On top/above - A turance tana nufin bisa.
Misali; Littattafan na bisa teburi.
Kishiyarta; Ƙarƙashin
HAU; Bisa (Tana nufin a kan wani abu)
One - A turance tana nufin guda.
Misali; Gida guda za mu zauna da ƙani na.
HAU; Guda (Tana nufin ɗaya)
One after the other - A turance tana nufin bi da bi.
Misali; Likitan yana duba marasa lafiyan bi da bi.
HAU; Bi da bi (Tana nufin ɗaya bayan ɗaya)
One of the sixty sections into which the Qur’an is divided - A turance tana nufin izifi.
Misali; Abdallah ya haddace izifi biyu a watan da ya gabata.
HAU; Izifi (Tana nufin ɗaya daga cikin kaso sittin na Ƙur'ani)
One Thousand - A turance tana nufin dubu.
Misali; Ya ba ni Naira dubu da ya zo duba ni a asibiti.
HAU: Dubu (Tana nufin lambar da ke bin bayan ɗari tara da casa'in da tara)
Oneness - A turance tana nufin kaɗaita.
Misali; Wajibi ne a kaɗaita Allah a wajen bauta.
HAU; Kaɗaita (Tana nufin ɗayantawa ba tare da abokin tarayya ba musamman ga Allah SWT)
Only - A turance tana nufin kawai.
Misali; Kuɓewa kawai na siyo da na je kasuwa.
HAU; Kawai (Tana nufin kaɗai)
Only - A turance tana nufin kurum.
Misali; Kwano ɗaya kurum ta isa kowa ya ƙoshi.
HAU; Kurum (Tana nufin kawai)
Only - A turance tana nufin kaɗai.
Misali; Ita kaɗai ce take zuwa da wuri kullum.
HAU; Kaɗai (Tana nufin kawai)
Open space in front of compound - A turance tana nufin farfajiya.
Misali; A farfajiyar gidan za a yi taron bikin.
HAU; Farfajiya (Tana nufin filin tsakar gida)