Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Tribunal Court - Kotun Wucin Gadi/Kotun Musamman
Truth - A turance tana nufin gaskiya. Misali; Idan mutum na faɗin gaskiya kimarsa na ƙaruwa. HAU; Gaskiya (Tana nufin abinda yake na haƙiƙa ma'ana yanda yake babu ƙari babu ragi) Kishiyarta; Ƙarya
Tsagaita - Tsahirtawa daga yin, ko barin wani abu ta hanyar taƙaitawa ko kaucewa, kamar daina yin abin da yake jawo ko haifar da asarar dukiya ko ta rayuwa.
Tsaron Sirri - Aikin tsaro ne da jami'an tsaro na farin kaya suke yi a boye domin nesa daga magauta.
Tuesday - A turance tana nufin rana ta biyu a mako. Misali; Kasuwar tana ci ranar Talata. HAU; Talata (Rana ta biyu a cikin ranakun mako)
Tunnel/Pipe - A turance tana nufin bututu. Misali; Mai gyaran bututun ya zo da wuri. HAU; Bututu (Tana nufin mazurari na ruwa ko iska da sauransu)
Tusk - A turance tana nufin haure. Misali; Da hauren giwa ake haɗa maganin. HAU; Haure (Tana nufin haƙori)
Twenty - A turance tana nufin ishirin. Misali; Kaji guda ishirin ya siyo don gudanar da bikin. HAU; Ishirin (Tana nufin goma sau biyu)
Two stringed, plucked musical instrument - A turance tana nufin garaya. Misali; Gurin ya cika da masu kiɗan garaya don bikin na 'yan bori ne. HAU; Garaya (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa na gargajiya)
Type of cloth without embroidery - A turance tana  nufin gare. Misali;Malam Audu ya sa gare. HAU; Gare (Tana nufin rigar Hausawa mara ado)
1 6 7 8