Tag: ilimi

  • Gudunmawar Tsangayun Alƙur’ani Wajen Cigaban Al’umma

    Gudunmawar Tsangayun Alƙur’ani Wajen Cigaban Al’umma

    Za mu iya cewa tsangayun Alƙur’ani da cibiyoyin ilmin Addinin Musulunci su ne tushen wayewa a wannan nahiya ta Afrika; wadda al’ummar duniya ke kallo a matsayin koma baya (har ana yi mata laƙabi da “Dark Continent” – Turawa, irin su Captain Hugh Clapperton da Major Dixam Denham da Dr. Waller Oudney; da Richard Lander ganau ne su, ba jiyau ba.

    Domin kuwa a lokacin da suka fara shigowa Wannan nahiya (Niger-area) a 1820 sun ga bambanci a bayyane tsakanin al’ummar Musulmi, idan aka kwatanta mu da mutanen Kudanci masu tafiya cikin tsiraici da rayuwa mai kama da rayuwar dabbobi. Domin kuwa sun tarar da cibiyoyin ilmi a tsangayu sama da dubu ashirin (20,000) a Arewacin Najeriya, ga Cikakken tsarin shugabanci da zamantakewa, ga mu da kotuna da wasiƙun hulɗar jakadanci da Larabci da Ajami da Limamai da masana daban-daban. Babban abin alfaharin Arewacin Najeriya a yau shi ne, zai yi wuya a haifi yaro ya girma ya balaga ba tare da ya dangana da makarantar allo ba.

    Tsangayun Alƙur’ani ba su gushe suna bayar da gudunmawa wajen cigaban al’ummar Najeriya ba; har sai da ta kai ta kawo cewa, idan ta fuskar noma da kasuwanci ne, to ana cin arziki da ƙwazo da himmar ma’abota tsangaya. Alal misali, tun kafin a samu man fetur a Najeriya; tattalin arzikinmu ya ta’allaƙa ne kan noman auduga da gyaɗa da sauransu. Kuma mun san irin yadda makarantan tsangayu suka yi fice wajen noma da gogayya da masu sayan gyaɗa da auduga tun a wancan lokaci.

    Ta fuskar kasuwanci kuwa, tsangayun Alƙur’ani sun shahara wajen yaye gardawa da matasa masu kishin kai da neman na kansu. Babban misali a nan shi ne irin hulunan Zanna Bukar da aikin Kwaɗo-da-linzami da Asake da ‘yan tsangaya ke yi. Waɗanda sun sami matuƙar karɓuwa, har ana safarar su zuwa wasu ƙasashe da ke Afrika ta Yamma.

    Cinikayya kuwa ba ta yiwuwa sai da kyakkyawar tarbiyyar ruhi da amana.

    Wannan ya sa irin almajiran da tsangayun Alƙur’ani suka yaye su suka mamaye kasuwanninmu na Kwari da Dawanau da Sabon Gari da sauransu. Rashin irin wannan tarbiya ta sanya ‘yan makarantun boko manya kamar jami’o’i ba sa iya gogayya a fagen kasuwanci. Dalili a nan kuwa shi ne, su sun fi so su ci da biro cikin ofisoshi.

    An ce kusan cikin kowaɗanne ‘yan kasuwa goma da ke Kasuwar Kwari; za ka iske fiye da biyar (5) asalinsu almajiran tsangaya ne. Cikin waɗanda suka yi fice akwai Alaramma Alhaji Malam Ibrahim Tal’udu; da Alhaji Rabi’u Mai Shadda da Alhaji Ahmadu Kofa da Malam Sa’idu. Idan kuwa muna zancen odar kaya daga ƙasashen waje ne ko mallakar kamfanoni ne; to ‘yan tsangaya irin su Alhaji Is’haƙa Rabi’u ba sa buƙatar sharhi.

    A taƙaice dai, tsangaya na tarbiyyantar ‘ya’yanta kan dogaro da kai komai ƙanƙantarsa. Shi ya sa ba za ka taɓa jin labarin ɗanta ɗaya ya gudu da kayan ‘yan’uwa cikin tsangaya ba; ko kuma a ce alarammomi sun yi yajin aiki don ba albashi.

    Amma ina iyakar adadin ‘ya’yan da boko ta yaye da suka wawashe kuɗaɗen ma’aikatunsu; ko na jihohinsu ko ma na ƙasar baki ɗaya?

    Daga ƙarshe, kada mu manta rawar da makaranta AIƙur’ani ke takawa wajen suturta kowannenmu in ya riga mu gidan gaskiya; da ɗaurin aure da raɗin suna da sulhu tsakanin Al’umma, ga uwa-uba; jagorancin Salloli da kuma yin addu’o’in zaman lafiya da koyar da Alƙur’ani ga ƙananan yara da manya dare da rana.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Zuwan Tajwidi Da Musabaƙa Da Tasirinsa Cikin Tsarin Tsangaya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sahabban Da Suka Fi Kowa Rawaito Hadisai danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Kayan Karatu A Tsangaya

    Kayan Karatu A Tsangaya

    Hausawa na cewa “Tun kafin a haifi uwar mai sabulu, balbela take da farinta”. Makaranta Alƙur’ani sun daɗe da mallakar kayan karatu da matallafa koyo (lnstructional/Teaching Materials).

