Multiple Of Ten - A turance tana nufin gomiya.
Misali; Gomiya biyar tana nufin hamsin kenan.
HAU; Gomiya (Tana nufin goma sau wani adadi)
Mumps - A turance tana nufin hangum.
Misali; Hangum ne ya fitowa Safiya, tana kan shan magani.
HAU; Hangum (Tana nufin ciwon da ke kumbura gefen kunci zuwa kunne)
Music - A turance tana nufin kiɗa.
Misali; Matasan sun kunna kiɗa suna cashewa don murnar bikin abokinsu.
HAU; Kiɗa (Tana nufin rauji ko sauti mai daɗi)
Music Producers & Marketers Association of Nigeria (MUPMAN) - Ƙungiyar Mawaƙa da Dillalan Waƙa Ta Najeriya
Musical Copyright Society of Nigeria (MCSN) - Ƙungiyar Haƙƙin Mallakar Mawaka Ta Najeriya
Muslim Media Practitioners of Nigeria (MMPN) - Ƙungiyar Musulmai 'Ƴanjarida Ta Najeriya
Muslim Rights Concern (MURIC) - Ƙungiyar kare-Haƙƙin Musulmai
Muslim Students Society of Nigeria (MSSN) - Ƙungiyar Ɗalibai Musulmai Ta Najeriya
Must - A turance tana nufin dole.
Misali; Dole ne dukkan musulmi ya yi sallah sau biyar a rana.
HAU; Dole (Tana nufin wajibi ko tilas)
Mutuntaka - Halaye da ɗabi'un kowane ɗan'adam, wadanda suke bambanta daga mutum zuwa mutum.