Tag: abincin turawa

  • Yadda Ake Macaroni 2

    Yadda Ake Macaroni 2

    Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Macaroni su ne:

    • Albasa
    • Tumatir
    • Green beans (koren wake)
    • Potatoes (dankali)
    • Niƙaƙƙen nama
    • Abin ɗanɗano
    • Vinegar (khal)
    • Kasbara
    • Shammar

    Kayan Aiki

    • Murhu/Risho/Gas
    • Tukunya
    • Kasko
    • Mazubi (mai tsafta)
    • Ludayi
    • Abin daka
    • Wuƙa

    Yadda Ake Haɗawa

    A sami albasa, tumatir, koren wake, duk a yi slicing ɗin su, sai a yanka dankali ƙanana, a soya sai a ajiye shi a gefe; sai a sa mai daidai ƙima a tukunya, ki zuba minced meat (niƙaƙƙen nama) a ciki, a soya kar ya yi ƙarau, a zuba albasa da tumatir a ci gaba da juyawa. Sai a soya green beans da ɗan mai kaɗan, in miyar ta dahu a zuba abin ɗanɗano a zuba dankalin, a sa shammar da kasbara ta ƙara dahuwa kaɗan sai a sauke a ci da macaroni fara.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Shinkafa Mai Ƙwai danna nan

    Dominn karanta bayani akan Mene Ne Abinci A Lafiyance? danna nan

  • Yadda Ake Mahshi

    Yadda Ake Mahshi

    Mahshi wani abinci ne da ake haɗawa da shinkafa, kayan lambu da kuma nama.

    Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Mahshi

    • Gatafosa/ yalon bature (garden egg)
    • Potatoes
    • Onions
    • Nama
    • Shinkafa

    Kayan Aiki

    • Murhu/Risho/Gas
    • Kwano
    • Cokali
    • Wuƙa
    • Kasko

    Yadda Ake Haɗawa

    A sami waɗannan sinadaran da aka lissafo a sama, kifafe cikinsu, dukkan su, su yi falai-falai; amma ba a yanka suba, za ki dafa shinkafa ta dahu kaɗan, sai ki kwashe ki saka a cikin kwano.

    Idan ta yi sanyi, ki kawo niƙaƙƙen nama, ki zuba naman ya fi shinkafar yawa, sai a zuba shammar da kasbara ki yayyanka su da tafarnuwa da gishiri da maggi ki chakuɗa ya haɗe jikinsa.

    Sai ki wanke kayan da kika fafe, ki tsane ruwansu, ki wanke koren tattasai sai (black pepper) ki zuba a cikin haɗin; ki dinga ɗiban shinkafar da kika haɗa, kina zubawa a cikin kayan da kika fafe; ki rinƙa soyawa kaɗan-kaɗan idan kin gama sai ki saka a cikin dage-dagen tumatir irin wanda ake ci da kufta.

    Domin karanta Yadda Ake Kebab (V.I.P SOUP) danna nan

  • Yadda Ake Fish Soup

    Yadda Ake Fish Soup

    Fish Soup wata miya ce da ake yi da kifi.

    Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Fish Soup su ne:

    • Fish (kifi)
    • Maggi, salt (Abin ɗanɗano, gishiri)
    • Curry
    • Oil
    • Kayan miya
    • Kanwa

    Kayan Aiki

    • Murhu/Risho/Gas
    • Kasko
    • Mazubi (mai tsafta)
    • Wuƙa

    Yadda Ake Haɗawa

    Da farko a soya mai da albasa, a zuba yankakken tattasai da tumatir da albasa a kawo ruwa kaɗan a zuba da ‘yar kanwa;

    A gyara kifin a wanke a zuba, a saka gishri da maggi da ƙiƙanshi kamar minti goma;

    Sai a sauke kana iyaci da shinkafa ko cous – cous e.t.c.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Alala danna nan

  • Yadda Ake Kebab (V.I.P SOUP)

    Yadda Ake Kebab (V.I.P SOUP)

    Kebab wani abinci ne da ake haɗa shi da nama, tare tumatir da dai sauransu.

    Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Kebab su ne:

    • Kidney, liver, meat (ƙoda, hanta, nama)
    • Onions (albasa)
    • Markaɗe
    • Spices (kayan ƙamshi )
    • Salt, maggi (gishiri da abin ɗanɗano)
    • Mai

    Kayan Aiki

    • Murhu/Risho/Gas
    • Kwano
    • Cokali
    • Wuƙa
    • Kasko

    Yadda Ake Haɗawa

    A sami ƙoda da hanta da nama (na rago) duk sai ki tafasa, ki yanka su triangle ƙanana, sai ki sami albasa ki soya, ki kawo mai kaɗan ki zuba.

    In yasoyu ki zuba mai, kibar ta tayi kauri sai ki saka dan kalin da naman acikin miyar.

    Sannan ki sa kayan ƙamshi, idan ya haɗu a sauke.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Fish Soup danna nan

  • Shinkafa Mai Ƙwai

    Shinkafa Mai Ƙwai

    Shinkafa mai ƙwai wani abinci ne da ake yi da shinkafa tare da ƙwai.

    Abubuwan Da Ake Buƙata wajen haɗa shinkafa mai ƙwai

    Shinkafa (dafaffiya)
    Curry/ kayan ƙamshi
    Abin ɗanɗano
    Albasa
    Ƙwai
    Attaruhu
    Mai

    Yadda Ake Haɗawa

    A fara dafa shinkafar sama–sama a tace, a wanke ta a saka ɗan mai a tukunya yadda zai isa, ya ɗanyi zafi a sa shinkafar a dinga juyawa, a sa albasa yankakkiya da attaruhu, sannan a saka abin ɗanɗano da curry da kayan ƙamshi a ci gaba da juyawa, a sa ƙwai da aka ɗan kaɗa shi a ɗan kwano a rinƙa juyawa har ta haɗe jikinta.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Danbun Shinkafa danna nan

  • Yadda Ake Boga (Burger)

    Yadda Ake Boga (Burger)

    Barkan mu da sake kasancewa a fannin girke-girken mu na WikiHausa. A yau za mu koyi yadda ake burger.

    Abubuwan da ake buƙata:

    1.Fulawa
    2.Yeast
    3.Kwai
    4.Bota
    5.Dankalin Turawa
    6.Salad
    7.Ketchup
    8.Salad cream
    9.Nama
    10.Albasa
    11.Maggi
    12.Kayan ɗanɗano da kayan ƙamshi
    13.Tumatir

    Yadda ake haɗawa:

    • A hada fulawa da gishiri da yis, ki kwaɓa su da ruwan ɗumi,
    • Sai a kai shi  ƙarƙashin rana ya yi kamar minti ashirin,
    • Sannan a shafa wa gwangwanin gashin bota a jikinsa, sai a saka kwaɓin fulawar a ciki.
    • A gasa a abin gashi, ya gasu har dai bayan ya yi brown, a cire a raba shi biyu.
    • A dafa nama tare da albasa da maggi, a daka shi, sannan a soya shi sama-sama,
    • Za a yanka dankalin Turawa ƙanana, sai a dafa shi tare da ƙwai, a yanka ƙwan, amman a tsaitsaye,
    • Sai a ɗauko wannan biredin da aka gasa, a shafe shi da salad cream da ketchup, a ɗauko salad a sa a ɓari ɗaya na jiki, amma kar a yanka salad ɗin.
    • Sai a zuba nama, ƙwai, dankali da yankakken tumatir da albasa a kan salad ɗin nan, sai ki rufe da ɗaya ɓangaren.
    • Idan ana so, ana iya ƙara gasa shi sama-sama ko a ci a haka.