    Bugu da ƙari, makaranta a tsangaya na da fasahar sarrafa waɗannan matallafan yadda za su dace da buƙatarsu. Alal misali, yadda suke feƙe alƙalami ya zama kafe ko jirge, ƙaramin baƙi ko babba da dai sauransu.
    Zai yi kyau, mu ɗauki waɗannan matallafan koyo a tsarin tsangaya domin mu yi musu nazari na musamman.

    Allo: “Faskaren gwani”, ko da yake dai ba alaramma ne ke sassaƙa alluna ba, amma duk da haka ba don su ba, da an daina sassaƙa shi. Kalmar allo ararriyar kalmar Larabci ce “Allawh” aka mayar da ita Bahaushiya da cikakkiyar ma’anarta ta Larabci ba tare da wani canji ba. Allo “Turmin dakan tilawa!” Kamar yadda wasu ke masa kirari, shi ne matallafi na farko da makaranta ke runguma a dukkan matakan karatu. Da yawa manyan makaranta ko alarammomi ke rubuta allunansu, alhali sun ma rubuta Alƙur’ani sau barkatai.

    Tun daga kan ƙananan almajirai masu ƙananan alluna, har zuwa kan samari masu rubuta sumuni ko rubu’i ko ma izu gaba ɗayansa, allo shi ne abokin karatu. A baya-bayan nan an gano cewa, haddar da aka samu ta hanyar allo tafi ƙwari a kan wadda aka yi da Alƙur’ani da takarda a hannu.

    Amfani da allo bai taƙaitu ga tsangayu a Arewacin Najeriya ba, har ma da ƙasashen Larabawa irin su: Sudan da Mauritaniya da Libya, duk suna amfani da alluna. Domin kuwa tin zamanin Sayyadina Umar aka fara yi wa yara rubuta kan alluna a makaranta. Duba Sashe na Farko, Babi na Ɗaya kan koya da koyar da Alƙur’ani zamanin Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) da Sahabbai (Radiyallahu Anhuma).

    Alƙalami:- Makaranta na sarrafa gamba ta hanyar feƙe ta gwargwadan yadda za ta ba su girman baƙin alƙalamin da suke so. Misali:

    Kafe: Shi ne alƙalamin da aka datse kansa a kwance ba tare da karkacewa ba. Alƙalami kafe shi ne mafi yawan lokuta, aka fi amfani da shi wajen rubutu, kuma yana ba da baƙaƙe masu zubin dakali-dakali (blocks).

    Jirge: Shi ne alƙalamin da aka datse kansa a Karkace. Ma’ana a jirge. Galibi gwaninta ke sanya iya rubutu da Jirge. Da makaranta sun ga rubutu za su iya gane cewa da wane irin alƙalami aka yi shi.

    Tawada:- Makaranta kan haɗa tawada ne da zuge da ƙaro. Koda yake tawadar da ake yi ta hanyar wanke ta fi kyau musamman in an gamu da gwanin haɗa ta. Irin wannan tawada ita ake kira zege da barbarci.

    Yambari:- Da yawa za a ga ado mai launi daban-daban cikin Alƙur’ani rubutun hannu. Wani rawaya wani kore da sauransu. Sirrin wannan shi ne amfanin da makaranta ke yi da wasu abubuwa su yi tawada mai launi. Yambari ɗaya ne daga cikin nau’o’in tawadun da makaranta ke amfani da shi; wajen yin rubutu mai ban sha’awa da ɗaukar ido.

    Adadin ayoyi a farkon kowace sura akan rubuta shi da jan rubutu. Wasali kan zo daga ƙarshe, shi ma ana yin sa da jar tawada (Yambari) Nau’ukan Yambari a wajen Bare-bari; sun haɗa da Kimeyaram don yin wasali Zarni; rawaya don yin hamza, Maririma (kore) don laftra.

    Korami:- Wani kwaroro ne da ake yi da kaba don sanya alƙaluma. Korami kan kare alƙaluma daga karyewa ko ɓata.

    Takarda:- Makaranta kan yi amfani da Takarda wajen rubuta wata bara ko laƙani. Su kuwa masu rubuta Alƙur’ani kan yi amfani da takarda ta musamman mai tsirkiya da ake kira Holoma.

    Bukari:- Wannan wani abin aiki ne da ya keɓanci marubuta Alƙur’ani. Bukari wani ɗan ƙarfe ne mai ƙafafu guda biyu, ƙafa ɗaya da bakin alƙalami ɗaya kuma mai tsini. Marubuta na yin amfani da Bukari wajen zana da’ira a matsayin kuri; ko alamar izu ka sabu’u ko kuma alamar sujjadda. Marubuci kan buɗe ƙafafun bukari gwargwadon yadda yake son girman da’ira a cikin rubutunsa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tsarin Karatu A Tsangaya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’o’i Domin Neman Tsari Daga Azzalumai danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Abubuwan Da Suke Kawo Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

    Abubuwan Da Suke Kawo Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

    Akwai abubuwa da dama waɗanda suke kawo tabbataccen da dauwamammen zaman lafiya da tabbataccen kwanciyar hankali ga ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi, kai har da duniya ma gaba ɗaya.

