Menstruation - A turance tana nufin haila.
Misali; Matan da ke haila ba sa shiga masallaci.
HAU; Haila (Tana nufin jinin da mata ke fitarwa a kowanne wata)
Mere - A turance tana nufin kacal.
Misali; Naira biyar kacal za ka biya ka ɗauki kayanka.
HAU; Kacal (Tana nufin kaɗai ko kaɗan)
Messy or disorderly - A turance tana nufin kaca-kaca.
Misali; Sun yi kaca-kaca da madara a ɗakin.
HAU; Kaca-kaca (Tana nufin a hargitse)
Metal Roof Drain - A turance tana nufin indararo.
Misali; Mun cika gidan nan da ruwan da muka tara a indararo.
HAU; Indararo (Tana nufin hanyar da ruwa yake zubowa ta saman rufin kwano)
Millet - A turance tana nufin gero.
Misali; Bana gero zalla ya shuka.
HAU; Gero (Tana nufin ɗaya daga cikin tsirrai wanda ake amfani da shi wajen yin fura da kunu da sauransu)
Millet Porridge - A turance tana nufin koko.
Misali; Koko da ƙosai ɗaya ne daga cikin abincin karin kumallon Hausawa.
HAU; Koko (Tana nufin abin sha da ake yi da gero, ana dama shi da tafasasshen ruwa kamar kunu)
Mingling With Others - A turance tana nufin cuɗanya.
Misali; Na yi cudanya da mutane da dama da na je Turai.
HAU; Cuɗanya (Tana nufin mu'amala da mutane)
Ministry - Ma'aikata
Ministry of Police Affairs - Ma'aikatar Harkokin 'Ƴansanda
Misfortune/Calamity - A turance tana nufin ja'iba.
Misali; Ya ga ja'iba, bayan ya rasa ɗansa shagonsa ya kama da wuta.
HAU; Ja'iba (Tana nufin masifa ko rashin sa'a ko ibtila'i)