Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Scratch - A turance tana nufin kuje.
Misali; Amir ya faɗi ya kuje a gwuiwa.
HAU; Kuje (Tana nufin jin ciwo a saman fata)
Seal - A turance tana nufin hatimi.
Misali; Wasiƙar tana ɗauke da hatimin sarki.
HAU; Hatimi (Tana nufin wata shaida ko alama)
Search - A turance tana nufin caje.
Misali; Na caje yaran duka ban ga wanda ya ɗauki littafin ba.
HAU; Caje (Tana nufin duba ko ina)
Search - A turance yana nufin biɗa.
Misali; Ya samu abinda ya je biɗa a balaguron da ya yi.
HAU; Biɗa (Tana nufin nema ko lalube)
Second (of time) - A turance tana nufin daƙiƙa.
Misali; Na samu faɗuwar gaba na tsawon daƙiƙa ashirin saboda firgicin da na shiga.
HAU; Daƙiƙa (Tana nufin motsawar da ƙaramin hannun agogo yake yi)
Secret - A turance tana nufin asiri.
Misali; An tonawa mutumin asiri, dama ya daɗe yana satar kayan mutane.
HAU; Asiri (Tana nufin abinda yake a ɓoye)
Securities & Exchange Commission (SEC) - Hukumar Kadarori da Hada-hadar Hannun Jari
See something from afar - A turance tana nufin hanga.
Misali; Kamar Talatu na hanga tana shiga gidan maigari.
HAU; Hanga (Tana nufin gano abu daga nesa)
Seed - A turance tana nufin iri.
Misali;Iri ya yi tsada yanzu shi yasa manoma ke kokawa.
HAU; Iri (Tana nufi abin da ake shukawa)
Seeking contribution from various people - A turance tana nufin karo-karo.
Misali; Za mu yi masa karo-karo ya siyi babur ya kama sana'a.
HAU: Karo-karo (Tana nufin haɗaka ma'ana a haɗo wancan da wannan guri ɗaya)