    Amma duk waɗannan abubuwa in aka dunƙule za su iya zama abu ɗaya tak, shi ne imani da bin dokokin Allah da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam). Wannan shi ne zai yi wa mutum jagoranci domin samun nutsuwa da hutun zuciya maras misalı, kuma ya zauna da kowa lafiya ta hanyar bai wa kowa haƙƙinsa.

    Ga kaɗan daga cikin waɗannan abubuwa:

    1. Imani da aiki nagari

    Allah Ta’ala ya ce: Duk wanda ya aikata aiki nagari, namiji ne ko mace, kuma yana mai imanı, to za mu raya shi rayuwa mai daɗi. (Suratun Nahl: 97). Kuma Allah yana cewa: “Waɗanda suka yi imani da Allah da ranar lahira, babu tsoro a kansu, kuma ba za su yi baƙin ciki ba” (Sura Mai’da” 69).

    Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce, “Lamarin mumini yana da ban mamaki, komai nasa alhairi ne, in ban da mumini babu mai samun haka. Idan alheri ya same shi, sai ya gode wa Allah, sai ya zama alhairi, in kuma sharri ya same shi, sai ya yi haƙuri, wannan sai ya kasance alhairi a gare shi” (Muslim 18/125).

    Wannan hadisi yana nufin in dai akwai Imani a zuciyar mutum, to babu wani abu a duniyar nan da zai dagula masa lissafi, ya hana shi sakat, ballantana ya tayar masa da hankali.

    Mu ɗauki misalin wani mumini guda ɗaya, shi ne Shaihul Islam Ibn Taimiyya. Wannan bawan Allah ya shiga tasku iri-iri, ya sha ɗauri da duka da korar kare daga garinsu, laifinsa kawai shi ne, dagewa da matsanancin naci kan gaskiya, kai a ƙarshe dai a kurkuku ya mutu. A dab da mutuwarsa, yake faɗa a cikin kurkukun Dimashƙa: “Babu fa yadda maƙiyana za su yi da ni, ni aljannata da lambuna yana cikin zuciyata, duk inda na je, ina tare da ita ba na rabuwa da ita, ɗaure ni, halwa ce, kashe ni shahada, in kuma an kore ni, na samu damar yawata duniya domin nazarin ayoyin Allah da ikonsa.

    Allahu Akbar! Allah ya jiƙan maza, maza sun faɗi.

    2. Imani da ƙaddara

    Ya ɗan’ uwa mai karatu, in kana fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, to ka yarda da cewa duk abin da ya faru a duniyar nan, gare ka ko ga waninka, mai daɗi, ko marar daɗi, to haka Allah ya nufa, haka ya so, haka ya ƙaddara, kuma in duk duniyar nan za ta haɗu a kan a canja wannan abu, ba zai yiwu ba. To in ka yarda da haka, sai ka huta wa zuciyarka, ka sami nutsuwa.

    Ga wani misali mai ƙayatarwa, ciwon daji ya fito a ƙafar Urwatu Ibnuz Zubair (Radiyallahu Anhu ) sai Likitoci suka ce za su ba shi giya ta bugar da shi, domin a guntule ƙafar cikin sauƙi. Sai ya ce atafau ba zai yarda ya sha giya ba ta kowane hali. Sai ya ce, “In so kuke sai lokacin da hankali na ya gushe za ku guntule min ƙafa, to ku bari sai na fara sallah”.

    Hakan kuwa aka yi, yana sallah aka guntule ƙafar, bai ko motsa ba, sai da aka tsoma dungulmin cikin tafasasshen mai, sai ya suma. Can cikin dare sai ya farka, ya ji ana yi masa jajen kafarsa da kuma ta’aziyyar mutuwar ɗansa a wannan ranar! Amma saboda tsabar imani sai ya ce “Alhamdu lillahi tun da Allah ya ba ni lafiya kuma ya bar mun ɗaya ƙafar da ragowar ‘ya’yan.

    Allahu Akbar! ka ji salaf na gaskiya, to yanzu wane abu ne zai iya tayar da hankalin wannan bawan Allah?

    3. Ilmin Addini

    Ilmi shi ne gishirn rayuwa, shi ne fitila mai kau da duhun jahilci da talauci da ɓacin rai da duk wata damuwa. Mai ilmi yana cikin farin ciki da daɗin da ba wanda zai iya siffanta shi, sai wanda ya shige shi, saboda babu tsoron kowa a zuciyarsa, sai na Allah.

    An yi wani azzalumin sarki a Masar mai suna Ahmad Ibn Tuluna, wanda aka ce ya kashe sama da mutum dubu goma sha takwas (18,000) ta hanyar hana su ci da sha, har sai sun mutu.

    Kowa yana tsoron wannan mamuguncin sarki, amma wani malami mai suna Abul Hasan Zahid (Radiyallahu Anhu) ya yi ta maza, ya yi shahada ya fuskance shi, ya je ya yi masa wa’azi kan irin ta’asar da yake aikatawa. Ai fa nan da nan ya harzuƙa, ya kufulo, ya sa aka damƙe wannan malami aka jefa a kurkuku. Ya sa aka kamo zaki, aka hana shi abinci kwana uku, sannan aka tura shi ɗakin da malam yake.

