Terms Dictionary

Stocks Exchange Market (SEM) - Kasuwar Hada-hadar Hannun Jari Supreme Court-kotun Koli
Stone - A turance tana nufin dutse. Misali; Akwai gungumemen dutse a garin mu. HAU; Dutse  (Tana nufin dunƙulallun halittun Allah da ke doron ƙasa)
Storm - A turance tan nufin hadari. Misali; Hadari ya taso, da alama za a yi ruwa mai yawa. HAU; Hadari (Tana nufin yanayin da ke nuna za a yi ruwan sama)
Strange - A turance tana nufin bambarakwai. Misali; Abin ya zama bambarakwai namiji da suna Hajara. HAU; Bambarakwai (Tana nufin abu ya kasance ba yanda ya kamata ba)
Stranger/Visitor - A turance yana nufin baƙo. Misali; Jiya na yi baƙo da yamma. HAU; Baƙo (Tana nufin wanda ba a sani ba ko wanda ya kawo ziyara)
Strive - A turance tana nufin dage. Misali; Ya dage da karatu har sai da ya ci jarrabawarsa. HAU; Dage (Tana nufin yin ƙoƙari matuƙa)
Struggle - A turance tana nufin daga. Misali; An sha daga da shi kafin ya yadda a yi masa allurar. HAU; Daga (Tana nufin gumurzu ko shan fama)
Struggle/Trouble - A turance tana nufin jidali. Misali; Ya janyo wa kansa jidali tunda ya auri yarinyar nan. HAU; Jidali (Tana nufin rikici ko ɗawainiya)
Stuttering/ Stammering - A turance tana nufin in'ina. Misali; An ce shan ruwan tattabaru na sauƙaƙa in'ina. HAU; In'ina (Tana nufin yin magana da ƙyar ko ana yi ana tsittsitsinkawa)
Suckling of Infant - A turance tana nufin jego. Misali; Indo jego take shi yasa ba za ta bi mu ba. HAU; Jego (Tana nufin shayar da jariri)
1 273 274 275 276 277 300