Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Town Wall - A turance tana nufin ganuwa.
Misali; An ɗauki shekaru ana gina ganuwar Jihar Kano.
HAU; Ganuwa (Tana nufin ginin da ake yi don katange gari da ba shi kariya)
Tracing Something - A turance tana nufin diddigi.
Misali; Jami'an tsaro na bin diddigin lamarin da ya faru jiya.
HAU; Diddigi (Tana nufin bibiyar abu)
Trade Union Congress of Nigeria (TUC) - Kadaurar Ƙungiyoyin 'Ƴankasuwa Ta Najeriya
Trading - A turance tana nufin fatauci.
Misali; Idi ya tafi fatauci wata biyu da suka wuce.
HAU; Fatauci (Tana nufin tafiya daga wani gari zuwa wani gari don siye da siyar da kaya)
Transaction - A turance tana nufin hulɗa.
Misali; An ƙulla hulɗar cinikayya tsakanin 'yan kasuwar.
HAU; Hulɗa (Tana nufin mu'amala ko cuɗanya)
Translation - A turance tana nufin fassara.
Misali; Ya fassara littafin daga harshen larabci zuwa harshen Hausa.
HAU; Fassara (Tana nufin daga wani harshe zuwa wani harshe)
Transmission Company of Nigeria (TCN) - Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki Na Najeriya
Tree - A turance tana nufin bishiya.
Misali; Idan an shuka bishiya takan ɗauki lokaci mai tsawo kafin ta girma.
HAU; Bishiya (Tana nufin ice ko tsiro da yake fitowa haka kawai ko idan an shuka, yana da ganyayyaki da itatuwa a wasu lokutan)
Tree - A turance tana nufin bishiya.
Misali; Wannan itacen ɗorawa ne.
HAU; Itace (Tana nufin bishiya)
Tribunal - Kotun Wucin Gida