    Wayyo! Ɗan uwa me kake zato zai faru? Ai malam ko a jikinsa, yana zaune ya fuskanci alƙibla, ya Sunkuyar da kansa kamar mai tunani. Shi kuwa zaki sai ya yi ta kewaya malam yana kaɗa jela kamar kare ya ga uban gidansa. Da ya gaji sai ya fito ya kama gabansa.

    Wannan abu ya bai wa kowa mamaki musamman wannan azzalumi (Ɗan Tuluna), waje ya ruɗe da kabbara da godiya ga Allah, saboda kuɓutar malam Abul Hasan. Shi da kansa Sarki ya zo ya ba shi haƙuri, ya ce, “Don Allah wai tunanin me kake yi lokacin da zakin nan ya yiwo kanka, na ga kai ko damuwa da shi ba ka yi ba?

    Sai ya ce, “Ai ni a lokacin tunanin hukuncin miyan zaki nake yi idan ya taɓa ni, shin najasa ne ko tsarkakakke? Sannan ya ce to ba ka ji tsoron zakin ba? Sai ya ce sam Allah ya yaye min wan nan. Kai ɗan uwa in ka na son jin daɗi na gaskiya da zaman lafiya da kwanciyar hankali to ka nemi ilimin addini saboda Allah kuma ka yi ƙoƙarin aiki da shi. Allah ya sa mu dace.

    4. Yawan ambaton Allah da karatun Ƙur’ani

    Allah Ta’ala ya ce: “Ku faɗaka da ambaton Allah ne zukatu suke nutsuwa (Suratur Ra’adi:28).
    Duk mutumin da yake yawaita zikiri, zai rayu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, wanda kuwa bai damu da zikirin ba, ya shiga uku.

    Allah Ta’ala ya ce: “Wanda ya kau da kai daga ambaton Allah, za mu hore masa wani shaiɗani ya kasance tare da shi (Suratu Zukhruf: 86). Kuma ya ce: “Duk wanda ya kau da kai daga Ambato na, to haƙiƙa rayuwar ƙunci za ta tabbata a gare shi, kuma za mu tashe shi ranar ƙiyama makaho (Surat Taha: 124).

    Kuma Allah ya ce: “Bone (azaba, wahala, tashin hankali) ya tabbata ga masu busasshiyar zuciya daga ambaton Allah, waɗannan suna cikin ɓata bayyanan ne” (Surat Zumar:22).

    Waɗannan ayoyın suna nunı ga tasirin da zikiri ya ke da shi wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali. Amma ya kamata ka sani cewa, zikiri kala-kala ne, wannan ya haɗa da karatun Ƙur’ ani da hadisi da ilmin Musulunci da addu’o’in ma’aiki, tun daga wayewar garı, har kwanciya barci, tunani kan ikon Allah da hikimominsa, tuna Allah lokacin aikata alhairi ko sharri, hailala, tasbihi, istigfari salati ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) da sauransu.

    Sannan ka sani cewa zikiri da duk wata ibada ba za su yi amfani ba, sai an yi su saboda Allah kuma daidai da yadda Allah da Manzonsa suka yi umarni, babu ƙari, babu ragi. Allah ya ganar da mu.

    5. Sakin rai

    Ya ɗan’uwa, in kana son zaman lafiya da kwanciyar hankali, to ka saki ranka ka tsarkake Zuciyarka daga duk wani dagwalo da tsatsa, waɗanda suke tayar da hankali irinsu hassada da girman kai da gaba da ganin ƙyashi da riya da jiji da kai da sauransu.

    6. Kyautata wa mutane

    Kyautata wa mutane ta hanyar nuna musu ƙauna da fatan alheri, da taimakonsu, da ba wa kowa haƙƙinsa, da girmama su, yana da tasiri mai ban mamaki wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali. Mutum mai alhairi yakan samu karɓuwa da farin jini a cikin al’umma, kai yakan fi waɗanda ya kyautatawa jin daɗi da farin ciki. Wannan abu an gwada an gani, yi ƙoƙari ka shiga cikin ayarin masu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    7. Ka hangi na ƙasa da kai, ka daina hangen na sama da kai

    Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce: “Ku rinƙa duban na ƙasa da ku, ku dai na hangen na sama da ku, saboda kada ku raina baiwar Allah a gare ku”. (Muslim ne ya rawaitoshi).

    Wannan Hadisi ya shimfiɗa ƙa’idar zaman lafiya da kwanciyar hankali, wato a kullum kada ka raina baiwar da Allah ya yi maka, duk halin da kake ciki ko mai muminsa, in ka duba ƙasa za ka ga ka fi waɗansu da dama, ka ga sai ka ji daɗi ka gode wa Allah, hankalinka ya kwanta. Amma idan kana hangen waɗanda suka fi ka, to ka shiga cikin taskar wahala da tashin hankali ke nan.

    Sai dai kuma wannan ya shafi abin duniya ne kawai, amma a harkar ilmi da addini, so ake yi kullum ka rinƙa hangen na sama da kai, domin ka yi himma ka yi koyi da su. In kuwa kana duban na ƙasa da kai a ilimi da ibada, sai lalaci da girman kai ya kama ka, shi ke nan kuma sai komai ya ruguje.

