Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Using clever or deceitful means for some purpose - A turance tana nufin kissa.
Misali; Ba asiri ta yi wajen fitar da abokiyar zamanta ba, kissa ce da kisisina.
HAU; Kissa (Tana nufin yin amafani da wayo da dabara da hilata don cimma manufa)
Utterance - A turance tana nufin furuci.
Misali; Yana da furuci daddaɗa.
HAU; Furuci (Tana nufin yin magana)
Uwar Garke - Babbar ƙafa ko garken da yake ba wa sauran kafafen intanet damar shige da fice domin samun bayani.
Uwar Kudi - Jari ko tsagwaron kudin da ake juyawa a harkar kasuwanci.
Valley -
A turance tana nufin kwari.
Misali; Ruwa yana gudana a cikin kwari bayan damina.
HAU; Kwari (Tana nufin gangare ko ramin da ruwa ke taruwa ko ya wuce)
Variable-tone Drum - A turance tana nufin kalangu.
Misali; 'Yan mata na son kiɗan kalangu matuƙa.
HAU; Kalangu (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kaɗe-kaɗe na gargajiya)
Vein - A turance tana nufin jijiya.
Misali; Allurar jijiya aka yi masa saboda zafin zazzaɓin.
HAU; Jijiya (Tana nufin hanyar jini a jikin mutum ko dabba)
Verdict - A turance tana nufin hukunci.
Misali; Duk wanda ya aikata laifi, za a yi masa hukunci daidai da abin da ya aikata.
HAU; Hukunci (Tana nufin matsayi ko sakamakon abin da aka aikata ko za a aikata)
Very - A turance tana nufin ƙalau.
Misali; Shanyin ya yi sanyi ƙalau sai an sake dafa shi.
HAU; Ƙalau (Tana nufin sosai ko matuƙa)
Very heavy first rains of the rainy season -