Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Young cow who has not yet given birth - A turance tana nufin karsana. Misali; Naman karsana yana da taushi da sauƙin dahuwa. HAU; Karsana (Tana nufin matashiyar saniya wadda ba ta taɓa haihuwa ba)
Younger brother - A turance tana nufin ƙani. Misali; Ƙanina yana makaranta tare da abokansa. HAU; Ƙani (Tana nufin ɗan’uwa namiji wanda yake bin wasu ma'ana yayye)
Younger sister - A turance tana nufin ƙanwa. Misali; Ƙanwata tana makarantar firamare. HAU; Ƙanwa (Tana nufin ‘yar’uwa mace wadda take da yayye)
Yuli - Wata ne na bakwai a shekara. Misali; A watan Yuli zai cika shekara biyar da gama makaranta. ENG; July (A turance yana nufin wata na bakwai a shekara)
Yuni - Wata na shida a shekara. Misali; Damina na kankama a watan Yuni. ENG; June (A turance wata ne na shida a shekara)
Zayyana - Aikin zana tsari da yadda zubin mahalli, kamar gida zai kasance a gine.
Ɓaci - Tana nufin lalacewa. Misali; Rigar ta ɓaci da amai sai an sake wata. ENG; Spoiled (A turance tana nufin ɓaci)
Ɓagas - Tana nufin samun abu cikin sauƙi ba tare da an sha wahala ba. Misali; A ɓagas y samu kayan da ya siyo. ENG; Cheaply (A turance tana nufin ɓagas)
Ɓararraka - Tana nufin dahuwa ba ƙaƙƙautawa. Misali; Waken yana ta ɓararraka tun ɗazu. ENG;Boil Continuously (A turance tana nufin ɓararraka)
Ɓarawo - Tana nufin mutumin da yake sata. Misali;An kama ɓarawo a gidan Alhaji Iro jiya da daddare. ENG; Thief (A turance tana nufin ɓarawo)
1 316 317 318 319 320 332