    8. Gajarta buri

    Ka sani cewa rayuwar nan ta duniya taƙaitacciya ce, saboda haka, kada ka sake ka taƙaice ta da yawan tunane-tunane da damuwa kan abin da bai zo ba ko kuma wandą ya riga ya wuce. Ka sani cewa rana da wata ba za su tsaya jiran ka ba, yi ƙoƙari ka amfani lokacinka da ayyukan alhairi, kada ka rinƙa dogon buri.

    Wata rana waɗansu mutane masu tsoron Allah suna tattaunawa kan gajarta buri. Sai ɗaya ya ce: “Ni a yanzu in na kai loma ɗaya bakina, ba na sa ran zan sake kai ta biyu” . Ɗayan kuwa sai ya ce, “Cafɗi-jan! Kai kana da ɗauka da yawa. Ai ni duk yayin da na ja numfashi ba na sa ran zan sake jan wani!” Allah Akbar, ɗan uwa duk wanda bai ɗauki duniyar nan da zafi ba, to haƙiƙa shi ne cikakken mai zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    9. Yarda da cewa rayuwar lahira ita ce haƙiƙar rayuwa

    Duniya ba gidan zama ba ce, hanya ce kawai da mutum zai bi zuwa gidansa na rayuwa, wacce ba ta da ƙarshe, ko cikin daɗi ko wuya. Wanda duk wannan aƙida ta tabbata a cikin zuciyarsa, to haƙiƙa rayuwarsa ta duniya za ta zama mai sauƙin gaske, shike nan sai ya yi ta tanadin samun tsira ranar lahira a nan duniya, kuma sai ya zauna lafiya cikin kwanciyar hankali.

    Ga wani labari mai ban sha’awa na Al-Hafiz bn Hajar (Radiyallahu Anhu) a lokacin da ya ke alƙalin Misra. Wata rana ya fito cikin kwarjini da ado, sai wani Bayahude cikin tsummokara da jigata ya tsayar da shi, ya ce, “Ranka ya daɗe, tambaya nake”. Sai ya ce, “Bismillah”. Sai ya ce, “An ce Annabinku ya ce, “Duniya kurkukun mumini ce, kuma aljannar kafiri ce”, to yaya aka yi ni nake cikin wannan hali na tsiya, kai kuma ga ka cikin daula?

    Sannan Hafiz ya ce: “I, duk da wannan ni’ima da na ke a ciki, in an kwatanta da ni’imar aljanna, sai ka ga kamar a kurkuku nake.

    Kai kuma duk da wahalar da kake fama da ita yanzu, in an auna da azabar da za ka gamu da ita a lahira, sai ka ga yanzu kai a aijanna kake”. Sai ya ce, “Haka ne”? Sai ya ce, “Ƙwarai kuwa”. Nan take sai Bayahuden nan ya musulunta!

    Saboda haka, ɗan uwa duk halin da kake ciki, ka da ka mance da lahira, domin ta fi duniya nesa ba kusa ba a ɓangaren daɗi ko wuya.

    10. Zama da mutanen kirki

    Haƙiƙa mutanen kirki muminai, masana, masu aiki da saninsu, masu tsoron Allah, su ne suke cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. To saboda haka, idan kana so kai ma ka sami haka, sai ka yi fatali da lalatattun abokai, ka yi abota da mutanen kirki, waɗanda za su nuna maka hanyar Allah. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce:”

    Misalin aboki nagari da lalataccen aboki, kamar wanda yake zaune ne da mai sayar da turare da wanda yake zaune da maƙeri. Shi dai wanda yake sai da turare, ko bai fesa maka ba, za ka shaƙi ƙamshi. Shi kuwa maƙeri ko dai ya ƙona ka, ko ka taso da ƙaurin wuta. (Buhari/Muslim). Wato dai zama da maɗaukin kanwa, shi ke kawo farin kai.

    11. Yin afuwa da kyautatawa wanda ya ɓata maka

    Tsakanin harshe da haƙori ma akan saɓa, ballantana tsakanin mutum da mutum, kuma Duk wanda ya ce: “Zo mu zauna, ya ce zo mu ɓata. Waɗannan kalmomi ne na hikima, masu ɗauke da darussa na rayuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali. To maganin saɓawa haƙuri da yin afuwa, saboda tilas sai ka ga yadda ba ka so, in kuwa ka ce duk abin da aka yi maka sai ka rama, to lallai wata rana za ka rame. Yin afuwa yana janyo wa mutum mutumci kwarjini, farin jini lada da farin ciki da kwanciyar hankali. Ga waɗansu ‘yan misalai:

    Waɗansu miyagun malamai sun taɓa haɗe wa Shaihul Islam Ibn Taimiyya kai, suka yi ta cutar sa, har suka yi masa sharri, aka jefa shi a kurkuku.

    Lokacin da aka sake shi, sai aka tambaye shi, ko kana tunanin ɗaukar fansa? Sai ya ce, “A’a, duk na yafe musu, ba komai, Allah ya saka musu da alhairi, wannan zaman kurkuku ya sa na yi nazarin Kur’ani na fahimci waɗansu abubuwa da dama, kuma ai su ne sanadi, na yi musu afuwa, ba wani abu”.

