Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Banki - Tana nufin gurin ajiya da karɓar kuɗi. Misali; Na kai ajiyar kuɗina banki jiya. ENG; Bank (A turance tana nufin banki)
Bankin Cigaban Afirka/Bankin Bunƙasa Afirka - African Development Bank (AFDB)
Bankin Duniya - World Bank
Bankin Lamunin Gidaje Na Najeriya - Federal Mortge Bank of Nigeria (FMBN)
Bankin Masana’antu - Bank of Industry(Bol)
Bankin Shige da Ficen Fatauci Na Afirka - Afican Export-Import Bank
Bankin Shige da Ficen Fatauci Na Najeriya - Nigerian Export-Import Bank (NEZIMBank)
Baobab Tree - A turance tana nufin kuka. Misali; Miyar kuka na ɗaya daga cikin miyoyin Hausawa na gargajiya. HAU; Kuka (Tana nufin koren ganyen bishiyar da ake amfani da shi don yin miya, yana da sinadarai masu matuƙar amfani a jiki)
Bara - Shekarar da ta gabata. Misali; Bara ya cika shekara biyar da rasuwa. ENG; Last year (A turance tana nufin bara)
Bara - Tana nufin mai yin hidima a cikin gida. Misali; Idris bara ne a gidan Alhaji Sani. ENG; Servant (A turance tana nufin bara)
1 21 22 23 24 25 298