Puppy - A turance tana nufin kwikwiyo.
Misali: Yara suna wasa da kwikwiyo a farfajiyar gida.
HAU; Kwikwiyo (Tana nufin jaririn kare)
Push Forward - A turance tana nufin hankaɗa.
Misali; Ya hankaɗa ta ta faɗi ƙasa.
HAU; Hankaɗa (Tana nufin turawa da ƙarfi)
Push Rudely - A turance tana nufin bangaje.
Misali; Musa ya bangaje abokinsa.
HAU; Bangaje (Tana nufin turewa da ƙarfi)
Putting a pot on the fire - A turance tana nufin girka.
Misali; Ta girka tukunya, ba za mu tafi ba sai ta sauke.
HAU; Girka (Tana nufin ɗora tukunya a kan wuta)
Quantity Surveyors Registration Board Of Nigeria (QSRBN) - Hukumar Maƙiyasta Kayan Gini Ta Najeriya
Quarrel - A turance tana nufin faɗa.
Misali; Ɗaliban faɗa suke bayan an tashi daga makaranta.
HAU;Faɗa (Tana nufin ɗaga murya da faɗin maganaganu marasa daɗi saboda ɓacin rai)
Quarter of yard -
A turance tana nufin kwata.
Misali: Ta sayi kwata na yadi domin ɗinka gyale.
HAU; Kwata (Tana nufin rubu’in yadi ko wani ɓangare ɗaya cikin huɗu na awo)
Quick Action/ Haste - A turance tana nufin garaje.
Misali; Indo tana da garaje, shi yasa ta zubar da niƙan.
HAU; Garaje (Tana nufin hanzari ko sauri ko zafin nama)
Quick-Tempered - A turance tana nufin ƙufula.
Misali; Ƙufula ya yi har ta kai ga ya mare shi.
HAU; Ƙufula (Tana nufin saurin fushi)
Quiver -
A turance tana nufin kwari.
Misali; Maharbin ya ɗauki kwari cike da kibiyoyi.
HAU; Kwari (Tana nufin akwati ko jakar da ake ɗaukar kibiyoyi a ciki lokacin harbin kibiya)