    Wani bawan Allah ya sami labarin cewa, wani mutum ya yi da shi, ya ci zarafinsa. Sai ya ɗauki goma ta arziki, ya tafi da kansa ya kai masa har gida. Sai mutumin ya tambaye shi dalilin wannan alhairi. Sannan ya ce, “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Wanda ya yi muku alhairi ku saka masa.” To kai ka ba ni kyautar ladan ayyukanka, ni kuma ba ni da wani abu da zan saka maka da shi, sai ɗan wannan abin duniyar. Allahu Akbar. Ɗan uwa ka ɗauki ɗabi’ar afuwa ga iyalanka, maƙotanka, da sauran al’umma, ka ga yadda za ka zauna lafiya, ka samu nutsuwa.

    12. Daddaɗar Magana

    Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce: “Wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, ya faɗi alhairi ko ya yi shiru”.
    Duk mutumin da yake aiki da wannan hadisi, haƙiƙa zai zauna lafiya da kowä, kuma zai samu kwanciyar hankali. Duk abin da zai fito daga bakinka ya kasance alhairi ne, magana ce ta gaskiya mai daɗi wacce ba za ta ɓatawa kowa ba.

    13. Addu’a

    Komai ya yi zafi maganin sa Allah. Kuma addu’a makamin mumini ce. Saboda haka bayan bin waɗannan mataki da sauran su, sai ka kasance kullum cikin roƙon Allah ya ba ka zaman lafiya da kwanciyar hankali. Musamman ka riƙi addu’o’in zaman lafiya na Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) kamar wannan addu’ar.

    Allahumma aslih lii diini allazi huwa ismatu amri, wa aslih Ii dunyaa ya allati fiiha ma aashi wa aslih lii aakhirati allati fihaa ma aadii, waj alil hayaata ziyaada talli fii kulli hairin waj alil mauta raahatalli min kulli sharrin.

    Allahuma rahmataka arju fa laa takilni ila nafsi tarfata ainin wa aslih lii sha’ani kullihi laa ilaaha illa anta.

    Allahuma inni a ‘uzu bika mnial hammi wal hazani wa minal jubni, wal bukhli, wa min galabatid daini wa ƙahnimijaali.

    Waɗannan kaɗan ke nan daga abubuwan da suke wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. A dunƙule za mu iya cewa bin Allah da Manzonsa sau da ƙafa da tsarkake zuciya da jiki da mazauni da baiwa ƙwaƙwalwa lafiyayyen abincin imani da kyakkyawar niyya, su ne kaɗai za su kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    Allah ya sa mu da ce. Amin.

    Bayan waɗannan ƙa’i’do’ji, malamai musamman masana halin ɗan Adam, suna bayyana waɗansu ladabai ko dabaru domin zaman lafiya da mutane iri-iri. Ko da yake waɗannan ƙa’idoji da suka gabata, sun isa ga duk mai son zaman lafiya da kwanciyar hankali ya rayu da su, amma duk da haka akwai waɗansu abubuwa da masana suka yi bayani, Ina ganin ya kamata a kammala wannan littafi da su.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Dabarun Zaman Lafiya Da Mutane danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Mutane Biyar Da Suka Yi kama Da Manzon Allah (S.A.W) danna nan.

    Wanna nan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali; wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Mene Ne Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali?

    Mene Ne Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali?

    Zaman lafiya da kwanciyar hankali shi ne burin dukkan ɗan Adam maza da mata; manya da yara musulmi da kafiri babu wani saɓani.

    Za mu iya cewa, yanayin nutsuwa da jin daɗi da farin ciki, annashuwa da samun gamsuwa a zuci Ga kuma waje; ba tare da wani tsoro ko fargaba ko damuwa ba, a kan abin da ya wuce, ko tsoron abin da zai zo; waɗannan abubuwa in sun haɗu, ana iya kiran su zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    Wannan an ɗan kusanto da ma’ana ce kawai, amma a gaskiya sanin haƙiƙanin zaman lafiya da kwanciyar hankali sai wanda yake cikinsa. Larabawa suna kiran sa “Sa’adah” kuma suna fassara shi da cewa kishiyar wato tsiya.

    Rukunan zaman lafiya da kwanciyar hankali guda uku ne:

    1. Ingantacciyar zuciya da jiki.
    2. ingantacciyar rayuwa.
    3. Kyakkyawar makoma.

    Duk mutumin da zuciyarsa ta gurɓata da kafirci da bidi’a da zalunci da sha’awa da sauran su, ko jikinsa ya yarda da lalaci da son hutu kowane lokaci da karɓa ba bayarwa, haƙiƙa wannan mutum ba shi ba zaman lafiya, ballantana kwanciyar hankali.

    Haka kuma duk mutumin da ya ɗaukar wa rayuwa ta ƙarya, mara tabbas, mai cike da ruɗani da hauma-hauma, wacce ba ta da wani tushe ballantana makama, shi ma ba zai shiga cikin masu zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.

