Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Accident Investigation Bureau (AIB) - Hukumar Binciken Haɗura
Actors Guild of Nigeria (AGN) - Kadaurar Jaruman Fim Ta Najeriya
Adabi - Yana nufin madubin duba rayuwar al'umma.
Misali; Adabin Hausa yana da faɗi da rassa daban-daban.
ENG; Literature (A turance yana nufin Adabi)
Adadi - Yana nufin yawan abu.
Misali; Kirkin Malam ba shi da adadi.
ENG;Sum/Total (A turance yana nufin adadi)
Adda - Makami ne mai ƙota da ake amfani da shi a gona da sauransu.
Misali; Ya sare bishiyar da adda yau da safe.
ENG; Matchet (A turance yana nufin matchet)
Adiko - Maɗaurin kai na mata.
Misali; Kande ta ɗaure kai da adiko.
ENG; Head-tie (A turance yana nufin maɗaurin kai na mata)
Administration - Ma'aikata, Mulki
Administrative Staff College Of Nigeria (ASCON) - Kwalejin Jami'an Ma'aikata Ta Najeriya
Advertising Practitioners Council Of Nigeria (APCON) - Hukumar Matallata Ta Najeriya
Afircan Women’s Development Fund (AWDF) - Asusun kyautata Rayuwar matan Afirka