Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Thief - A turance tana nufin ɓarawo. Misali;An kama ɓarawo a gidan Alhaji Iro jiya da daddare. HAU; Ɓarawo (Tana nufin mutumin da yake sata)
Thin and Flimsy - A turance tana nufin fale-fale. Misali; Yadin da aka ba mu fale-fale ne ba shi da kauri. HAU; Fale-fale (Tana nufin abu mara nauyi ko kauri)
Things done or said intentionally - A turance tana nufin gayya. Misali; Da gayya ta yi mata magana don su yi faɗa. HAU: Gayya (Tana nufin da gangan ko ana sane)
Thirst / Craving - A turance tana nufin ƙishi. Misali: Bayan doguwar tafiya a rana, matafiyin ya ji ƙishi sosai. HAU: Ƙishi (Tana nufin jin buƙatar shan ruwa ko kuma tsananin sha’awar wani abu)
This year - A turance tana nufin bana. Misali; Bana damina ta yi harshe, ma'ana an yi ruwa sosai. HAU; Bana (Tana nufin shekarar da ake ciki)
Thorn - A turance tana nufin ƙaya. Misali: Yaron ya taka ƙaya a hanyar dawowarsa daga makaranta. HAU: Ƙaya (Tana nufin tsini mai kaifi da ke fitowa a jikin wasu bishiyu ko tsirrai, wanda kan iya cutarwa)
Thresh Grain - A turance tana nufin casa. Misali; Sai an casa shinkafar sannan za a dafa. HAU; Casa (Tana nufin cire tsaba daga cikin kwansonta, kamar shinkafa da gero da sauransu)
Throne - A turance tana nufin karaga. Misali; Sarki yana zaune a kan karaga tun safe. HAU; Karaga (Tana nufin kujerar mulki ko sarauta)
Throw powdered or ground thing into the mouth - A turance tana nufin hambuɗa. Misali; Madara ta hambuɗa a baki ta gudu. HAU; Hambuɗa (Tana nufin ɗiban abu a watsa a baki)
Thunder -

A turance tana nufin kwarankwatsa.

Misali; Yara sun tsorata da kwarankwatsa yayin da ruwan sama ya fara.

HAU; Kwarankwatsa (Tana nufin sauti mai ƙarfi tare da hayaƙi da ake ji a lokacin hadari ko yayin da ake ruwan sama)

1 300 301 302 303 304 332