Surround - A turance tana nufin gewaye.
Misali; Ya gewaye gonarsa da kara saboda gudun dabbobi.
HAU; Gewaye (Tana nufi yi wa abu ƙawanya)
Surveyors Council of Nigeria (SURCON) - Hukumar Safiyo Ta Najeriya
Swallow - A turance tana nufin haɗiye.
Misali; Ya haɗiye alawar da na ba shi.
HAU; Haɗiye (Tana nufin cinyewa, ko shigar abu cikin ciki ta hanyar maƙogwaro)
Kishiyarta; Amayar
Sweat - A turance tana nufin jiɓi.
Misali; Mara gaskiya ko a ruwa sai ya yi jiɓi.
HAU; Jiɓi (Tana nufin gumi ko zufa)
Sweat - A turance tana nufin gumi.
Misali; Yau ana zafi kowa ka gani gumi yake.
HAU; Gumi (Tana nufin ruwan da yake tsattsafowa a jikin mutum ta saman fata musamman idan yana jin zafi ko ya yi gudu)
Sweet made from ground tigernuts and groundnut - A turance tana nufin daƙuwa.
Misali; Zan kai wa amarya daƙuwa saboda idan ta yi baƙi ta ba su.
HAU; Daƙuwa (Tana nufin alawar da ake yin ta da niƙaƙƙiyar gyaɗa da aya da sikari)
Sweet pounded millet mixed with water - A turance tana nufin gumba.
Misali; An raba gumba a gidan mutuwar.
HAU; Gumba (Tana nufi dakakken garin gero da sikari da ruwa)
Swell - A turance tana nufin kumbura.
Misali; Ƙafarsa ta kumbura lokacin da ya ji ciwo a filin ƙwallo.
HAU; Kumbura (Tana nufin ƙara girma ko tashi sakamakon bigewa ko jin ciwo)
Swollen - A turance tana nufin hulu-hulu.
Misali; Idonsa ya yi hulu-hulu tun jiya saboda ciwo yake masa,.
HAU; Hulu-hulu (Tana nufin kumburi sosai)
Sympathy - A turance tana nufin jaje.
Misali; Shugaban ƙasa ya yi wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa jaje.
HAU; Jaje (Tana nufin taya alhini da tausayawa wanda wani abu mara daɗi ya same shi)