    Sanin kyakkyawar makoma da tabbacin inda aka dosa yana da muhimmanci wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Yanzu a haɗa musulmi da ya yarda da Allah da ranar Lahira da wuta da aljanna, da kafiri wanda shi kawai duniya ita ce farko ita ce ƙarshe a wurinsa?

    To amma wacce hanya ce mafificiya domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali? To mai karatu sai in ce maka nan fa ake yin ta; saboda duk mutumin da ka yiwa wannan tambaya, zai ba ka amsa saɓanin ta ɗan’uwansa. Mutane da yawa suna cikin ruɗani game da wannan amsa; kowa kuma aiki yake yi tuƙuru domin tabbatar da ita a kan kansa.

    Amma fa kashi casa’in bisa ɗari sun yi hannun riga da hanyar ba da amsa ingantacciya. Kafin na ba da amsa, bari mu yi nazarin kaɗan daga cikin ruɗu da mutane da dama suke ciki, game da hanyoyın samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ruɗani Game Da Hanyoyin Samun Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Samun Lafiya Ga Cututtuka danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali; wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Illolin Karɓe-karɓe Da Barace-barace

    Illolin Karɓe-karɓe Da Barace-barace

    Addinin musulunci addini ne da ya girmama ɗan Adam ya mutunta shi ya kuma yi umarni da ya kare mutuncinsa ya girmama kansa kada ya wulaƙanta kansa da kansa ya zubar da ƙimar sa ta ɗan Adam.

    Domin tabbatar da wannan manufa Allah ta’ala ya umarci kowa ya tashi ya zage dantse wajen neman na kan sa; ya yi umarni ya kasance mai wadatar zuci da godiya ga Allah ta’ala; kuma ya hana bara, roƙo, maula, bambaɗanci da sauran su.

    Wannan ɗabi’a ce mummuna wacce take kashe zuciyar mutum ta haifar masa da talauci da ƙasƙancin a duniya da lahira. A duniya talauci zai aure shi ya mamaye shi, a lahira kuma zai tashi babu tsokar nama ko ɗaya a fuskar sa.

    Duk abin da mai karɓe-karɓe yake samu haramun ne tsantsa sai dai in yana da wani dalili da shari’a ta yarda shi; wanda ya halatta masa yin roƙon kamar yadda za a kawo hadisai da suke magana akan hakan.

    Ya Allah ka ba mu wadatar zuci ka ba mu ikon godiya a gare ka da dagewa wajen neman halal; ka tsare mu da cin haram da zubar da mutunci mu wajen roƙe-roƙe. Amin Summa Amin.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Wadatar Zuci Take danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Wane Ne Bahaushe? danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Jerin Littattafan Hadisai Arba’in (40) Littafi Na Biyu; Akan (Falalar Wadatar Zuci, Neman Halal Godiya Ga Allah Da Illolin Bara Da Roƙo); wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Hikimomi A Kan Wadatar Zuci

    Hikimomi A Kan Wadatar Zuci

    1) Guntun gatarinka, ya fi sari ka ba ni.

    2) Rabon kwaɗo ba ya hawa sama.

    3) Adon wadata kyauta, adon talaka wadatar zuci.

    4) Abubuwa biyu ba sa zama guri ɗaya, wadatar zuci da hassada, abubuwa biyu ba sa rabuwa, kwaɗayi da hassada.

    5) Mai neman ɗaukaka ya bi Allah, mai neman wadata ya kasance mai wadatar zuci.

    6) Wadatar zuci ita ce tsantsar ‘yanci, kwaɗayi shi ne tsantsar bauta.

    7) Mai matalauciyar zuciya ba zai taɓa wadatuwa ba har abada.

    8) Dutsen da yake hannunka, da shi kake jifa.

    9) Ƙwai a baka, ya fi kaza a akurki.

    10) Duk wanda bai gamsu da kaɗan ba, ba zai gamsu da mai yawa ba.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ƙa’idoji Da Ladaban Neman Halal danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Kyautata Tarbiyyar ‘Ya’ya danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Jerin Littafan Hadisai Arba’in (40) Littafi Na Biyu; Akan (Falalar Wadatar Zuci, Neman Halal Godiya Ga Allah Da Illolin Bara Da Roƙo); wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yadda Wadatar Zuci Take

    Yadda Wadatar Zuci Take

    Wadatar zuci shi ne babban arziki wanda ba ya ƙarewa; wanda ya same shi, ya huce haushin da takaicin duniya, ba shi ba hassada ba ganin ƙyashi ba baƙin ciki ba ruwansa da ƙulle-ƙulle, ba ya tankwaɓarwa da wani arzikinsa.

    Wanda yake da wadatar zuci ya huta; shi ne kaɗai yake jin daɗin rayuwarsa yake cin arzikinsa hankalinsa a kwance.

    Wadatar zuci ita ce yarda da gamsuwa da jin daɗi da godiya ga Allah, a bisa abin da Allah ya ba ka na ni’imominsa; waɗanda ba su da iyaka misali: Rayuwa, lafiya, Sana’a, Mahalli, Iyali, abin hawa da sauran su, ba tare da hangen abin da wani ko wasu suke da shi ba, kuma ba tare da kwaɗayin abin kowa ba. Ita ake kira (Al- ƙaratu) da larabci.

