Monkey - A turance tana nufin biri.
Misali; Da muka je gidan ajiye namun daji mun ga biri da kura.
HAU; Biri (Tana nufin dabba mai yanayin siffar mutum)
Mother - A turance tana nufin inna.
Misali; Kande ƙanwar inna ce.
HAU; Inna (Tana nufin mahaifiya)
Motion Picture Practitioner’s Association oF Nigeria (MOPPAN) - Ƙungiyar Jaruman Fim Ta Najeriya
Motomechs & Technician Association (MOMTAN) - Ƙungiyar Injiniyoyi da Kanikawan Mota
Motor Fan - A turance tana nufin farfela.
Misali; Farfelar motar ta lalace, sai an kai gyara.
HAU; Farfela (Tana nufin fankar da ke jikin mota)
Motorcycle - A turance yana nufin babur.
Misali; A kan babur na zo makaranta yau.
HAU; Babur (Abin hawa ne mai ƙafa biyu)
Mouth - A turance yana nufin baki.
Misali; Ya buɗe baki za yi magana sai ruwa ya sakko.
HAU; Baki (Gaɓa ce da ke fuskar mutum wadda ake amfani da ita wajen magana, cin abinci da sauransu)
Mud - A turance tana nufin caɓi .
Misali; Ka yi hankali da caɓi a hanyar saboda jiya an kwana ana ruwa.
HAU; Caɓi (Tana nufin jiƙaƙƙiyar ƙasa)
Multinational Corporation (MNC) - Kamfanonin Manyan Ƙasashe
Multinational Joint Task Forces (MJTF) - Rundunar Tsaro Ta Haɗin Guiwar Ƙasashe