Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Tiredness - A turance tana nufin gajiya.
Misali; Gudu na sa gajiya sosai.
HAU; Gajiya (Tana nufin mutuwar jiki da jin rashin ƙarfi)
Tomorrow - A turance tana nufin gobe.
Misali; Gobe babu karatu saboda hutun ƙarshen mako.
HAU; Gobe (Tana nufin bayan kwana guda ma'ana ranar da za biyo bayan wacce ake ciki)
Kishiyarta; Yau
Tongue - A turance tana nufin harshe.
Misali; Ya tauna harshe yayin da yake cin abinci.
HAU; Harshe (Tana nufin gaɓar da ake magana da ita wadda take cikin baki)
Tooth - A turance tana nufin haƙori.
Misali; Ba zai iya tauna ƙashi ba saboda ba shi da haƙori.
HAU: Haƙori (Tana nufin ɗaya daga cikin sassan jikin ɗan Adam da sauran halittu, wanda ake amfani da shi wajen tauna)
Topple Over - A turance tana nufin ɓingire.
Misali; Ta ɓingire da bacci ana karatu.
HAU; Ɓingire (Tana nufin kwanciya ba tare da tsammani ba)
Tortoise - A turance tana nufin kunkuru.
Misali; Kunkuru yana iya rayuwa sama da shekaru tamanin ba doron ƙasa.
HAU; Kunkuru (Tana nufin wata dabba mai rayuwa a ruwa ko a doron ƙasa ko kuma guri mai danshi, tana tafiya a hankali kuma yana rayuwa mai tsayi)
Tower - A turance tana nufin hasumiya.
Misali; An fara gyara fentin hasumiyar masallacin unguwar mu.
HAU; Hasumiya (Tana nufin wani siririn gini mai tsawo da ake yi a masallaci ko majami'a)
Town - A turance tana nufin birni.
Misali; A birni ake samun manyan gidaje da manyan makarantu
Kishiyarta; Ƙauye
HAU; Birni (Tana nufin maraya ko inda ababben more rayuwa na zamani suke)
Town - A turance tana nufin Gari (Birni).
Misali; Abin mamaki, guri ya zama gari.
HAU; Gari (Tana nufi inda mutane suka fi yawa musamman inda ba ƙauye ba (birni))
Kishiyarta; Ƙauye
Town Planners Registration Council of Nigeria (TOPREC) - Hukumar Ayyukan Matsara Birane Ta Najeriya