    Wato dai wadatar zuci ita ce kullum mutum ya dinga duban ni’imomin da Allah yai masa; yana jin daɗin su, yana duban na ƙasa da shi, yana godiya ga Allah yana gamsuwa da iya arzikinsa, ba ya hangen na wani ballantana ya sa rai ko ya miƙa hannun roƙo gare shi.

    Mai wadatar zuci yana rayuwa cikin ‘yanci da mutunci da kuma rufin asiri; yana ji a ransa ko da an fi shi kuɗi ko muƙamai; to shi ma ya fi wani, koma ya fi sauran zama lafiya da kwanciyar hankali.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Fa’idojin Wadatar Zuci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Bushewar Zuciya danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Jerin Litattafan Hadisai Arba’in (40) Littafi Na Biyu; A kan (Falalar Wadatar Zuci, Neman Halal Godiya Ga Allah Da Illolin Bara Da Roƙo); wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Fa’idojin Wadatar Zuci

    Fa’idojin Wadatar Zuci

    Wadatar zuci tana da fa’idoji da amfani mai yawan gaske ga kowanne ɓangare na rayuwar duniya ga mutum a duniyarsa da lahirarsa.

    Wasu daga cikin fa’idojin wadatar zuci su ne:

    1) Mai wadatar zuci zai sami yardar Allah Ta’ala.

    2) Imani ba ya zama cikakke sai an haɗa da wadatar zuci.

    3) Mai wadatar zuci yana rayuwa cikin jin daɗi da walwala.

    4) Mai wadatar zuci ba ya riƙe kowa a zuciyarsa, wai don ya fi shi wani abin n duniya, yana nuna ƙauna ga kowa, shi ma yana da farin jini da muhibba a cikin mutane.

    5) Imaninsa da yardarsa da hukuncin Allah da amincewarsa da shi da tawakkalinsa kullum daɗuwa suke yi.

    6) Ba ya shiga cikin damuwa da ɓacin rai, zuciyarsa a sake take.

    7) Wadatar zuci tana hana mutum hassada da annamimanci da yi da mutane.

    8) Hanya ce shararriya zuwa Aljanna.

    9) Allah yana sanya albarka cikin rayuwar mutum da samunsa.

    10) Mutum yana sanin matsayinsa da darajar da Allah yai masa kuma ya kasance mai jan girmansa da mutuncinsa.

    11) Yana kasancewa mai godiya ga Allah, wacce take sawa Allah Ta’ala yai ta ƙara wa mutum ni’imominsa.

    12) Wadatar zuci tana sanya mutum ya kasance mai kamewa, ba zai dinga wulaƙantar da kansa ba wajen bara da karɓe-karɓe.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Suke Hana Wadatar Zuci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Mutum Da Son Zuciya. danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Jerin Littafan Hadisai Arba’in (40) Littafi Na Biyu; Akan (Falalar Wadatar Zuci, Neman Halal Godiya Ga Allah Da Illolin Bara Da Roƙo); wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Abubuwan Da Suke Hana Wadatar Zuci

    Abubuwan Da Suke Hana Wadatar Zuci

    Sai dai kuma duk da waɗannan darajoji da fa’idoji da wadatar zuci ke da su; mutane da dama zukatansu a talauce suke, matattu ne kuma matalauta ne.

    To mene ne yake haifar da rashin wadatar zuci?

    Akwai dalilai da dama ga kaɗan daga cikin su:

    1) Yawan zama da mawadata masu almubazzaranci, marasa godiya ga Allah, marasa wadatar zuci.

    2) Tsananin kwaɗayin abin duniya da ƙwallafa rai kan sai an yi rayuwar kece raini da fantamawa.

    3) Ƙarancin karanta Alƙur’ani da ƙaranci da la’akari da abin da yake koyarwa.

    4) Ƙarancin tunanin mutuwa da kwanciyar kabari da lahira, sai ya kasance babu komai a ran mutane masu mataulautan zukata sai hange-hange da lissafin abin wani.

    5) Dulmiya cikin sha’awa da biyewar rai kan duk abin da yake so .

    6) Son rayuwar bushasha da burga.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yaya Mutum Zai Kasance Mai Wadatar Zuci? danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Jerin Littattafan Hadisai Arba’in (40) Littafi Na Biyu; A kan (Falalar Wadatar Zuci, Neman Halal Gadiya Ga Allah Da Illolin Bara Da Roƙo) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Sharuɗɗan Mai Kula Da Waƙafi

    Sharuɗɗan Mai Kula Da Waƙafi

    An sharɗanta kasancewar mai kula da waƙafi ya kasance:

    • -Ya zamo Musulmi.

    -Baligi wanda ya halatta ya yi tasarrufi a shari’ance.

    -Ya kasance mai adalci.

    -Haka kuma ya kasance yana da ilmi ko ƙarfi da zai ba shi damar tsayuwa tsayin daka wajen
    kula da shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Dangogin Waƙafi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Yin Sadaka A Asirce danna nan.

    Wannan baya nin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmawar Waƙafi/Hubusi Da Tasirinsa Wajen Gina Tattalin Arzikin Al’umma; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa; shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.