Shinkafa Mai Ƙwai

0
651

Shinkafa mai ƙwai wani abinci ne da ake yi da shinkafa tare da ƙwai.

Abubuwan Da Ake Buƙata wajen haɗa shinkafa mai ƙwai

Shinkafa (dafaffiya)
Curry/ kayan ƙamshi
Abin ɗanɗano
Albasa
Ƙwai
Attaruhu
Mai

Yadda Ake Haɗawa

A fara dafa shinkafar sama–sama a tace, a wanke ta a saka ɗan mai a tukunya yadda zai isa, ya ɗanyi zafi a sa shinkafar a dinga juyawa, a sa albasa yankakkiya da attaruhu, sannan a saka abin ɗanɗano da curry da kayan ƙamshi a ci gaba da juyawa, a sa ƙwai da aka ɗan kaɗa shi a ɗan kwano a rinƙa juyawa har ta haɗe jikinta.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Danbun Shinkafa danna nan

labarin da ya wuceTatsuniyar Gizo Da Giwa
Labarin na GabaAsalin Kiɗan Fiyano