daga Abul Yasar (Radiyallahu anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce:

    “Wanda ya yi jinkiri ga wanda yake cikin ƙunci ko ya yafe masa abin da yake bin sa, Allah zai sanya shi a cikin inuwarsa”

    (Muslim: 3014).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sadaƙa Tana Kawar Da Musiba danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Za A Ci Jarabawar Bala’in Da Ya Tsananta A Cikin Sauki danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Ba wa Ɗan Uwa Sadaƙa

    Falalar Ba wa Ɗan Uwa Sadaƙa

    An karɓo da ga Salman ɗan Amr (Radiyallahu anhu) haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce:

    “Bai wa miskinin sadaƙa lada ɗaya ne, bai wa ɗan uwa saƙaka lada biyu ne” (Ladan sadaƙa da ladan sada zumunta)

    (Tirmizi 658).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Sassauci Ga Wanda Ake Bi Bashi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Zikiri danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Yin Sadaka A Asirce

    Falalar Yin Sadaka A Asirce

    An karɓo daga Abu Harairata (Radiyallahu anhu) yace: Annabi (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce: “Mutane bakwai Allah zai sanya su a cikin inuwarsa a yinin da babu wata inuwa sai inuwarsa:

    1) Shugaba mai adalci.

    2) Matashi da ya taso kan bautar Allah.

    3) Mutumin da zuciyarsa take a rataye a masallaci.

    4) Da mutanen da suke ƙaunar juna saboda Allah, suka haɗu a haka, suka rabu a haka.

    5) Da mutumin da kyakkyawar mace mai matsayi ta neme shi, sai ya ce: Ni ina tsoron Allah.

    6) Da mutumin da ya yi sadaka a ɓoye ta yadda hagunsa ba ta san abinda damansa ta bayar ba.

    7) Da mutumin da ya tuna Allah yana shi kaɗai, har ya yi ƙwalla. (Bukhari 1423, Muslim 1031).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ba wa Ɗan Uwa Sadaƙa danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Dasa Bishiya

    Falalar Dasa Bishiya

    An karɓo daga Jabir (Radiyallahu anhu) ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce:

    “Duk musulmin da ya dasa bishiya, za a rubuta masa lada duk lokacin da aka ci wannan dashe. Ko aka sata, ko namana dawa ya ci ko tsuntsu ya ci, ko aka ragi dashen.”(Bukhari 2320, Muslim 1552).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Yin Sadaka A Asirce danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ƙulhuwallahu Ahad danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Zikiri

    Falalar Zikiri

    Allah Maɗaukakin Sarki ya ce:-

    “Fazkuruunii azkurkum washkuruu lii walaa takfuruunii

    { ku ambace ni, zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce min} (Baƙara, aya ta 152).

    Yaa ayyuhal – lazina amanuzkurul laaha zikran kasiiran wasabbihuuhu bukratan wa’asiilaa“.

    { Ya ku waɗanda suka yi Imani, ku ambaci Allah ambato mai yawa } (Ahzab, aya ta 41).

    Wazzakiriinal – laaha kasiiran wazzaakiraati a’addallahu lahum magfiratan wa’ajran aziimaa

    { Da masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambaton sa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma }

    (Ahzab, aya ta 35).

    Wazkur Rabbaka fi nafsika tadharru’an wa khifatan wa duunal jahri minal ƙauli bil guduwwi wal’asaali walaa takun minal Gafiliina”.

    { Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai ƙasƙantar da kai da tsoro, ba da ɗaukaka murya ba (tsaka-tsaki tsakanin asirtawa da bayyanawa), da safe da maraice, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu } (A’araf, aya ta 205).
    Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, kamar misalin rayayye da matacce ne”.

    Kuma yace: { Shin ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Sarkin da yake mallakar ku, kuma mafi ɗaukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gare ku da ku haɗu da abokan gabarku ku riƙa dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku? Suka ce ka ba mu labari. Ya ce: Ambaton Allah Maɗaukaki}.

    Kuma ya ce: { Allah Maɗaukaki yana cewa: Ni ina tare da zaton bawana da ni, kuma ina tare da shi idan ya ambace ni. Idan ya ambace ni a cikin jama’a zan ambace shi a cikin jama’ar da ta fi su alheri, in ya kusance ni taki ɗaya zan kusance shi kamu guda, in ya kusance ni kamu guda zan kusance shi tsawon gaɓa guda, in ya zo min ya na tafiya zan zo masa ina gaggawa }.
    Daga Abdullahi ibn Busr, Allah ya yarda da shi, ya ce: Ya Ma’aikin Allah! Shari’o’in Musulunci sun yi yawa a gare ni; saboda haka ka nuna mini wani abu da zan yi riƙo da shi. Ya ce; { kar harshenka ya gushe face yana ɗanye daga ambaton Allah }.

    Kuma Mai tsira da amincin Allah ya ce; { wanda ya karanta harafi ɗaya daga Littafin Allah yana da (ladan) kyakkyawan aiki ɗaya saboda shi; kuma dukkan kyakkyawan aiki ɗaya yana da (ladan) misalinsa goma. Ba ina cewa Alif Lam Mim harafi ba ne a’a, Alif harafi ne, Lam harafi ne, Mim harafi ne}.

    Kuma daga Uƙbata ibn Amir, Allah ya yarda da shi, ya ce; Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya fito alhali muna cikin rumfa, sai ya ce; A { wane ne daga cikinku zai so ya fita kullum da safe zuwa ƙoramar Buɗhan ko Aƙiƙ; ya dawo da taguwa biyu masu manyan tozuna, ba tare da yin wani laifi ba, ko yanke zumunta? } muka ce; “Muna son haka” .

    Ya ce: { Ɗayanku ya je masallaci ya nemi sani, ko ya karanta ayoyi biyu daga cikin Littafin Allah; Mabuwayi mai ɗaukaka, ya fi masa taguwa biyu, ayoyi uku sun fi masa taguwa uku; ayoyi huɗu sun fi masa taguwa huɗu, da kwatankwacin adadinsu na raƙuma }.

    Kuma mai tsira da amincin Allah ya ce; {wanda ya zauna a wani waje bai ambaci Allah a wajen ba; wannan zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah. Wanda ya kwanta a makwanci bai ambaci Allah a wajen ba; shi ma zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah}.

    Kuma mai tsira da amincin Allah ya ce; { Babu wasu mutane da suka zauna a wani majalisi da ba su ambaci Allah a cikinsa ba; kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba, face ya zamo musu abin bibiya; in Allah ya so ya yi musu azaba, in ya so ya gafarta musu }.

    Kuma mai tsira da amincin Allah ya ce; { Babu wasu mutane da za su tashi daga wani majalisi da ba su ambaci Allah a cikinsa ba, face sun zama kamar sun tashi daga kan mushen jaki ne; kuma zai zamanto musu abin da- na- sani }.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’o’in Tashi Daga Barci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Kalmomi Guda Biyar Masu Amfani A Duniya Da Lahira danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani; Domin karanta cikakken littafin danna nan.