Open Space/Arena - A turance tana nufin fage.
Misali; An ba wa 'yan dambe fage don su fafata.
HAU; Fage (Tana nufin fili ko dandali)
Open-ended variable tone drum which is beaten with fingers - A turance tana nufin kotso.
Misali; Ya daɗe yana kaɗa kotso a ƙauyensu.
HAU; Kotso (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa)
Opportunity - A turance tana nufin faraga.
Misali; Mun samu faraga mun yi abubuwan alkhairi da yawa.
HAU; Faraga (Tana nufin samun dama)
Orange-headed male lizard - A turance tana nufin jan-gwada.
Misali; Jan-gwada ne ya hana sauran ƙadangarun cin abinci.
HAU; Jan-gwada (Tana nufin namijin ƙadangare)
Organization - Hukuma, Ƙungiya
Organization Of African Trade Union Unity (OATUU) - Gamayyar Ƙungiyar 'Ƴankasuwa Ta Afirka
Organization of Islamic Cooperation (OIC) - Kadaurar Haɗa-Kan Musulmi
Organization of Petroleum Exporting Countries (OPEC) - Ƙungiyar Ƙasashe Masu Arzikin Fetur
Organization Of Trade Unions of West Africa (OTUWA) - Ƙungiyar 'Ƴankasuwa Ta Yammacin Afirka
Orgasm - A turance tana nufin inzali.
Misali;Lalurar sanyi na sanya saurin inzali ga ma'aurata.
HAU; Inzali (Tana nufin gamsuwar jima'i)